Ticker

Sauyawar Harafin t Zuwa c A Karshen Gaba

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

643. Harafin t yana cikin wannan doka,

 Malam lura sai ka nuna basirarka,

 Can ƙarshen gaɓa, ka duba rubutunka,

 In t  ta biyo ga tsarin kalmominka,

  Masu hawainiya ga dokar zanawa.

 

644. Mota in kana buƙatar jam’inta,

 Wannan da take gudu a saman kwalta,

 In Allah ya ban kuɗi sai na sai ta,

 Ita mota idan fa ta kai har ta yawaita,

  Motoci ka bayyana babu musawa.

 

645. Tuta kowace ƙasa na launinta,

 ‘Yan Nijeriyarmu duk mun ɗaga tuta,

 ‘Yan makarantarmu kowane ya riƙa tuta,

 Su manyan garuruwanmu an kai masu tuta,

  Tutocin Mujaddadi na burgewa.

 

646. Sata mai yawa gari taka ruɗewa,

 Kowa hankalinsa sai ƙara ɗagawa,

 Shi mai dukiya ko ba ya da hutawa,

 Kayan tanadinsu sai ƙara fakewa

  Domin sace-sace na hana walawa.

Post a Comment

0 Comments