Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
708. Larabci yana da h ga rubutunsa,
Shi ne ya wakilci h haruffanmu na Hausa,
Kwai ha babba ga ƙarami kuma na bin sa,
Ha babba muke da
sautin na Hausa,
Ba mu da mai ruwa daɗai mu Hausawa.
709. Ba mu faɗin “Khadija” balle mu rubuta,
In ka lura mai
ruwa an ka rubuta,
Ita ko Hausa babu
shi ga haruffanta,
Sai dai h ka lura in za ka karanta,
Lura da kyau “Hadiza” za mu rubutawa.
710. “Alkhairi” a bar wa Larabci wannan,
Shi ma dai ruwa
sun ka yi wannan,
Ai tsarin rubuta
Larabci ne nan,
Ita ko Hausa ba a
samun ta da wannan,
“Alheri” da Hausa shi za ku rubutawa.
711. Al’ummah a ɗebe h don ƙari ce,
Kar ka saka ta ka
ga ai Larabci ce,
In aka sa ta
ma’ana ta lalace,
An saɓa ma ƙa’ida an dabirce,
Al’umma wajen
rubutu aka sawa.
712. Ba mu da “p” da “q” da “x” don a kiyaye,
Turanci ya zo da
su Hausa ta jaye,
Ba ta da hurrumi
da su sai a kiyaye,
In aka sa su to ka
san an yi tawaye,
Ba mu da “v” ga Hausa don ƙara kulawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.