Ticker

Ya Gano Matarsa ba ta Kama Kanta ba Kafin Ya Aure ta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum dafatan katashi lfy, Allah yakara basira. Don Allah ina so a amsa mini wannan tambayan ko abamu shawara, ina da abokina/amini na mun tashi tare mun yi karatu tun daga matakin primary har zuwa jami'a tare muka gama, mun zama kamar yan'uwa. Abokina yayi aure wata huɗu da suka wuce kuma daga baya yake samun labarin matar tashi ba ta kama kantaba kafin ya aureta, Harma ya haɗu da wassu daga cikin wadda suka sadu da ita kafin ya aureta, kasancewa ba a gari ɗaya suke ba a makaranta suka haɗu, kuma yayi iya binciken halinta kafin ya aureta amma bai gano rashin kamun kantaba. Kuma a halin yanzu ya ce ta fita a ransa tun da yaji labarin abubuwan da tayi a baya, A matsayina na amininsa nace kar yayi hukuncin da babu shi a sharia da sunnah ya bari mutura tambaya a malamanmu na sunnah domin samun cikekkan amsa da shawarwari . Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam

Mutukar ta tuba, kuma ingantaccen tuba ne, zai iya cigaba da zama da ita, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taɓa aikatawa ne ba.

Saidai in har ya daina sonta kwata-kwata, to rabuwa ita ce mafita, saboda duk matar da ba ka so, to ba ka iya tsayawa da hakkokinta ba.

Rayuwar aure tana ginuwa ne akan soyayya da sha'awa, idan ɗaya ya samu tangarda, aure ba zai tafi a saiti ba.

Allah ya shar'anta saki ne saboda tunkuɗe cuta daga ma'aurata ko kuma ɗaya daga cikinsu.

Ina baka shawara da ka kara bincike da nazari saboda Makiya da Mahassada da Magauta suna iya ɓata mutum da tsagwaron Kage.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments