Sauyawar Harafin z Zuwa j

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa 

    631. Harafin z yakan zamo j ga rubutu,

     Sauyawa yakai, ku lura masu karatu,

     An tanadi tsare-tsare gun masu rubutu,

     Su lura da wanga tsari na rubutu,

      Daidai gun gaÉ“a ta Æ™arshe ga kulawa.

     

     

    632. Shi ma kan sa gun tilon dai aka zance,

     Kalmar duk da taz zamo É—ai ga kwatance,

     Kwai tsari na sauya shi z a misalce

     In aka so a mai da ita jam’i to ce,

      In aka mai da shi yawa ga rubutawa.

     

    633. Ga kalmar maza idan aka sauya ta,

     Kwai Æ™ari gaban ta malam ka rubuta,

     Ai sauyin baÆ™i na z an ka hukunta,

     Æ˜arin j ake gaban z a rubuta,

      Gun jam’inta ai mazaje aka cewa.

     

    634. Sa natsuwa ka dubi geza ga tilon ta,

     Æ˜ari za ka yo gaban z ka rubuta,

     Shi ma za ka sanya j don a karanta,

     Lura da kyau, ga furucinta ka furta,

      Gezoji ga nata jam’i aka sawa.

     

    635. Reza za ta zamto rezoji ke nan,

     Wannan da ake saye a yi askin nan,

     Ko kuma wadda an ka yanke akaifan nan,

     Malam lura wagga kalmar rezan nan,

      Z ta birkice zuwa j aka cewa.

     

    636. Gwarzo ya buwaya tilas a yaba shi,

     Ya sha É—amara a yanzu ba masu taÉ“a shi,

     Ya gawurta babu kowa a gaban shi,

     Kowa na faÉ—in mu je ka mu gai da shi,

      Dole yabo ga duk gwarajen Hausawa.

      

    637. Harafin z wajen tilon bai sauyawa,

     Lura da kyau shi tilonsa ba ya canzawa,

     Banza, banza-banza, ai z ka biyowa,

     Reza in guda tazo z aka sa wa,

      Gun jam’insa lura j shika komawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.