Ticker

Wasu Muhimman Wuraren Hade Kalmomi

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

Gabatarwa

 

365.  To fa! Ko a yanzu babbar magana ce,

 Ka da ka saki taho mu je ƙarshen zance,

 Ilimin ka haɗe ga ƙa’idojin ka gwanance,

Bi ni da hankali da kyau kar ka ɗimauce,

  Ka ji ƙari ga mai rubutu na haɗewa.

 

366.  Masana sun ka ce rubutu nasararsa,

 Ta dogara ne ga wanda shi ke tsara sa,

 Wanda ka rattaba shi, tare da dokarsa,

 Shi masani a kodayaushe hikimarsa,

  Gane abin da mai rubutu ke cewa.

 

367. Suka ce day yawa akan kai ga wurare,

 Wanda suke da tarnaƙi, sai da kwarare,

 In an ɓata da wag ga doka ta burare,

 Sai ma’ana ta jagule, sai ta zurare

Da tunanin mutum yake son rikicewa.

 

368. Ga abu daf faɗi awar dai a raba su,

 To kuma babu shawara dole haɗa su,

 Doka ce ta ba da damar a game su,

 Ba a raba su ko faɗin ya nuna su,

  In kuma an raba abin sai kwaɓewa.

 

369. Ga tsarinsu nan idan za a kiyaye,

 Ga shi ƙwata-ƙwato a fili bai ɓoye,

 A bi doka a zo a zauna kai waye,

 Ga rubutu a sanya ƙaida kar a kuranye,

  Za a fahimci kowane ba ruɗaswa.

 

370. Mun ware su ne daban don gane su,

 Ba makawa ga ɗalibai sai su tsare su,

 Su bi doka, su kyautata ga ribar su,

 Sa natsuwa ka gane duk mun ware su,

Don tawagarsu ce muhimmi ga kulawa.

Post a Comment

0 Comments