'Yar Damisa - Gabatarwa

    'Yar Damisa - Gabatarwa

    Assalam alaikum. Gaisuwa gare mu marubuta da makaranta da duk wasu ma'abota harkar adabi.

    Na san da yawa an sanni da rubutu na zube da waƙe har da zaurancen Haiku cikin harsunan Hausa da Turanci. Sai dai ba a sanni da rubutu na wasan kwaikwayo (dirama ko film script) ba.

    Abin dake faruwa ko in ce abin da ya faru shi ne tun farko ni a gaskiya ban so harkar fim ba duk da shi ke na ta6a zuwa na yi gwajin a sa ni cikin wata dirama da fitaccen marigayin furodusan nan Tijjani Ahmad na CTV ya gaiyace in zo a yi da ni a tashar wajen 1990 ne ina jin.

    A gaskiya gwajin da na yi wato auditioning ya kar6u inda nan take aka kaure da tafi bacin na gama nuna irin kwaikwayon wanda zan zama a diramar wato wani ne mahaifinsa ya rasu ya bar masa ƙanne maza da mata wanda hakan ta sa dole ya daina karatun boko ya koma dawainiyar gidansu.

    Sai dai a gaskiya ban sake komawa cikin 'yan diramar (cast) ba. Don kamar yadda na ce da farko ne fim ba ya daga cikin abubuwan da na so in dinga yi a midiya. Shi ne kawai na koma harkata ta gidan radio.

    Dalilin da ya sa nake kawo muku wannan zance da kuma tarihi shi ne akwai dirama sikirif da na ta6a rubutawa wajen 1990 koma kafin nan da na tsinto a cikin rumbun ajiyata da zan so wasu ƙwararru a harkar fim irin su Ado Ahmad Gidan Dabino, Anas Bala Babinlata, Fauziyya D. Sulaiman da dai ire-irensu su karanta mu ji me za su ce akai.

    Kamar yadda ku ka gani a sama taken wasan kwaikwayon shi ne 'YAR DAMISA kuma na ƙudiri niyyar in kawo rubutun nan don na tabbata ba za a rasa waɗanda za su so su karanta shi ba. Sannan za a d'auki darussa daga cikin labarin. Ban da nunawa y'an baya yadda rayuwa take a da wajen shekaru 30 baya.

    Sai ku kasance tare da bangona na Facebook, WhatsApp, Instagram don bibiyar wannan labari ta sigar salon rubutu na dirama da da yawa ba kasafai za ka ga marubutw na amfani da shi ba wajen ilimantarwa, faÉ—akarwa, wa'azantarwa, nishad'antarwa da dai sauransu.

    Sai kuma don Allaah a kiyayi haƙƙin mallaka don ba zan lamunci satar fasaha ba. Ku biyo ni mu je - Shafi Na Farko

    From the Archive of:

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +2348067062960

    ©2023 Tijjani M. M.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.