Ticker

6/recent/ticker-posts

Tanada Kalmomin Wanzanci da Adana su don mai Koyon Al’adar Harshe

Himma Journal of Contemporary Hausa Studies, Vol. 5 No. I: October, 2014, Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua University, Katsina

Tanada Kalmomin Wanzanci da Adana su don mai Koyon Al’adar Harshe

English Rendition as, Collecting and Collating Words Used in Hausa Barbers Tradition for Learners of Language of a Culture

Dr. Bashir Aliyu Sallau
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa Yar’adua UniversityKatsina – Nigeria

Tsakure

Harshe abu ne wanda yake yaɗuwa da kuma mutuwa sakamakon hali da yanayin da masu amfani da shi suka shiga na rayuwar duniya. Wannan al’amari yana faruwa ne sakamakon irin cuɗanyar da take faruwa tsakanin wata al’umma da sauran al’ummomi waɗanda suke maƙwabtaka ta kusa ko ta nesa. Ingantaccen nazari a kan al’adun Hausawa a yau zai ƙara tabbatar da wannan bayani, don kuwa a yau ana fuskantar matsalar ɓacewar wasu kalmomi waɗanda suka danganci al’adu da halin zamantakewar Hausawa a wannan zamani. Misali, ire-iren kalmomin da ake amfani da su wajen tafiyar da sana’o’in gargajiya na Hausawa a yau suna ɓata sakamakon cuɗanyar Hausawa da wasu al’ummomi musamman Larabawa da Turawa. Wannan dalilin ne ya sa aka fahimci dacewar gabatar da wani abu don tanada wasu kalmomi na wanzanci da kuma adana su yadda za su zama jagora ga mai koyon al’adar harshe.

Gabatarwa

Sakamakon bincike da nazarce-nazarcen da masana da manazarta da ɗalibai suka gabatar a fannoni daban-daban na rayuwar Hausawa an fahimci akwai dangantaka makusanciya tsakanin harshen Hausa da al’adun Hausawa. Wannan kuwa ya faru ne saboda da harshe ake furta kalmomin da ake amfani da su wajen tafiyar da dukkan wani al’amari da ya shafi tafiyar da al’adun Hausawa. Dangane da haka, yana da matuƙar muhimmanci ga masu nazarin harshe a wannan zamani su nazarci ire-iren kalmomin da ake amfani da su a fannonin al’adun Hausawa musamman waɗanda suka danganci sana’o’in gargajiya na Hausawa. Kasancewa ta ɗalibi mai nazari a fannonin al’adun Hausawa, kuma wanda ya gaji yin sana’ar wanzanci iyaye da kakanni har na kai matsayin da na gaji mahaifina a matsayin Sarkin Askar Yariman Katsina Hakimin Safana, na ga ya dace in ba da tawa ‘yar gudummuwar ta hanyar fito da ire-iren kalmomin da ake amfani da a wannan sana’a, waɗanda a yau wasu daga cikinsu sun ɓata ba a ko jin ɗuriyarsu a wannan zamani. A tunanina yin haka zai taimaka a tanada su tare da adana su don amfanin mai koyon al’adar harshe.

Harshe da Al’ada a Mahangar Manazarta

Kafin mu yi zurfi cikin wannan nazari yana da matuƙar muhimmanci mu yi waiwaye don ganin irin ma’anar da masana da manazarta da ɗalibai suka ba kalmar harshe da ta al’ada. Da farko za mu fara da kalmar harshe.

A ra’ayin Bagari, (1978), cewa ya yi “harshe kowane iri ne, asalinsa furuci ne a baka ba rubutu kan takarda ko wani abu daban ba”.

Shi kuwa Calɓin, (1984:4), ya bayyana cewa harshe “tafarkin isar da sakonni ne dangane da tunani da motsin rai da buƙatu, ta hanyar amfani da sautuka da fasalin da wata al’umma ta ƙayyade”.

Idan muka dubi ra’ayin Junaidu, (1990), za a ga ya alaƙanta wannan kalma ta harshe ne da tunanin ɗan’Adam, a inda ya ce, “yayin da bil’Adama yake yin tunani yana yin wannan tunani nasa ta hanyar amfani da harshe”. Ya ƙara da bayyana cewa; “yayin da Bahaushe yake tunani yana yin sa ne da harshen Hausa, haka Balarabe da Larabci, Bature da Turanci da sauransu”.

Ƙamusun Hausa (2006:197), na Jami’ar Bayero ta Kano an bayyana cewa, harshe na nufin “hanyar magana tsakanin al’umma iri ɗaya.

Idan muka nazarci waɗannan mabambantan ma’anoni da waɗannan masana suka ba kalmar harshe ma iya yanke hukuncin cewa, kalmar harshe dai na nufin hanyar magana tsakanin al’umma ko hanyar isar da saƙo tsakanin al’umma.

Idan muka koma a kan ire-iren ma’anar da aka ba al’ada za a ga cewa:

Bisa asali kalmar al’ada ta Larabci ce wadda Hausawa suka ara sakamakon shigowar Larabawa ƙasar Hausa. A lugar Larabci kalmar al’ada na nufin wani abu da aka saba yi, ko ya saba wakana, ko aka riga aka san da shi. Da wannan dalili ne wasu masana furu’a ke gabatar da wani zancen hikima mai cewa: “Al’adatul baladi kas sunnah”. Ma’ana ita ce, al’adar da gari ya saba da ita kamar sunna ce” (Bunza, ɗɗɗ).

Bayan da Hausawa suka ari wannan kalma ta al’ada masana da manazarta da ɗaliban ilimin halin zamantakewar Hausawa sun kawo ra’ayoyinsu don bayyana ma’anar kalmar al’ada da harshen Hausa.

Ibrahim, (1982:1), a nasa nazarin ya ba kalmar al’ada ma’anoni iri uku kamar haka:

“Al’ada na nufin haila, watau irin jinin nan da mata suke yi a wata-wata”.

“Al’ada na nufin bin wata hanya don yin maganin gargajiya, misali yin karatu ko tofi ko turare ko zubar da jini da sauransu”.

“Kalmar al’ada tana nufin abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya, waɗanda suka shafi yanayin rayuwar al’umma da dukkan harkokin da suke yi don zaman duniya.

Dangantakar Harshe da Al’adun Hausawa

Akwai makusanciyar dangantaka tsakanin harshe da al’adun Hausawa don kuwa da harshe ake amfani wajen bayyana wasu kalmomi da ake amfani da su wajen tafiyar da wasu harkokin al’ada. Misali, ana amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomin da harshe yake furtawa wajen yin bauta da gaisuwa tsakanin al’umma da kuma ambaton abubuwan da ake amfani da su wajen gudanar da sana’o’in gargajiya na Hausawa.

Ta fuskar addini za a ga akwai keɓaɓɓun kalmomi da ake amfani da su don bayyana abin da ake bauta wa da yadda ake yin bautar. Ire-iren waɗannan keɓaɓɓun kalmomi sun haɗa da ‘Mahalicci’ da ‘Ubangiji’ da ‘Buwayi’ da ‘Allah’ da sauransu. Haka kuma, ta fuskar yadda ake yin bauta, akwai keɓaɓɓun kalmomin da ake amfani da su waɗanda suka haɗa da ‘durƙusawa’ da ‘rusunawa’ da ‘sujada’ da ‘ruku’u’ da sauransu.

Ta fuskar gaisuwa ma akwai keɓaɓɓun kalmomin da ake amfani da su waɗanda suke bayyana al’adun Hausawa. Ire-iren waɗannan kalmomi sun haɗa da: ‘Barka da kwana’ da ‘barka da rana’ da ‘barka da yamma’ da sauransu. Haka kuma, ana amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi don amsa ire-iren wannan gaisuwa, inda ake amsawa da ‘barka kadai’. Ana kuma amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi wajen gaida shugabanni kamar haka: ‘Ranka ya daɗe’ da ‘Yallaɓai da sauransu.

Idan muka waiwaya ta fuskar sana’o’in gargajiya na Hausawa da sauran dukkan al’amuran da suka shafi rayuwar Hausawa za a ga cewa, kowace sana’a tana amfani da keɓaɓɓun kalmomi waɗanda suke bayyana sunayen ire-iren kayayyakin da ake amfani da su a wannan sana’a da ire-iren abubuwan da ake amfani da su wajen aiwatar da wannan sana’a. Misali, idan muka ɗauki sana’ar noma za a ga akwai kayan aikin da ake amfani da su waɗanda suka haɗa da ‘fartanya’ da ‘gatari’ da ‘galma’ da ‘masassabi’ da sauransu duk ana amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi wajen furta su.

A sana’ar ƙira ma akwai kayan aikin da ake amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi don bayyana su waɗanda suka haɗa da ‘muntalaga’ da ‘awartaki’ da ‘matsoni’ da ‘zuga-zugi’ da sauransu.

Haka wannan al’amari yake a sana’ar fawa inda ake amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi don bayyana sunayen kayan aikin da ake amfani da su waɗanda suka haɗa da ‘barho’ da ‘jantaɗi’ da ‘tukufa’ da ‘tsinka’ da sauransu.

A taƙaice dukkan wata sana’a da Bahaushe yake yi don biyan bukatun rayuwarsa na yau da kullum tana da ire-iren sunayen da ake kiran kayan aikin da ma irin aikin, kuma ana amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi na harshen Hausa wajen furta su.

Sana’ar Wanzanci

A Hausance, sana’ar “wanzanci” tana nufin amfani da askar aski domin yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya don cire belun-wuya. Sana’ar wanzanci ba ta tsaya a nan ba don kuwa ana amfani da ‘yar tsaga don yin ƙaho da cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. A sana’ar wanzanci dai ana yin hujen kunne da yanke yatsan cindo (shiddaniya) da yanke linzami a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma masu yin sana’ar wanzanci na bayar da magungunan gargajiya ga waɗanda suke buƙata (Sallau, 2009:45).

Domin yin aikace-aikacen da suka danganci sana’ar wanzanci akwai kayayyakin da ake amfani da su waɗanda kowanensu yana da irin keɓaɓɓaen sunan da ake kiran sa da shi. Haka su ma ayyukan da ake yi, kowane aiki akwai irin keɓeɓaɓɓen sunan da ake kiran sa da shi. Dangane da haka ne, za a bi waɗannan fannoni na sana’ar wanzanci don tanada ire-iren waɗannan keɓaɓɓun sunaye da ake amfani da su wajen gudanar da wannan sana’a. Yin haka zai taimaka wajen taskace su da adana su domin amfanin mai koyon al’adar harshen Hausa.

Sunayen Keɓaɓɓun Kalmomin Kayan Aikin Wanzanci

Aska: Ana amfani ita wajen yin aski kuma ƙarama ce madaidaiciya, tsawonta bai kai kamu ɗaya ba. Akwai bambanci tsakanin wadda ake askin jarirai da wadda ake yi wa manya aski. Ta askin jarirai ba ta kai girman wadda ake yi wa manya aski ba. Da kuma askar aski ake amfani wajen yin kaciya, ana amfani ne da irin wadda ake yi wa manya aski watau mai kaifi da nauyi wajen yin kaciya. A halin yanzu ana amfani da askar aski iri uku, akwai ta asali ta baƙin ƙarfe. Irin wannan aska ita wanzamai suka gaji amfani da ita, kuma maƙeran Hausawa ne suke samar ta ita ga wanzamai.

Dutsin Washi: Dutsin washin asaken aski dutsi ne ƙarami mai sulɓi da ake amfani da shi domin yin washin asaken aski idan kaifinsu ya dakushe, wato kaifinsu ya ragu.

Fata: Fatar dabbobi ce ake samu daga wajen dukawa wadda aka jeme don wasa askar aski bayan an wasa ta da dutsi. Ana amfani da mai faɗin misali inci ɗaya da rabi, tsawonta kuma misalin inci goma sha biyar zuwa ashirin.

Kalaba: Kalaba ƙarfe ne ƙarami da ake amfani da shi don cire belun-wuya wanda tsawonsa misalin inci shida ne zuwa bakwai, kuma ba shi da kauri sosai. Maƙera ne suke ƙera kalaba, ba kuma dukkan maƙeri ne yake ƙirar kalaba ba, akwai maƙera na daban masu ƙera ta. Ana yin ta ne da kaifi a gefe ɗaya na kanta sai a lanƙwasa kan ya zamo kaifi ciki. A kan yi wa gindinta kauri domin a ji daɗin riƙewa idan za’a yi aiki da ita.

Ƙoshiya: Ƙoshiya itace ne ƙarami ake sassaƙawa da ɗan faɗi ga kai da kuma kauri ga gindi don taushe harshen wanda za a cire wa belun-wuya. Tsawon ƙoshiya misali inci shida ne zuwa bakwai, faɗin kanta kuma bai iyar da kai inci ɗaya ba. A taƙaice tsawon ƙoshiya ɗaya yake da na kalaba.

‘Yartsaga[1]: Aska ce ƙarama da maƙera suke ƙerawa, tsawonta ya kai misalin inci huɗu zuwa biyar, kanta kuma ana yin sa da faɗi da tsini da kaifi. Wasu maƙera na amfani da ƙusa inci huɗu ko inci biyar domin yin ‘yartsaga. Ana amfani da ‘yartsaga wajen ayyukan wanzanci domin yin wasu ayyukan da wanzamai suke yi a farjin mata kamar cire angurya da yanke linzami da cire haƙoran shuwa. Ana kuma amfani da ita domin yin tsagar gado da ta magani da kuma ta kwalliya.

Hantsaki: Ƙarfe ne da maƙera suke ƙerawa da baki a gindi da kuma tsini a kai. Ba shi da kauri sosai, kuma tsawonsa misalin inci huɗu ne. Ana amfani da hantsaki domin cire angurya a farjin mata.

Ƙaho: Ƙahon sa ne ake gyarawa domin yin ƙaho a jikin mutum don magance wata cuta. Ana amfani da wannan keɓaɓɓar kalma don bayyana sunan kayan aiki da shi kansa aikin, kuma ana amfani da ƙaho madaidaici wanda ba mai girma ƙwarai ba, kuma ba ƙarami ba don yin aikin. Ana yanka misalin tsawon inci biyar ko shida. Ana yi wa wajen tsininsa ‘yar ƙaramar ƙofa.

Jijiya: Jijiyar agarar ƙafar akuya ko tunkiya domin a riƙa liƙƙofar tsinin ƙahon da a aka kafa wa mutum domin ya liƙe wurin da aka kafa shi a jikin mutum.

Kura: Ƙugiya ce ta ƙarfe wadda ake amfani da ita wajen cire haƙori mai ciwo ko mai girgiɗa, yanayinta ya yi kama da abin da kafintoci suke cire ƙusa, amma ita kura ba ta kai girman abin cire ƙusa ba.

Tankolo: ‘Yar jika ce wadda dukawa suke ɗunkawa da fatar akuya ko tunkiya domin wanzamai su riƙa sanya askar aski ɗaya ko kuma babba wadda za a sanya asaken aski masu yawa.

Zabira: Jaka ce babba mai aljihuna da yawa misali uku ko huɗu. Ana yi mata maratayi domin a riƙa ratayawa. Ita ma dukawa ne suke ɗunka ta da fatar akuya ko tunkiya domin yi wa wanzamai abin da za su riƙa sanya dukkan kayan aikin wanzanci waɗanda aka yi bayaninsu a baya.

Sunayen Keɓaɓɓun Kalmomin da Ake Amfani da su Wajen Aski

Ƙwaryar-Molo: Aske gashin kai duka da askar aski ko reza.

Ƙwal-a-Kwaba: Aske gashin kai duka da askar aski ko reza.

Tal-a-Kwaba: Aske gashin kai duka da askar aski ko reza.

Maraba-da-Gora: Aske gashin kai duka da askar aski ko reza.

Saisaye: Amfani da almakashi a rage yawan suma daidai-wa-daida.

Ciko: Amfani da almakashi a rage yawan suma a baya a bar ta gaba da yawa.

Ƙahon-Barewa: Gyaran fuska ne da ake yi wa Hausawa da Fulani inda ake gyara gashin da yake wurin goshi a kuma aske dukkan saje tun daga wurin da ya haɗu da sumar kai har zuwa wurin gemu.

Zanko: Wani nau’in aski ne da ake yi wa ‘ya’yan Hausawa da Fulani inda ake aske gashin kai na ɓangaren hagu da na dama a bar gashin tsakiyar kai kamar layi tun daga goshi har zuwa ga ƙeya.

Bawale: Aski ne da ake yi wa jarirai da yara ƙanana waɗanda kafin a haife su an haifi wasu suka mutu, watau ‘ya’yan wabi. Ana fara yin irin wannan aski lokacin da za a yi wa jaririn askin yada wanka, kuma za a ci gaba da yi masa irin wannan aski har sai lokacin da za a yi masa kaciya sannan a aske shi. Yadda ake yin irin wannan aski shi ne, da farko za a fara aske gashin kansa na ɓangaren dama, idan suma ta sake tsirowa sai a aske na ɓangaren hannun hagu. Haka za a yi ta juyawa har zuwa lokacin da za a yi masa kaciya. An keɓe wannan suna ga irin wannan aski da kuma wanda ake yi wa irin wannan aski.

Tukku: Gashi ne ake bari curi-curi a wurare daban-daban a kan yara maza ko manya don kwalliya ko riƙo da al’ada ko don muzantawa.

 Sunayen Keɓaɓɓun Kalmomin da Ake Amfani da su Wajen Cire Belu

Belun-Wuya: Tsokar nama ce wadda take kusa da maƙogaro a ƙuryar dasashin sama cikin bakin mutum. Ana kuma ce mata hakin-wuya.

Laɓɓe/Linzami: Zirin nama ne wanda yake haɗe harshen mutum da dasashin ƙasa. Idan ba a tsage shi ya rabu ba magana ba za ta fito sosai ba.

Haƙoran-Shuwa: Wata irin tsokar nama ce fara wadda take kamanni da haƙori da take tsirowa a dasashin jarirai.

Belun-Mata: Tsokar nama ce wadda take tsirowa a cikin farjin mata ta toshe ƙofar farjin yadda ko fitsari ba zai fito sosai ba.

Gurya/Angurya: Wani farin abu ne da yake tsirowa a farjin mata wanda yake kama da gurya da ake fitarwa a wurin auduga ya toshe ƙofar farjin mata yadda ko fitsari ba zai fito sosai ba.

Shafaffa/Sadadda: Mace wadda ƙofar farjinta ta shafe yadda ko fitsari ba zai fito sosai ba.

Sunayen Keɓaɓɓun Kalmomin da Ake Amfani da su Wajen Tsaga

Ɓalli-ɓalli: Tsaga ce da ake yi wa yara masu shekara biyu zuwa goma da haihuwa don maganin yawan ciwon zazzaɓi. Ta samo wannan suna ne sakamakon yanayin ciwon wanda idan ya kama yaro, idan aka taɓa daidai wurin da zuciyarsa take sai a ji tana harbawa da ƙarfi ɓal-ɓal.

Zarar Danshi/Mafigiya/Fitar-Ruwa: Tsaga ce da ake yi a tsakiyar goshi kamar fashin-goshi na Barebari domin maganin zazzaɓi mai zafi da kan kama yara waɗanda suke da shekara biyu zuwa goma da haihuwa.

‘Yan Jarfa: Wanzaman da suke yi wa ‘yan mata tsagar kwalliya.

Tambara: Budurwar da iyayenta da ‘yan’uwanta suke nuna wa so da ƙauna.

Tagumin-Gafiya: Tsaga ce wadda ake yi wa mata a ƙasan leɓen ƙasa an fi yi wa Kanawa da Gobirawa da Zamfarawa irin wannan tsaga.

Kwale: Tsaga ce wadda ake yi wa ‘yan mata a kundukuki daidai saitin idanu.

Kalangu: Tsaga ce ƙarama wadda ake yi a fuska daidai saitin kunnuwa, kuma an fi yi wa Katsinawa irin ta.

Garɗin-Gero: Tsaga ce da ake yi wa mata a wuya wadda ta yi kamanni da bishiya.

Kwanciya-da-Masoyi: Tsaga ce wadda ake yi wa mata a hannu daga kusa da kafaɗa zuwa kusa da guiwar hannu. Ita ma ta yi kamanni da bishiya.

Matakin-Soro: Tsagar kwalliya ce wadda ake yi wa ‘yanmata a tsakiyar goshi daidai saitin karan-hanci. Irin wannan tsaga ana yin gado huɗu zuwa shida kurkusa da juna.

‘Yarbaka: Tsagar kwalliya ce wadda ake yi wa ‘yan mata a kumatu ta haɗe da wutsiyar baki. Wannan tsaga gado ɗaya ce kuma ana yin ta caɓa-caɓa a kumatu. Wasu kan kira irin wannan tsaga da sunan cika-baki.

Me-ka-ce-Maigida: Tsagar kwalliya ce da ake yi a kafaɗun mace daidai saitin ƙashin da ya fito daga wuya ya haɗe da kafaɗa kuma gado ɗaya ce. Ana yin irin wannan tsaga a kowace kafaɗa.

Sunayen Keɓaɓɓun Kalmomin da Ake Amfani da su Wajen Kaciya

Bakin-Jaɓa: Azzakarin yaro wanda lokacin da aka zo yi masa kaciya ya gagara talawa, sai dai a yi masa kaciya haka nan ba tare da an wanke ba.

Loɓa: Fatar da ta lulluɓe kan azzakarin yaron da ba a yi wa kaciya ba.

Tamalmala: Wani abu ne mai kamanni da kitse wanda akan samu saman azzakarin yaron da ba a yi wa kaciya ba.

Kari: Gudummuwar da ‘yan’uwa da abokan arziki suke bayarwa a lokacin da aka yi wa yaro kaciya.

‘Yankara: Sullen karan dawa ne ake samu a yanka guntu-guntu. Ana samun sulle madaidaici domin yanka ‘yankara. Ana yanka kowane guntu misalin tsawon inci ɗaya. Ana amfani da ‘yankara ne a wurin kaciya inda ake rarake uku a saka zare a cikin kowane sai a ƙulla zaren yadda ‘yankaran za su yi kusurwa uku, daga nan sai a rataya wurin kaciya tsakanin azzakarin yaron da ‘ya’yan golayensa. Amfanin ‘yankara wurin kaciya shi ne su raba azzakarin yaron da ‘ya’yan golayensa yadda kaciyar za ta riƙa samun iska, kuma ba za ta riƙa liƙewa da ‘ya’yan golayen ba.

Karkiya: Karan dawa ne mai ƙwari ake samu a yanka tsawon misalin inci goma sha biyar zuwa inci ishirin. Ana amfani da ƙarkiya ne ga yaron da aka yi wa kaciya lokacin da zai kwanta barci, sai a ɗaura ta wurin cinyoyinsa domin kar ya manta ya haɗƙafafuwansa su matse kaciyar ya yi fami.

Sunayen Keɓaɓɓun Kalmomin Wasu Fannonin Wanzanci

Kushekara[2]Ƙashin baya da tsokar nama wadda ta lulluɓe shi tun daga doron wuya zuwa tsakiyar baya na dabbar suna. Ana ba da wannan nama ga wanzamin da ya yi wa jaririn da aka haifa aski da sauran ayyukan wanzanci.

Karfata: Ƙafar gaba ta dama ko ta hagu wadda ta dabbar suna wadda ake yankewa don ba wanzamin da ya yi wa jaririn da aka haifa aski da sauran ayyukan wanzanci.

Ƙwarya: Dawa ko gero ko masara ko shinkafa haɗe da kayan yaji da ake ba wanzamin da ya yi wa jaririn da aka haifa aski da sauran ayyukan wanzanci.

Kammalawa

Dangantakar da take tsakanin harshen kowace al’umma da al’adunta abu ne wanda yake fili kuma ya kamata a ƙara tanada shi da adana shi don amfanin masu koyo da koyarwa. Za a ƙara fahimtar haka idan aka nazarci ire-iren keɓaɓɓun kalmomin da ake amfani da su a fannonin rayuwar Hausawa ta yau da kullum. Haka kuwa ya faru ne saboda a al’adar Hausawa kowane fanni da ya danganci gudanar da al’adar ana amfani da wasu keɓaɓɓun kalmomi da a mafi yawancin lokaci, za a tarar sun dace da muhallin da ake amfani da su. Kamar yadda aka fito da ire-iren keɓaɓɓun kalmomin da ake amfani da su a fannonin da suka haɗa da halin zamantakewar Hausawa da shigabanci da sana’o’in gargajiya da sauran fannoni kamar yadda aka kawo su a wannan nazari zai ƙara taimakawa wajen ƙara tanada su da adana su ga masu koyon harshen al’ada.

MANAZARTA

Alhassan, H. da Wasu, (1982) Zaman Hausawa. Zariya: Institute of Education Press, ABU.

Bargery, G. P. (1993) A Hausa – English Dictionary and English – Hausa Vocabulary, Zaria, ABU Press.

Bagari, D. (1978) “Rubutun Ajami da na Boko”. Maƙala da aka Gabatar a Taron Ƙara Juna Ilimi Kan Ajami, Kano: Jami’ar Bayero.

Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al'ada, Jerin Litattafan Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa, Lagos: TIWAL.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeiya, (2006) Ƙamusun Hausa, Jami’ar Bayero, Kano. Zaria. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Garba, Y. C. (1984) Nazarin Hausa, Lagos, Nelson Pitman.

Junaidu, I. (1990) “Dangantakar Harshe da Tunanin ɗan’Adam, Maƙala da aka Gabatar a Bikin Makon Hausa na Ashirin. Kano: Jami’ar Bayero.

Ibrahim, M. S. (1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Musa, R. (1983) “Wanzanci a Ƙasar Hausa: Asalinsa da Yanayinsa da Matsayinsa Jiya da yau”, Kundin Digiri na Ɗaya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B. A. (2008) “Ƙaho: Matsayinsa na Hanyar Warkarwa a Al’adar Hausawa da Addinin Musulunci”, Takarda da aka Buga Cikin Mujallar Taguwa. Katsina: Tsangayar Kula da Halayyar ɗan’Adam,  Jami’ar Umaru Musa.

Sallau, B. A. S. (2000) ”Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B. A. S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye – Sauyen Zamani Jiya da Yau”, Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sallau, B. A. (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: M. A. Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.

Sallau, B. A. (2010) Magani a Sha a yi Wanka a Buwaya. Kaduna: M. A. Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.

Sallau, B. A. (2011) “Raɗa Suna Jiya da Yau”, Takarda da aka Buga Cikin Mujallar Himma . Katsina: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.

Sheriff, B, (2000) “The Kanuri Barber and His Art”, in Borno Museum Society Newsletter, Number 42 and 43. Maiduguri: The Ƙuarterly Journal of Borno Museum Society.

Sharifai, B. I. (1990) “Take da Kirarin Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsu ga Rayuwar Hausawa. ”Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Suleman, A. H. (1990) “Tsagar Gargajiya a Ƙasar Kano: Nazarin Ire-Iren Tsaga da Muhimmancinsu ga Al’ummar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Wurma, A. G. (2008) “Kalma Ɗaya Ma’ana Tuli a Hausa”, Takarda da aka Buga Cikin Mujallar Algaita ta 5, Fitowa ta 1. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.



[1] Wasu na kiran ‘yartsaga da suna jarfa, kuma daga nan ne aka sami salon maganar da Hausawa suke yi, inda suke cewa, “Wanzami ba ya son jarfa”. Dalili kuwa shi ne, da jarfa ake amfani wajen yin tsaga, idan an tsaga jiki za a ji zafi, don haka, wanzami ba ya son ya ji zafi a jikinsa.

[2] Saboda irin muhimmanci da kushekara take da shi a matsayin wani ɓangare na biyan ladar aiki a cikin sana’ar wanzanci ya sa a cikin ire-iren kirarin nuna jaruntaka da Hausawa suke yi suke cewa, “kushekarar Jaki sai wanzami Kura”.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments