Ticker

    Loading......

Wakafi (,)

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

441. Shi waƙafi sifarsa tamkar na wata ne,

 Za ka ga ɗan ɗigo, ƙasan an yo zane,

 Kuma an lanƙwaso shi ya yo ciki done,

 In ka gan shi Hausa sun ce waƙafi ne,

  In aka yi shi nan ake numfasawa.

 

442. Za a tsaya kaɗan misalin sheɗawa,[1]

 Tamkar ka faɗa da niyyar ƙarawa,

 Sheɗa an ka so ga masu karantawa,

 Sai a kula a sa ta nan ga rubutawa,

Kar ya tsawaita gwargwadon hanzartawa.

443. Za a saka ta can ga jimla ga gaɓarta,

 An mata tanadin muhalli ka rubuta,

 In aka sa ta barkatai an lalata,

 Ba a saka ta ko’ina sai gurbinta,

  Don ma’ana ta samu damar zaunawa.

 

444. Tamkar za a lissafi ga bayaninka,

 Ko kuma za ka rarrabe ga rubutunka,

 Ko kuma in ka jera ‘yan kalmominka,

 Sai ka saka shi don a gane a karanta,

  Ga abu nan daki-daki ga rubutawa.

 

445. Za ka rubuta, “na gani, sai mun sadu,”

 Na ji batunku, to ku kawo muna shedu.

 Shin mulki ake biɗa, ko kuma gandu?

 In Sarki kake biɗa, to tafi Gwandu.[2]

  Na same shi, ya faɗa bai ƙarawa.

 

446. Na ga Abubakar, da Isa, da Nalado,

 Na ga Bala, da Buba, har malam Ado,

 Na tuna Sani, da Labbo, sai baban Indo,

 Na ga Alu, da ɗansa sun ɗauko kwando,

Da su Musa, da Manu, ya hana sheƙawa.

 

447. Sha ɗaya, sha bakwai, da sha shidda, ka lura,

 Tun farkon ƙidan ɗaya, lambar mara,

 Biyu, da huɗu, da shidda, su ba su da mara,

 Ga tara, ga takwas, haɗa malam tara,

Sha uku, sha takwas, misalin ƙirgawa.

 

448. Kowace kan gaɓar ƙida in ka kiyaye,

 An yi alama gabanta domin a kuranye,

 Kar ka sake ka zo wurin har ka tumaye,

 An so ka tsaya kaɗan ka nisa ba tauye,

  Waƙafi an ka sa ya zan mai nunawa.

 

449. Haka aka son ka dinga lura ka kiyaye,

 A rubutun ka sanya ƙa’ida to kai waye,

 Ƙin saka ƙa’ida a nan kai tawaye,

 Shi waƙafi a sa shi don kar a tumaye,

  Sa waƙafi daki-daki ba caɓawa.



[1] Kalmar “sheɗawa” daidai take da “numfasawa.”

[2] Gwandu ƙaramar hukuma ce da ke jahar Kebbi.

Post a Comment

0 Comments