Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
713. Hausa yawa gare ta in za a fasalta,
Ga ta ƙasa guda, da faɗi a gare ta,
Ga yalwa akwai ƙasashe a cikin ta,
Ga tari na al’uma,
babu kamar ta,
Tun ga karuruwanta nan aka ganewa.
714. Da Kananci da Sakkwatanci nau’i ne,
Na karin harsuna,
a yankin kowanne,
Ya yi daban da
inda kowansu ka zaune,
Harshen Hausa yay
yawa ko ka gane?
Dauranci da
Zazzagancin Hausawa.
715. Da Arabci, Haɗejiyanci a saka shi,
Su duka Hausa ce,
suke yi ba ƙyashi,
Amma dai akwai
kari an gane shi,
Kwai wani
sashikarin daban aka furta shi,
Da Kabanci da
Gudduranci aka sawa.
716. Gobarci da Gimbananci duka na nan,
Su duka nasu
yanki, tsarin nan,
Na karin harsuna,
daban da Kanancin nan,
Sannan ga karin da
ya zo yankin nan,
Katsinanci uban
buki ban mantawa.
717. Nan niya,
canniya, ina tilaminku?
Hurcikke, ka zo mu
zauna ɗakinku,
Zamfarci wajen kiɗa ba a barin ku,
Makaɗa duk a Hausa ai babu irin ku,
Da Gubanci karuruwanmu na Hausawa.
718. Furuci duk ya zan karin harshe ƙyale,
Ɗauki na daidai, ka san
yana nan a tule,
In ka yi baƙo gidanka nan sai ku
yi lale,
Lale da zuwansa, ɗan’uwa lale-lale,
Kar ka saka shi ko kaɗan ga rubutawa.
719. “Hwanho”
mai ruwa, wuyan nasa a tsuke,
“Hwatar” raƙumi da kyau, malam
soke,
Sarkawa ka kama
kifi su ‘yan soke,
“Hwari” sun yi “hwarmaki” gonar rakke,
Sun muzanta babu geron ɓatawa.
720. Ba mu da “hw”
a Hausa mun dai san “fari”,
Ba mu da “hw” ga sautuka ko can dauri,
Amma dai muna da “f” Hausa ta “fari”,
Fatima, Fati,
fatsima ɗiyar mai alheri,
Mun san “farmaki” da yaƙi da karawa.
721. Na ji “tcimen” da ɗaci na maɗacci,
“Tcahe” gari da ba a “tcamar” matalauci,
Ba a rubuta “tc”, a Hausa ga kwatanci,
Kar ka rubuta “tc”
kana ji marubuci!,
Ba mu da “tc” ga Hausa “Tsama” aka sawa.
722. Kai mai son kiɗi biɗo masu kalangai,
“Dwagi”, “dwage-dwage”, kyanwa ta dagai,
Yaya za ka yi da “dw” kai sa dagai,
Shago yai karo da Ado ya “dwagai”,
Baki na jini
shina ƙara bugawa.
723. Ba a rubuta “dw”
ka dai ce ya “dagai”,
Mai wahala ya nemo
jirai ga kalagai,
“Dwaɗe” kunnuwanka domin ya zagai,
“Dwagai” babu shi,
ka bar “dw” sa “dagai”,
Ita ce mazhabar
rubutun Hausawa.
724. “Rwarwake-rwarwaken ga yau har malammai,
Mari an ka ce Bukar ya “rwaga” mai,
Ya ɗauko abin bugu ya rabka mai,
Ya “rwarumo” mucciya yana so ya buga mai,
Ya taushe shi ga
ciki zai “lwatcewa”.
725. A biɗo ƙa’idar rubutu a bi sannan,
“Rarake”, za ka sa rubuta shi wurin nan,
“Latsewa” ake buƙata a saka nan,
Kar ka rubuta “rw”
ka sa “r” a wurin nan,
Kar ka rubuta “lw” ga zance latsewa.
726. ‘Yan Daura suna da
‘hy’ sauti to sai,
An ka umurci kar a sa ta a tsari sai,
Ai nazari Haɗejiyawa da Yakasai,
Ƙofar kuka mun ka “hya” “hyayi” sosai
Mai zafi ƙwarai zufa na karyowa.
727. Ba a rubuta “hy”
zaman “sh” ne daidai,
Can Daura da “hy” a
Hausa ku gane dai,
“Sh” an ka sani ku sanya shi a daidai,
Sa “sh” nan da kyau rubuta shi kamar dai,
Shan shayin Kano da ƙwai aka toyawa.
728. Duk harufan da mun ka ce kar ka rubuta,
Ba mu nufin a yada
su kar a karanta,
Dialect ne muke buƙatar ka fahimta,
Mun rarrabe yadda
du ya dace a rubuta,
Ba a ce babu su
ba can gun furtawa.
729. Ba shan kai, a nan ga tsarin furucin su,
‘Yan Sakkwato ne,
ana buƙatar ceton su,
Su ko Kanawa a bar
su can ga Kanancinsu,
Doka ce ta ce, a
bar su wajen mai su,
Ga misali wurin
ruwaya aka sawa.
730. In an ce ka zana yadda ya furta shi,
To sai ka saka, ka
tsara ya kamar shi,
Kai saka yadda za
a rubuta shi,
A karanta ka zana
yadda ya furta shi,
Dama an ka ba ka
nan ba a hanawa.
731. Sai ka rubuta yadda yac ce duka sosai,
Bi shi a hankali
ka saurara sosai,
Kai bari damuwa da
dialect ne to sai,
Ka saurari batunsa
don rubutawa sosai,
Ba da ragi ba
kana ba ka ƙarawa.
732. In ka kiyaye ɗan bayanin ga da gaske,
Domin nan garai
akwai ƙarin haske,
Daga nan za ka san
ƙasashen nan take,
Kowane yankin ƙasar ka gane shi a
take,
Hausar kowace ƙasa za ka iyawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.