Yadda Ake Yanke Farce Asunnah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Yaya ake yanke farce asunnah, shin mutum zai fara da ɗan yatsarsa na dama ne ko hagu?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Yanke farce sunnah ne daka cikin Sunnonin fidira kamar yanda hadisai ingantattu suka nunar, Anaso farawa dayanke farcen dama saboda hadisin da yatabbata daka A'isha Allah yakara mata yarda ta ce: Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance damaitawa tana burgeshi cikin dukkan Al'amuransa wajan ( sanya takalmansa datafiyarsa da dukkan al'amuransa) Bukhari (163).

    Nawawi acikin al-majmu'u (1/339) ya ce: Malamai sun yi ijma'i akan yanke farce sunnah  ne, akan maza da mata na hannuwa dana kafafuwa,  Mustahabbine mutum yafara yanke na hannun dama sannan na hagu, sannan nakafar dama sannan ta hagu.

    acikin sharhin muslim (3/149) yasake cewa: Anso mutum yafara da hannun dama, yafara da karamin ɗan yatsarsa sannan mai bi masa har nakarshe.

    Sannan sai ya koma kafarsa ta dama yafara da karamin ɗan yatsarsa, Sannan Sai kafarsa ta hagu ita kuma zaifara da babban ɗan yatsarsa yakare dakaramin ɗan yatsansa.

    Hanabila sukuma sun ambaci wani tsarin nadaban wajan ɗan yatsan daza'a fara yankewa dawanda za'a kare da shi yayin yanke farce, sai dai cewa bai tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ba.

    Al'iraƙi rahimahullah acikin Darhul tasreeb ( 2/77) ya ce: Babu wani hadisi daya tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam wajan yanda za'a yanke farce daza'ai aiki da shi.

    Ibnu hajar rahimahullahu acikin fat-hul bari ( 10/345) ya ce: Babu  Wani hadisi daya tabbata daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam wajan tsarin yanda za'a yanke farcen wani ɗan yatsan akan wani, Sannan ya ce ibnu daƙeƙil Eiid ya yi inkarin yanda ake yanke farce wanda imamu gazali ya ambata da waɗanda suke tare da shi, dukkansu basu da asali, farar da mustahabbanci bashi da dalili, abune munnuna awajena asanina, koda mai riyawa zai riya cewa farawa da yatsar dama saboda darajarta, sauran kuma ba zai riya musu hakan ba.

    Hakane farawa da hannun dama da yatsar dama yanada asali, saboda damaitawa tana burge Annabi Sallallahu Alaihi wasallam.

    Saboda haka dai maganar imamu nawawi rahimahullahu tana da asali wajan yanda za'a yanke farce domin yagina fatawarsa akan hadisi ingantacce wanda damaitawa yana daka cikin Sunnah.

    Saboda haka yankan farce za ka fara da hannun dama da karamin ɗan yatsa, sannan hagu da babban ɗan yatsa ka kare da karamin ɗan yatsarka, hakama kafafuwa.

    WALLAHU A'ALAMU.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.