Sifa

     Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    394. Ita kalmar sifa bayanin zati ce,

     Ko girman jiki idan an tantance,

     Ko launinsa babu sauran wani zance,

     Ita aikinta fayyacewa a taƙaice,

      Domin bayyanar da siffa ga rabewa.

     

    395. A misalan da za su zo duk siffa ne,

    Ƙato, ƙatuwa bayani na sifa ne,

    Guntu, guntuwa a nan duk siffa ne,

    Laduwa santaleliyar yarinya ce,

      Ko kuma santamemiya gun miƙewa.

     

    396. Jibgege da shi da tiƙeƙe sa su,

     Rusheshe a tunkuɗa shi a tsarinsu,

     Ɓulelen ga had da ma ɓarkeken su,

     Kalmomin sifa ka san ba a haɗa su,

      Wagege da tuttuƙe can ga tuƙewa.

     

    397. Launi duk yana bayanin siffan nan,

    Zance ja, baƙi, fari ka san wannan,

     Shuɗi, shuɗiya, kaloli ne sannan,

     Ga kore muna da shi du a kalar nan,

      Haka nan algashi wajen siffantawa.

     

    398. Kalma kowace iri in siffa ce,

     Ko furucinta ya rabe gun zance,

     Sai ka haɗe ta in ta zo ma a rubuce,

     Kai komai yawanta, komai ta gajerce,

      Kalmominta ko guda ba a rabewa.

     

    399. A rubutu na Hausa siffa, sunaye,

     Aiki, ko zaginsa duk in ka kiyaye,

     Ba a haɗe su, ba a sanya su a goye,

     Duk adadin gaɓar sifa in ka kiyaye,

      Kalma ce guda, guda aka zanawa.

     

    400. A misalan da zan daɗo duka siffa ne,

     Shi dai wanga shanƙalallen yaro ne,

     Ga shi fari hala ma wai ko Buzu ne?

    Jibgegen ga santamemen ƙato ne,

      Ƙaton nan baƙi ƙirin nan nika cewa.

     


     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.