Sauyawar Harufa Cikin Kalmomi

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    609. Nahawun Hausa ya amince da rubutun,

     Hausawa ko sun bi tsarin tun-tun-tun,

     Sun yadda su kyautata wa masu karatun,

     Kuma sun ce a zo da tsari na rubutun,

      Wasu harufa cikin gaÉ“a mai sauyawa.

     

    610. Wasu harufa sukan shige wasu halaye,

     Dus sanda ka gan su malam ka kiyaye,

     Kai azama ka lura, inda sun kai tawaye,

     Don da yawa waÉ—ansu ka gan su a sauye,

      Sai su fito daban-daban tun farawa.

     

    611. Sauyawar cikin gaɓa ɗaya aka yin ta,

     Malam lura ka ga sauyi a cikinta,

     Æ˜ari za ya zo ka duba, ka rubuta,

     Tai daidai ya zan gaÉ“ar an sauya ta,

    Kuma ta zamo gaɓa ta ƙarshen ƙarewa.

     

    612. Duk harufan da wagga doka tas shafa,

     Tilas su kasantu sun bi tsari ba Æ™anfa,

     Babu guda wanda zai zame bai da madafa,

     MatuÆ™ar dai baÆ™i yana nan bagiren fa,

    Wasula masu bin ta su za su gwadawa.

     

    613. Doka ta aminta in za a rubutu,

     Sai a kula kar a duba tsarin sabbatu,

     Ba ma’ana gare su, su masu karatu,

     Ko sun ga abin da an ka zana na rubutu,

    A riƙa kula da sauye-sauye da ka zowa.

     

    614. Ga su guda-guda a nan zan kawowa,

     Babu hayaniya, a bar zance kuwwa,

     Malam bari hanzari ka bar yin gaggawa,

     Zan zano su yadda ba sa rikitarwa,

      Sai a kula da hankali don ganewa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.