Wulakanci Da Rainin Da Marubuta Ke Fuskanta A Kano: Laifin Su Waye?

    Marubuta na daga cikin mutane masu hankali, kaifin basira da zurfin tunanin da suka fi kowa muhinmmanci a cikin al'uma amma a yanzu su aka fi kowa rainawa a fagen gudanar da al'amuran jama'a a nan Kano da ma wasu jihohin a Arewacin Najeriya.

    Kama daga daidaikun mutane, ƙungiyoyi, ma'aikatu, masana'antu, makarantu kai har ma da uwa uba a gwamnati. Da yawa za ka ga ba su dauki marubuta komai ba. Ko mene ne dalilin da ya sa haka? Dalilin da yawa ba a shakka ko gani girman marubuta?

    Ko don mutane yanzu sun daina sha'awar neman ilimi ne ga shi da yawa ba a son karatu kuma ba a amfani da ilimi wajen aiwatar da lamurarmu. Yanzu komai da ka ake yi ba a amfani da masana, kwararru da gogaggu wajen yin ayyukanmu a al'ummance.

    Abinda da yawa ba mu gane ba shi ne marubuta ba y'an kasuwa ba ne ba manoma ba ne ba y'an siyasa ba ne da dai sauransu duk da shike suna gudanar da waÉ—annan sana'o'i da ma wasunsu. Marubuta sune masu yasa a rijiyar da ake shayar da al'uma ruwa don a rayu.

    Sannan rubutu ba abin wasa ba ne ba siyasa ba ce kuma ba tijara ba ce shi ya sa da dama za ka ga marubuta kowa na ƙoƙarin kare martabarsa yake kama kansa kuma ba ya son a ce da shi wani ɗan jagaliya ko ɗan sharholiya tun da yana ɗaya daga cikin masu nazari da hangowa jama'arsa abin da gobe ke tafe da shi.

    Sannan marubuci na jama'a ne baki ɗaya don abin da ya kan rubuta ba don alfanun wani mutum ɗaya kawai ya ke yi ba a'a kuma ba na wani ɗan lokaci ba ne a'a sannan rubutunsa ba ta wata ƙungiya ba ne. Ga shi sau da dama abin da akan rubuta abin da ya shafi kowa da kowa ne ba tare da nuna wani 6angaranci ba.

    Marubuta kan yi rubutunsu ne don shaidawa da shaidar da dukkan abin da ya faru. Hakazalika su kan yi rubuce-rubuce don ajiye abubuwan da suka faru a kundin tarihi su sanar da na gaba me ya faru, yaushe ya faru, a ina ya faru, da wa da wa hakan ta faru akansu sannan akan wane dalili abin ya faru.

    Marubuta suna daga cikin masu ruwa da tsaki a fagen inganta, É—aukaka da kuma gabatar da tarihi, dabi'u da al'adu na kowacce al'uma ta yadda ya fi dacewa duniya ta kalle su ta san su ta kuma fahimce su da shi. Balle yanzu da aka samu ci gaba aka samu yanar gizo (intanet). Kun ga babu wanda ya isa ya hana a ji ku ke nan.

    Wannan nauyin kuwa na dindindin ne ba na wucin gadi ba. Babu al'umar da za ta samu ci gaba ta ko wane fannin rayuwa muddan ta yi wasarairai ko ma ta yi watsi da masu makaman yaƙinta mariƙa abinda ya fi takubba kaifi wato sojojin artabunta da kowa a duniya a zahiri da baɗini wato marubutanta.

    Ya kamata dukkan marubutanmu na wannan shiyyar ba kawai na Jihar Kano ko daidaikun jihohin Arewa ba su farga akan wannan muhinmmanci na su. Su kuma tashi daga barci su daina sumisumi suna bin bango kamar wasu kadangaru. Su san ko su su waye a cikin masu seta al'umarsu don samar da ci gaba mai É—orewa.

    Duk wanda ya manta ko shi wane ne a cikinmu bari mu tuna masa cewa shi fa jigo ne turkey ne babba a wajen kare haƙƙin al'umarsa tunda shi ko ita Allaah SWT Ya bawa baiwar faɗa a ji. Shi aka bawa muryar da za tai amo duniya ta ji. Shi Allaah AWJ Ya bawa alkalamin da Ya yi rantsuwa da shi. Amma kuma ace marubuta ba a dauke ku a ga6ar komai ba.

    Wallaahi laifi ba na kowa ba ne laifinku ne. Kun zama tamkar kashi babu wanda yake son ya yi wata mu'amala da ku sai mai kwashe ku ya zubar. Shi ma ko ita ma suna yi suna kyamar yin hakan. Abin takaici kuma shi ne kun yarda da hakan daidai ne alhali kamata ya yi ku zama tsumangiyar kan hanya.

    Gaskiya mun zama ne kamar kazar da take kwance ne akan dami. Na faɗa a wani shirin da muka gabatar na Alƙalami Harshen Zuciya kwanaki a Freedom Radio cewa marubuta duk yadda suke son su kawo sauyi ba kawai a al'umarsu ba kai har a duniya baki ɗaya dole ne su zama masu haihuwar amo sannan su ci gaba da amsa amon nan har sai kowa ya ji ko da kuwa ba a so.

    Duk inda wani abu ya ta6a martaba da kima da mutunci da haƙƙi da duk wani abinda ya shafe mu a al'ummance ya dame mu ko ya ta6a addininmu, al'adarmu, harshenmu, jiharmu, shiyarmu, ƙasarmu, nahiyarmu da dai sauransu to ya zama wajibi mu magantu mu koka mu yi terere mu yi ƙorafin mu yi rubutu mu yi odiyo mu yi bidiyo mu ce wALLAAHI BA MU YARDA BA!

    Sannan da zarar wani marubucin ya yi wannan rubutu to kada kowa ya yi ƙasa a gwuiwa indai marubuci ne ɗan halal to lalle ilalla ya tabbatar ya tofa albarcin bakinsa da kakkausar murya in har ta kama.

    Marubuta wAllaahi cin kashin da ake mana ya isa. Kuma ba komai ba ne yake jawo mana wannan rainin matsayi da girma ba illa kwaÉ—ayi. KwaÉ—ayin abin duniya da neman yin fice a daidaikunmu.

    Duk wani wanda ya samu mukami sai ya dinga ganin sauran marubuta ba komai ba ne kuma duk wani marubuci ko marubuciya ba kowa ba ce. Su kuma sauran marubuta saboda gudun kar a ce suna kyashi da baƙin cikin ko suna kushe da hassada wani ya samu a cikinsu sai ya rufe kurtun tawadarsa su tsane alƙalumansu su ajiye.

    Shi ya sa waɗanda ba marubuta ba da zarar sun ga bangon gidan marubuta ya tsage sai su kutsa kai su ƙarasa abinda kuka fara wato ɗaukar ku a daidaikunku da ma a Ƙungiyance fanko ba nauyi. Ga shi nan abin ya dame ku amma rashin haɗin kai da sanin martabar kanku da junanku yana nema ya kaiku ya baro.

    To ku sani in ba ku ba babu wanda zai iya gyara muku. In kun shirya gyarawa to don yanzu dai ya kamata ace kunne ya ji ko jiki zai tsira wannan kuma sanin gaibu ne sai Allaah.

    Ni dai kun ji abin da ke kai kawo a zuciyata.

    From the Archive of:

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +2348067062960

    ©2023 Tijjani M. M.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.