TAMBAYA (37)❓
DAN ALLAH
malam shin normal mutum,kaman wanda ba annabi bane zai iya ganin malaiku? Mal
hakan ya faru dani tun shekarun baya sai na ji tsoro tambaya kar’amin kalon marar
hankali koh mai karya.
Da watan
ramadan ne mun fito za mu sallan taraweeh sai naga haske kalar hasken wata
da sufan mutane suna sallah,hakan ya tayar min da hankali shi ya sa har yau banmanta
ba. Allah ya kara daukaka
AMSA❗
Mutum bazai
iya ganin Mala'ika ba har sai an mayarda gangar jikinsa daga Insaniyya
(Matsayin dan Adam) zuwa Malakutiyya (Matsayin Mala'ika)
Misali:
Lokacin da aka yi tafiyar Mi'iraji da Annabi SAW. Da farko yana matsayin
Insaniyya ne shi ya sa yake tambayar Jibrilu AS menene wannan, ko kuma menene
wancan shi kuma yana ba shi amsa wannan a tafiyar daren ke nan (Isra'i daga
Makkah zuwa Baitul Muqaddis da ke Palestine) amman da aka fara tafiyar Mi'iraji
(Hawa sama ta daya zuwa ta 7 har zuwa fadar Allah SWT) sai aka mayar da shi
siffar Malakutiyya
Haka kuma ya
tabbata a cikin Hadisi na 2 da Imam an-Nawawy ya fitar wanda aka karbo daga
Sayyadina Umar RA, wanda sahabbai RA sun ga wani mutum wanda ba su ga alamomin
tafiya a tare da shi ba, har a karshe Annabi SAW ya ce Mala'ika Jibrilu AS ne
ya zo domin ya koyardaku addininku
(Jami'
at-Tirmidhi littafi na 37 hadisi mai lambata 2616 haka kuma yana cikin Arba'una
Hadith)
Anan kinga
Mala'ika Jibrilu AS ya rikida daga Siffar Malakutiyya zuwa Insaniyya
Haka kuma idan
mutum ya zo mutuwa yana ganin Malakul Maut, wanda shi ma hakan ba ta yiwuwa sai
an mai da mutum daga Insaniyya zuwa Malakutiyya shi ya sa shi yana ganin
Mala'ikun su kuma sauran mutane ba sa iya ganinsu. Wannan ke nan
Warware
Shubuha:
A ilimin
kimiyyar Sararin Samaniya (Astronomy) akwai abun da muke kiransu da suna
Asteroids, Meteors, Meteorites, Fireball da Comets, kowannensu yana da haske
dukda dai daga jikin rana suke samun hasken nasu (Kamardai al-Qamar wato wata
wanda ba shida hasken kansa saidai yana samun haskene daga rana kamardai
mudubi)
Shi wancan
Comet din shi hausawa suke kira da tauraruwa mai wutsiya wadda aikinta shi ne
kado Shaidanun Aljannu masu son zuwa Sama ta daya domin su jiyo maganar
Mala'iku idan sunji sai su sanar da yan uwansu har azo na kasansu shi kuma ya
sanarda bokaye su kuma su sirka gaskiya daya da qarerayi 99
Safford
Meteorite wanda ake kiransa da Willcox Meteorite ya fado ne a garin Safford da
ke garin Arizona na kasar Amurka a 8 ga watan March na shekarar 1884
Ya nutse a
kasa har tsayin kafa 20 (fadinsa kuma yakai kafa 40) da nauyi kilograms 16.5
(kaurin 12 inches). Karfin fadowarsa saida ya zama silar tsagewa da fashewar kofofi
da wundinan gidajen mutane
A yanzu haka
wannan dutse yana Smithsonian Institution's National Museum na gidan tarihi da
ke garin Washington D.C, Amurka ga wanda yake son ganinsa ko kuma taba shi
Su irin
wadannan dutsunan sunada haske a sama kuma hasken rana shi ne yake tarwatsasu
su zamo kamar toka a sararin samaniya. Maybe ko irin wadannan dutsunan kika gani
kamar suna sallah sai qwaqwalwarki ta baki tunanin Mala'ika ne tun da daman su
da haske aka haliccesu
Na biyu kuma,
saidai ince Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.