Sauyawar Harafin /d/ Zuwa /j/

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    615. Harafin d idan wasullan da ka bin sa,

     Sun shiga inda za su motsa shi dukansa,

     Sun ka amince a ba shi damar furucinsa,

     Wato dai ina nufin wasullan da ya Æ™unsa,

    ‘A’, “O”, “U”, a nan wurin zai nunawa.

     

    616. In kalma tana da d can daga ƙarshe,

     Sauyawar akan gane a can tarshe,

     Doka ta aminta sauya gaÉ“ar Æ™arshe,

     Ma’ana za ta kumbure, sai ta yi reshe,

      Gun jam’inta nan abin zai sauyawa.

     

    617. In ka ce “gado” tilo ne ka kiyaye,

     Kullum Æ™udurin sayensa na nan ga iyaye,

     In kuma babu shi amarya sai tai ta hawaye,

     Kalma ce guda, aboki kan ka yana waye,

      Jam’in nasa ko “gadaje” ka biyowa.

     

    618. In ka ce “gada” da mota ka hayewa,

     Waggana wadda a’ akwai hanyar Yalwa,

     Can Jaba na gane ta, ta fi misaltawa,

     Kalma ce guda gada mai sauyawa,

      Jam’in nata ko “gadoji” aka cewa.

     

    619. Lura da kyau “gida” tilo ne ga zubinsa,

     Duk mai rai a yau yana da muradinsa,

     Ko sun yi yawa gare shi ko ma don gasa,

     Ita kalmar gida guda ce, furucinsa,

      In kuma sui yawa “gidaje” aka cewa.

     

    620. Gwadda  na da kyau ga mai buÉ—in baki,

     Shi mai azumi yana muradin yanka ki,

     Malam sa wuÆ™a ga gwadda ba birki,

     Na matsu in gane ta in kai ta ga baki,

      Gwaddoji saman tire sai yankawa.

     

    621. Farda kasuwar ice aka samunta,

     Had da arakke duk ana É—aÉ—É—aurata,

     Bata-bata a kai, a kai ta a saida ta,

     In sun yi yawa ga jam’u nan aka sauyata

      Fardoji ga jam’u shi aka zanawa.

    622. Ga misalan ga duk biyar in ka kiyaye,

     An zano tilo da jam’unsu Æ™awaye,

     An bayyana kowanensu kai ya waye,

     Lura da kyau waÉ—anda kag gan su a lauye,

      Da tilo ne gami da jam’i aka sawa.

     

    623. Harafin d a gun tilo in ka kiyaye,

     Shi ka zuwa ya girke tanda ya yi toye

     Gun jam’unmu bai zuwa sai ya yi É“oye,

     Bai É“oye ba, na ga an sa shi a sauye,

      Ya zama j ga jam’u can gun tsarawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.