Tumben Sukari

    Tabbas maza ke maganin jumurin maza,
    In anyi sassarfa da sannu a huta.

    Gumba ta dutse ce kirarin Æ´an maza,
    Wata É—aukakar sai an saye ta da bauta.

    Da kururuwa yaƙi ya ke daɗa turɓune,
    Ihun maza ke razanin mai wauta.

    Hular maza sai dai a sa ma ta ƙoƙuwa,
    Luru abin ƙawa wajen ƴanmata.

    Na kalli kansakalin da naiyo gajiya,
    Zallar ƙarafa ba alamar ƙota.

    Na kutsa dakarun da kowa ke gudu,
    Nai ƙwalli-ƙwalli da ƴan maza sun firgita.

    Na ta da ƙura tunda sanyin safiya,
    Na turnuƙe fili kamar a mahauta.

    Na kai isha'i tun subahi ba jira,
    Ba na ta yunwa ma bare na tuna ta.

    Na kar mutum miliyan dubu sau fam dubu,
    Tawagar da ko Rabbasu zai shakkar ta.

    Tawagar da in aka dangana ta da Hantaru,
    Sai dai ya nemi shiri su barshi ya huta.

    Taron da ko dajjalu yai arba da su,
    Zai ja da baya ganin yawansu zarata.

    Ko hibru ko ma hubru dole su dangana,
    Da ganin mayaƙannan kamar an shata.

    To wa ya kai zafin ƙashi ya mazan jiya,
    Wannan da ba gajiya barefa su huta.

    Ni ko a ran É—ai nai yini da rabin yini,
    Sai ga jini ta samansu na ta shatata.

    Kafin daƙiƙa goma nai fatalin jini
    Tamkar a É“alle kan ruwanya ratata

    A fagen ma'aunin ƙafiya na yo ƙure,
    Na zarce ɗan ƙwairo da mamman shata.

    Na zarce san-mai sabulu har É—an dawo,
    Kai har Haruna uji yana shakka ta.

    Na karkaɗe sharar mawaƙan zamani,
    Ala da farfesa ka bin waƙa ta.

    Wasu ma suna ajabin ta ya har nai haka,
    Ƙwanji da murya duk ana shakka ta.

    Sai ko na ce "ni ne guda mai cin dubu
    A wuri guda don ni na san yarenta"

    Ni ne na ke kwana a zaune ina jira,
    Na jira da kamar dubu na rubuta

    Ni ne idan na riƙe maƙoshin ƙafiya,
    A cikin mawaƙa babu mai ƙwatar ta.

    To don hakan ne ma na ce kar kui gara-
    Je don rubutun namu ya bambanta.

    Sukari a ƙwar ɗakinmu tamkar dala ce,
    Kowa ya zo ya sha shi babu fusata.

    Ringim garinmu, garinda kowa malami,
    Can nai tsugun nattashi tun yarinta.

    Waƙa ko zance ne wurina don kuwa,
    Na jaddada kuma na iya na huta.

    Maisugar Ringim✍️✍️
    09123098967
    ringimmaisugar@gmail.com
    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.