Ticker

Suna

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

371.  Suna shi ka fayyace muna kowanne,

 In an ambace shi, an san ko wa ne,

 Suna kowane iri linzami ne

 Jagora yake ga mai shi kowane,

  In ka kira shi mai abin zai waigowa.

 

372. Sunaye ga Hausa ba sa sauyawa,

 Duk yada sun ka zo hakan aka zanawa,

 Ko da sun rabe a baki ga furtawa,

 Idan sun zo rubuce ba a warewa,

  Ga rubutunsu kowane ba a rabawa.

 

373. Tamkar Cindo ne, da Korau, Ko Jimrau,

 Sunayenmu ne na Hausa balle Barau,

 Makau, Mande, Modi, Idi, sa Korau,

 Sun tafi sun nufaci ƙauyen nan Birau,

  Ko Jatau da Wargaji mai horaswa.

 

374. Gun mata muna Indo ko Lado,

Hausawa suna da suna wai Kwaido,

 Sannan ga Bala da Mani da Nalado,

 Ga wata ma da nata suna wai Moddo,

 Mai yatsu biyar da ƙari ce Chindo,

   Ga Fati da Nanuwa sai lalewa.

 

375.  Gun laƙabi mu ce Nasani da Nabube,

 Ga Nabala, Namalam da  Nacabe,

 Sa Na’alu Gadanga, duk har da Narabe,

 Ga su Na’umbe, ga Nahantci da Naturbe,

  Ga Na’abu, Na’ila duk ba a rabewa.

 

376. Maihatsi, Maizuma da Maigero suna nan,

 Maikaza akurki ba ya ƙaunar as ɗin nan,

 Mairago da Maitumaki, sa Maigishirin nan,

 Maimasa da Maisaye sa su waɗannan,

  Ga Mai’eka mai aro bai maidawa.

 

377. Mata na Tabawa sannan Tamakama,

 Wani suna da nig gani wai Tabulama,

 Ga Ciwake ga Taroro na daɗa ma,

 Ga Ta’alu, Tababa, sai na ƙara ma,

  Ga Tamagajiya, Ta’innon Ɗandawa.

 

378. Ɗanlami da Ɗanhusai duk a haɗe su,

 Ɗanjuma da Ɗanja duk kar ka rabe su,

 Ɗanashibi da Ɗanladi duk sai a haɗe su,

 Shi kuma Ɗan’ali saka shi a layinsu

  Ɗanmowa da Ɗantani ɗinga haɗewa.

 

379. Duba misalanga tsaf kana mai gane su,

In ya zo da ɗan da mai sai a haɗe su,

Tamkar yadda an ka zana misalinsu,

Harhaɗa dukkannsu kai har da irinsu,

  Ba a raba su can ga sunan Hausawa.

 

380. Ɗanmaigoro kana ga Ɗanmairakke,

 Ɗanmaidankali ka sa Ɗanmaikeke,

 Ɗanmaisabulu akwai Ɗanmaifanke,

Ɗanmaimarkaɗe da ma Ɗanmaimarke,

  Ɗanmaidoka masu ikon ɗaurewa.

 

381. Cigari, Citumu da Ciwake da Cindo,

 Duk a haɗe su ba rabo, bari kirdado,

 Ci gari, Ci tumu, da Ci wake da Cin do,

 An yi kure, ka bincike duba Lado,

  Bagari Bashiri misalai na naɗewa.

 

382. Bisala, Bakuso ga tsari a haɗe su,

 Masu rubuta Bi sala sun ɓata su,

 Haka ma Ba kuso a duba tsarinsu,

 Duk makamantansu wajibi ne a haɗe su,

Haka Sodangi duk haɗe su ga tsarawa.

 

383. Harshen Hausa ya kasance da nagarta,

 Ya ara sai ya kwakkwahe shi ya inganta,

 A karanta a tsara komai a rubuta,

Sunayen aro idan an Hausanta,

  Ba a raba su gun rubutun Hausawa.

 

384. Abdullahi za ka sa can ga rubutu,

 Haka Abdulwahab abin ya ingantu,

 Abdulmajidu shi ma a rubutu,

 Sai a haɗa su tare komi ya ingantu,

  Haka Abduljalali duk ba a rabawa.

 

385. Misalan da ke sama sai a kiyaye,

 Za ka ga an haɗe dukannin sunaye,

Duk sunan da ka ga Abdul ka kiyaye,

Shi da cikon gabansa kalmar sunaye,

  Ba a raba su can ga dokar Hausawa.

386. In ka raba ganinka sunan Allah ne,

Abdul Wahab ka zana shi kure ne,

 Abdul Majidu ma ka kwaɓa ne,

 Abdul Lahi dai na zana shi kure ne,

  Ko Abdul Jalali duk sai sokewa.

Post a Comment

0 Comments