Ticker

    Loading......

Sauyawar Harafin s Zuwa sh A Karshen Gaba

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

647. Harafin s yakan zamo sh bisa doka,

 Sh aka sa wa a sauya s tsarin doka,

 Dole a sauya s a sa sh a bi doka,

 Lura da kyau ka zan kula buɗe idonka,

  Can ƙarshen gaɓa ga dokar zanawa.

 

648. Gun kalmar ƙasa idan za ka kiyaye,

 Ai s ke a ƙarshe don kar ka kuranye

 Amma in ya zam tilo, sa ta yi goye,

 In jam’in ƙasa ya zo sh ta yi raye,

  Za ka ga ta zamo ƙasashe ga fitowa.

 

649. Tasa in ta zo da jam’inta kiyaye,

 Sa mata sh ka kauce tsarin bobaye,

 Doka ce ta ce da s zo ki kuranye,

 In tasa tai yawa ku duba kai waye,

  Tasoshi kake faɗa gun furtawa.

 

650. Busa bushe-bushe shi ne jam’inta,

 Sarki shi ake wa busar ƙasaita,

 Bushe hitilar ka babu mai iya kunna ta,

 Bishiya in ta faɗi, nan aka ta da ta,

  Basasshe da an ganai sai ƙonewa.

 

651. Casa, cashe-cashe to ka ji zubinsu,

 Shinkafa, gyaɗa, da gero, duka sa su,

 Acca ta yi kyau a gyarata ta casu,

 Mai casan abinci na cashe guminsu,

  Casasshe yana shiga gun ƙirgawa.

 

652. Tusa in ana buƙatar jam’inta,

 Wagga da budari yakai ku rubuta,

 Sh ya fi ta zo da ƙarshe a rubuta,

 In kuma tai yawa ga bakin furta ta,

  Tusoshi ake faɗa babu musawa.

 

653. Ka ga ƙasa guda tilo ce nahawunta,

 Sa mata sh ta zo a ƙarshe na gaɓarta,

 Matuƙar dai ana buƙatar jam’inta,

 Malam ɗauki naka biro ka rubuta,

  Gun jam’inta ko ƙasashe aka cewa.

 

654. Shi kafinta bai ga laifin ƙusa ba,

 Sun haɗa dangantaka da ƙusa ba gaba,

 Ƙusa ta lume ga katako babba,

 Ya saka hincibarsa bai so ya cire ba,

  Ƙusoshi ka sa miyatai burgewa.

Post a Comment

0 Comments