Wuraren Amfani da Karamin Baki

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    599. Shi ƙaramin baƙi daɗai bai rikitarwa,

     Domin kodayaushe shi ne aka sawa,

     Da yawa mai kurenmu shi yaka zanawa,

     Ba ya rikitar da mai rubutun Hausawa,

      In aka zo ga ƙa’ida gun zanawa.

     

    600. Duk a wurin da ba baƙi babba ake ba,

     Ko ka sa shi ka ga ba zai riba ba,

     Don ba ka so sa shi inda yad dace ba,

     Ba shi zuwa wurin da nashi ba ne ba,

      Ƙaramin za a sa wurin don dacewa.

     

    601. Kowane aikatau baƙi ƙarami zai zo,

     Matuƙar dai cikin rubutu ne yaz zo,

     Amma in ya zo a farko zo-zo-zo,

     Za a rubuta babba, don farko yaz zo,

      Yanka yanke-yanke ko yayyankewa.

     

    602. Can ga sifa da ‘yan ƙanana ake zane,

     Su ma dai kamar hukunci aiki ne,

     Ƙarami za a sa shi babba yana zaune,

     Can bagirensa ko a farko yin zane,

      Dogo ko baƙi, fari mai haskawa.

     

    603. Haka doka ta ce wakilan sunaye,

     Sai a rubuta ‘yan ƙanana kai waye,

     Kar a sake sanya manya dogaye,

     Na baƙi ko wasal a kowane halaye,

      Duk harufa ƙanana za a rubutawa.

     

    604. Tamkar ya buwaya, ta shiga ɗakinta,

     Ko kuma ni ka ba shi, shi ke aurenta,

     Sannan wa zai biya sadakin kanwata?

     An ce ku zo batun neman mata,

      To sun gayyace ku kun kasa fitowa.

     

    605. Matuƙar ya fito ga sunan mabuwayi,

     Za a saka shi babba, don samun sauyi,

     Ba a rubuta ƙanƙanin harafi, bai yi,

     Tsari ne na ƙa’idar rubutu a yi koyi,

    Babba ake saka shi don wanwancewa.

    606. Bayan neni ko’ina ɗan yaro ne,

     Sa ƙaramin baƙi, wakilin ko wa ne,

     Ba a saka shi babba, mun san laifi ne,

     Ƙarami ko da yaushe in dai harafi ne,

      Bai rigima da babba can gun zanawa.

     

    607. In waƙafi ya zo a bayansa a sa shi,

     Ai nazarin iri na kalmar kan sa shi,

     Domin babba na da gurbinsa na sa shi

     In dai ba wurin haraf babba ba sa shi,

      Ko da mai ruwa a nan babu rabewa.

     

    608. Haka bayan baka alamar buɗewa,

     Sa ƙarami ka bar batun duk ruɗewa,

     Sai ka bi yadda ƙa’ida ke tsarawa,

     Har ma can a dab da ƙarshen zanawa,

      Da rufewa ƙanana duk za a sakawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.