Tattaunawar Ilimi Cikin Waiwayen Tarihi a Zauren Makada da Mawaka

    ... Dangane da masu alfarma sarakunan Zazzau...

    Malam Abdu Sani

    Amma wannan tauye tarihi ne . Domin kuwa ba shi ne Sarkin Zazzau na 19 ba . In an yi haka ba aiwa tarihin masarautar Zazzau adalci ba saboda sauran Sarakunan don ba Fulani ba ne shikenan an share na su tarihin kenan bacin a kan ginshikin wadancan Sarakunan a ka dora ita sarautar ta yanzu. Kuma kafin zuwan shi wannan Sarkin Zagezagi kaf suna ganin kan su a matsayin’yan Zazzau ba wani banbanci. Kuma masarautar ana fassara ta a gida uku ne cewa 1: Gidan Katsinawa 2: Gidan Barebari 3: Gidan Mallawa. Ba wani da yake cewa gidan Fulani or whatever. Kuma Sarkin Zazzau ai Sarkin duk wanda ya ke kasar Zazzau ne ba Sarkin Fulani ba ne kawai. Bugu da kari nan gaba za’a samu wasu su ma dan takama da na su usulin su samo Sarkin Hausawa na 20 ko Sarkin Barebarin Zazzau na 11. Kuma dai don Allah Wai meye ribar wannan kirgen salsalar? Yanzu ya za mu ji in Yarabawa su ka fara kiran Tinubu da Shugaban Nigeria Bayarabe na 3? Does it make any sense. Again nan gaba za’a manta da alaqanta shi da Fulanin a riqa cewa Sarkin Zazzau na 19 kawai wanda wani da bai san sha taran ta kowanne jinsi ce ba zai bi usulin tarihi ne kawai wanda sai aga cewa Sarkin Zazzau na 19 original watakila ma ba wanda ya karbi Musulunci ba ne ma. To ka ga garin gyaran gira an tsone ido. Ya kamata wanda su ke da kafa a masarautar Zazzau su ba su shawara cewa wannan lissafin kuskure ne kuma nan gaba yana iya jawo rarrabuwar kan mutanen Zazzau. Allah Ya dora mu a kan tafarki madaidaici amin. Afwan in na yi kuskure ina neman gyara da yafiya. BISSALAM

    Wakar Dr Shata “ Wai a su ukun wa za kai wa habaici? Barebari dai dangi bai ne , Mallawa ma dangi nai ne bare Katsinawa kakannin sa..” A waqar marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris . RahimahuLLAH

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji

    😅🙏✊... Idan na samu natsuwa zan tanka maka daidai gwargwadon fahimta ta da kuma fahimtar abun da ka bijiro dashi Allah ya gafarta Malam kuma Mai Girma Majidadin Ɗanmadamin Birnin Magaji ✊✊

    Malam Abdu Sani

    Rumbun ilmi da tarihi Maigirma Danmadamin Birnin Magaji daman mun kwana biyu ba mu dauki karatu ba. Allah Ya kara basira. Amin. Godiya mu ke. Majidadin Danmadamin Birnin Magaji. 👍👍🙏

    Malam Aminu Mairuwa , Esq:

    Salam, Maigirma Alhaji Abdu Sani barka da dare Yallabai. Duk da yake Maigirma Danmadamin Birnin Magaji ya ce zai bada amsa idan ya natsa, zan so inyi shishshigi irin namu na kananan  almajirai masu neman ilimin tarihi. Nasan InshaAllah Maigirma Danmadami zayyi cikakken bayani idan Allah yasa an natsa.

    Tare da girmamawa gaskiya babu wani tauye tarihi akan wannan magana ko shiri da akayi. Musamman abinda ya shafi ce ma Maimartaba Sarkin Zazzau Amb Ahmad Nuhu Bamalli na 19. Wannan gaskiya ne kuma babu shakka ko wani kuskure akan hakan. Idan mun tuna ance shine Sarki na 19 a Daular Sarakuna Fulani, ba wai ance sarki na 19 ba tun da aka fara sarauta a Zazzau. Abin lura shine Fulani sun fara sarauta a Zazzau a 1804 bayan da Sarkin Zazzau Mallam Musa Bamalli ya amso tutar Jihadi kuma ya fara mulki a 1804 din. Idan aka lissafa sarakunan Zazzau daga Sarki Mallam Musa a 1804 zuwa Sarkin Zazzau Amb Ahmad Nuhu Bamalli a yau dinnan 8 October 2023 anyi sarakuna 19. Hakan ya nuna kenan babu ja shine Sarki na 19 a Daular Fulani.

    Yamata a lura babu wanda ya taba kore samuwar sarakunan Habe da suka fara mulki a Zazzau daga 1486 har zuwa Sarkin su na Karshe Sarki Muhammadu Makau a 1804. Don haka idan za a  lissafa ana bambamcewa da cewar sarakunan Daular Fulani domin saukin fahimta, amma fa ba wai don kore samuwar sarakunan baya ba.

    Akan maganar gidajen sarautar Zazzau, ba 3 bane , guda 4 ne. Akwai gidan Fulani Mallawa, Gidan Fulani Barebari (Fulata-Borno), Gidan Fulani  Katsinawa da Gidan Falani Sullubawa.

    Bani tsammani wani ya taba cewa Sarkin Zazzau ba na zagezagi bane, karewa ma shi kanshi Maimartaba Sarki Bazazzagi ne. Babu wani nuna bambanci sam idan an kira shi da Sarkin Zazzau na 19 a Daular Fulani domin kuwa tarihi ne na zahiri ya kawo haka, kuma tarihi ba karya bane. Duk wani abu da aka fadi a kan Sarkin Zazzau da masarautar Zazzau ba molon ka bane , tarihi ne kuma yana nan a rubuce.

    Akan musakin kiran President Tinibu da Shugaban Kasa na 3 Bayarbe.  Idan  wani ya kira shi haka  ba laifi domin hakan take a tarihi ( idan an kirga da shugabancin Obasanjo a  soja).

     Wannan babu kuskure a cikin kuma gaskiya ne domin tarihi ne. Haka ma idan aka kira Buhari da Shugaban  Njgeira na 9 Bahaushe babu wani kuskure.( Sai dai a lura ban sako fahimtar wasu ba akan cewar Tafawa-Balewa Bageri ne, Murtala da Shagari Fulani, Abacha Babarbare, Buhari Fulani . Wannan wata fahimta ce mai zaman kanta kuma ni ba wannan bangaren nike kallo ba a yanzu. Kuma ko ma  menene su wadannan shugabanni babu wanda zai cire su daga farfajiyar Hausa domin dukkan su ko 'zo in kashe ka' basu ji da wancan yarukan  da ake hada su  dashi. Karewa ma irin su Abacha dan Kano ne , nan aka haife shi kuma ita ce garin shi a hukumance . Barbancin shi kawai a tsaga ne da ke fuskar shi da kuma sunan mahaifinshi da kuma kila ace asali) .

    Lissafa Sarakuna akan yadda suka samu ba akan Zazzau aka fara ba. Duk dauloli tsaffi da suka wanzu tun kafin Jihadi haka ake lissafa sarakunan su. Ko yanzu idan za a fadi Sarkin Kano a tarihance  za a ce na 15 a Daular Fulani (Sullubawa). Idan zaka fadi Sarkin Katsina na yanzu ma  za a ce na 4 a Daular Fulani Sullubawa shi ma. Don haka yake babu ko shakka a tarihi kuma ba wani rabuwar kai da hakan zai kawo. Domin kuwa su wadannan daulolin dinkakku ne basu da wani wake- da -shinkafa da har wani zaiji an ware shi. Da Sarki da talakan karshe a garin duk harshen su daya kuma addinin su daya akan marinjayin yanayi (in a majority instance).   

    Ba kayi wani kuskure ba Maigirma  Alhaji Abdu Sani domin fahimta fuska ce . Haka kuma babu wani da ya kewaye da sanin komai sai Allah. Ni ma karambani ne nayi kuma zan iya kuskure . Idan anga kuskure ko karin bayani sai a gyara ko ayi karin bayani din. Na hado wannan rubutun nawa da ratayen hujjoji domin dogaro. Akwai littafin Government in Zazzau da tsakure a cikin shi. Bissalam

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji

    Ma Shaa Allah laƙuwata illa billah!!! Mai Girma Dokaji Magajin Garin Dikko Na Korau sannu da hwama, muna godiya sosai da wanga gamsasshen bayani. Allah ya ƙara hasken Makaranta. Inji Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni da ya tafi gidan Tafidan Kabi/Tafidan Argungu Arzika sai yacce "Arzika mun tabbata Gidan Sarkin Kabi ka wuce ace haye nai kayyi" a cikin hwaihwan shi mai amshi "Ɗan Hassan madagora, Mai dama da hauni kayi jinkiri, ka gadi Muhammadu shirin ku ya zo daidai", saboda haka babu karambani ko shishshigin da kayi a wannan bagiren, ka kuma yi muna bayani dalla - dalla.


    Allah ya gafarta Malam kuma Mai Girma Majidadin Ɗanmadamin Birnin Magaji, Malam Abdu Sani Kano dafatar ka fahimci dalili/dalilan kiran Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamali CFR da laƙabin Sarkin Zazzau Na 19 a tsarin Sarakunan Masarautar Zazzau da Daular Fulani ta samar ya zuwa yau.

    Ka kuma ji cewa idan an ƙirga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Ƙasa Bayarabe na biyu ko na Uku (duba da karo biyu Cif Obasanjo ya yi mulki a Nijeriya) ba laifi ba ne a Tarihance, kamar yadda za a iya kiran sauran Shugabannin da aka yi a Nijeriya da nasu Yaren/Harshen.


    Bayan Wafatin Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam a Tarihin Musulunci sai aka samu Khulafa'ul Rashidun su huɗu, bayan wafatin su wasu Sahabban sun biyo bayan su, bayan su kuma wasu sun biyo su har aka cimma inda aka fara samar da Sarakuna musamman da samuwar Dauloli daban-daban a wurare daban- daban kuma ya zuwa yanzu idan aka zo bayar da Tarihin kafuwar Musulunci ta wannan sigar( kamar yadda aka bayar da na Daular /Masarautar Zazzau) ake bayar da shi. Babu kuma tauyewa a cikin wannan lamari domin ba a hana a yi waiwayen /tariyar baya ba domin kawo Tarihin waɗan da suka yi mulki a can baya ba, idan kuma aka tsaya akan hakan babu laifi domin ba a iya ƙwacewa Tuwo sunan sa.

    Zan yi burki anan domin kamar yadda Marigayi Mai Martaba Sarkin Zuru, Jihar Kebbi Alhaji Usman Danga ya ce a wani taro da aka kira shi ya yi jawabi bayan Tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Sakkwato ( a lokacin Zuru tana cikin Jihar Sakkwato) Kanal/Burgediya Ahmed Muhammad Daku ya faɗi kusan dukan abun da ke cikin zuciyar sa a lokacin nasa jawabin, sai Marigayi Mai Martaba Sarki ya ce "Tau babu abun da zan ce, don komi zan hwaɗi Yaron ga Daku Ta Riga ta kwashe ta hwaɗi, saura dami Allah Ta watce ku lahiya" 😅😅🙏✊✊

    *** ***
    Ka na da taka gaskiyar Mai Girma Ɗanmaliki domin fahimta akan ce "fuska".

    Kamar yadda Tarihi ya amince da Rise na Daula to haka ma ya amince da Fall na wannan Daular. Kenan Rise And Fall Of Kingdom /Empire gaskiya ne akwai shi. To kuwa tun da lamarin juyi - juyi ne yakamata mu yarda da juyi a cikin irin wannan lamari.

    A wasu Daulolin da basu samu shigowar wasu al'umma daban  a sha'anin mulkin su ba, ya zuwa yau babu irin wannan lissafi a tsarin Sarakunan su. Misali, duk da cewa Daular Gobir ta faɗi a farko farkon ƙarni na 19 kuma Fulani sun karɓe ƙarfin mulki daga wajen su tun a lokacin, amma rashin shigar Fulani a cikin tsarin mulkin su ya zuwa yau idan ana lissafin Sarakunan Gobir ana farawa ne tun daga Gubur zuwa Sabon Birnin Gobir /Tcibiri akan lissafa Sarakuna ɗaruruwa amma ba zaka ji an ambaci na wata ƙabila ba 'Kai tsaye za a ce Sarakunan Gobir'.

    Daga shekarar 1515 da Muhammadu Kanta ya ƙirƙiri Daular Kabi/Kabawa /Lekawa ya zuwa yau 08/10 /2023 sun yi Sarakuna 33, duk da faɗuwar Daular a lissafin Sarakunan su babu tantama su dai ne ake lissafawa, saboda me? Saboda Daular ce kurum ta faɗi ba a samu sabbin al'ummar da suka shiga a cikin tsarin mulkin Daular ba duk kuwa da amshe Hedikwatar ta a Takalafiya /Birnin Kabi(Birnin Kebbi) da samar da Argungu da Sarkin su Nabame ya yi a cikin 1840s.

    Tun daga 1300 da Dakka ya samar da Daular Zamfara da hedikwata a Dutcin Zurmi, duk da mamaye su da Gobirawa suka yi a cikin 1760s a sabuwar hedikwatar su dake Birnin Zamfara ya zuwa yada zangon da suka yi a Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro da Tunfafiya da Sabon Garin Damri har zuwa komawar su a Anka tsakanin 1815 zuwa 1824 inda suke a halin yanzu, ya zuwa yau wajen lissafin Sarakunan su ana cewa ne "Sarkin Zamfara/Sarakunan Zamfara, saboda me? Saboda Gobirawan da suka mamaye su a cikin 1760s basu shigo a sha'anin mulkin su, haka ma Fulanin da suka karɓi mulkin su daga Gobirawan da suka mamaye su ba su a cikin sha'anin mulkin su.

    Da wannan nike cewa kuna da taku hujjar jan wannan zance, kamar yadda muke da tamu hujja ta tsayawa akan tamu hujjar amincewa da wannan tsari. Allahu Wa'alam!!!

    Malam Nakwada

    Godiya Rankaidade da qara ilmantar da ni da kayi. 

    Amma Rankaidade ka qara bude bayanin da nayi tun farko. Misalan da ka kawo na Daular Gobir da Kanta-Aegungu; ina gani suma da ace fulani sun kafa tutar su a can aka tura wani ya amahe masu mulki, ko da ba a wargaza masarautar/Daular su ba, da yanzu ana nan ana yi masu irin wanga lissafin tarihin na qabilanci. Da za kaji ana Sarkin Argungu na 18 a mulkin Fulani 🤷‍♂️😀

    ***
    To ai kuwa idan aka yi haka ba a yiwa mutanen wadannan yankuna adalci ba. Ya za ace wata kabila ta zo ta kwace sarauta ta mulki mutane kuma sai ta yanke tarihin su ta jona daga inda nata ya fara??🤷‍♂️😀

    Ba fa canza mutanen nasarutun aka yi ba. Su din ne dai tun na fil azal. Sarautar ce kawai wata qabila ta qwace da qarfi.

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji

    Ba a yanke ba ko alama tun da ba a kira Mai Martaba Alhaji Ahmad Nuhu Bamali CFR da laƙabin Sarkin Zazzau Na 19 ba ne. An kira shi ne daga lokacin da Ƙabilar tasa ta fara mulki a Zazzau. Kiran sa Sarkin Zazzau Na 19 na Daular Fulani a Zazzau ya bayar da dama/gib'i cewa kenan akwai wasu Sarakunan a wannan Daular/Masarautar kafin Ƙabilar sa su fara mulki har ya zamo na 19. Anan babu Tarihin da aka Tauye, ga masu ra'ayi irin naku wannan ya baku damar bincikawa da waiwaye ko tariyar baya domin gano to su wane ne suka yi mulki a wannan wuri kafin Malam Musa Bamalle da ya fara mulki a matsayin Sarki na farko a Daular Fulani ta Zazzau.

    You have to blow your own Trumpet.... 😅🙏✊
    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.