Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mutum Zai Yi Wanka Idan Ya Kalli Abin Da Ya Tayar Masa Da Sha'awa

 TAMBAYA (41)

Assalamu Alaekum warahmatullahi wabarakatuhu. Patan malam yana lpy, Dan Allah ina d tambaya

Dan Allah idan mutun ya yi tunani ko ya yi karatun littatafae ko kuma ko ya kallali wani abun d yatayar masa da sha'awarsa, shin sae mutun ya yi wankan janaba kafin ya yi ibada ko kuma kawae tsarki mutun xaeyi?

Sannan miyake wajabta wankan? Allah ya ba da daman amsa minmin

AMSA

Waalaikumus, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Alhamdulillah

Idan har silar karatun littafin ko kuma kallon sai maniyyi ya fita to ya zama dole mutum ya yi wankan janaba

Amman idan ba abin da ya fita to ba za ki yi wankan ba

Domin kuwa wankan yana wajabtuwane ga kowanne baligi namiji ne ko mace silar fitar maniyyi a mafarki ko a farke

Abubuwan da ke wajabta wankan janaba sun hada da fitar maniyyi silar mafarki ko kuma sha'awa, zubar jinin haila ko kuma boyuwar kaciyar namiji a gaban mace duk waɗannan suna wajabta wankan janaba

Rashin yin wankan sabawa umarnin Annabi SAW ne domin kuwa Mala'ikun rahama ba sa shiga gidan da mai janaba yake ciki har sai ya kasance cikin tsarki

Haka kuma kallon abin da kan tada sha'awa ko kuma karanta littattafan da za su gayyato sha'awa suma duk haramun mutum yake aikatawa saboda fadin Allah SWT

( وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ )

المعارج (29) Al-Ma'aarij

Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments