Ticker

    Loading......

Wararrun Kalmomi

 Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

294. A rubutu na Hausa in za a rubuta,

 To a bi doka, a tabbata an inganta,

 Kalmominmu bi da bi sai a kwatanta,

 Wata kalma idan ka kalli bayaninta,

  Ba jam’i takai ba sai dai warewa.

 

295. Za ka ga ta shigo ga jam’u ta ware su,

 Ko sun kai kaza yawa za ta rabe su,

 Sai ku biyo mu za mu ba da bayaninsu,

 Ga rubutunsu inda duk za a raba su,

  Ɗan adadi kaɗanna shi taka warewa.

 

296. Ba ta game dukansu sai dai ta yi zaɓe,

 Wani shashe cikin rubutu a yi keɓe,

 Ba a haɗe shi, tabbata kar ka yi kwaɓe

 Wawware shi za a yi, can ya yi raɓe,

Wani ɗan ɓangaren abin taka nunawa.

 

297. Ga kalmar waɗansu duba ta a sosai,

 Ba a raba ba, ga shi ta kammala sosai,

 In kuma an ka sa waɗan su, to yassai,

 An yi kure, waɗansu ne gane sosai,

  Ga sauransu nan ka sa ta a ƙirgawa.

 

298. Ka ga nan rubuta sauran su kure ne,

Ga ta ukunsu nan irinsu kwatanci ne,

Ga rubutun irin su, to ka kauce ne,

Sai ka haɗe su ba rabe wa kowanne,

  Ba a raba su can ga dokar zanawa.

 

 

299. Ba tazara cikin gaɓoɓin ka kiyaye,

 Ba a rabe su ba a sa ‘su’ ta yi ɓoye,

 Saɓon ƙaida ya sa ma’ana tauye

 Don haka yanzu mai rubutu ka kiyaye,

Haka aka son ganin su can ga rubutawa.

 

300. Ɗalibbai suna ta fama da karatu,

Ya dace cikin karatu su shagaltu,

‘Yammata a daina wasa aje shantu,

Ga wasu na gani suna tafka rubutu,

  Amma ga waɗansu can na holewa.

 

301. Yaran zamani halinsu abin ƙi ne,

Su yi ɓarna ka hanƙure don tilas ne,

Su yi cuta suna ganin alheri ne,

Ka yi horo suna ganin zalunci ne,

Sai sauransu ‘yan kaɗan masu kulawa.

 

302. Ka ga irinsu sun fi dace wa irina,

 Mai halin ƙwarai ka dace da irina,

 Mai yin shaye-shaye shi ne ya yi ɓarna,

 Da irinai, irinka su ke muna rana,

  Na ga irinta mai irin naka na sawa.

 

303. Ban da irinmu wa ka wasa da irinka?

Shin ko za ka sa irinsu ga harkar ka?

Ka yi ƙwazo, irinmu na son aikin ka,

A garin nan irinku kowa ke shakka,

  Wa yaro a nan ubanai ka fitowa.

Post a Comment

0 Comments