Yaro Bari Murna Karenka Ya Kama Zaki - Ankararwa Ga Angwayen Auren Gata

    Yaro Bari Murna Karenka Ya Kama Zaki - Ankararwa Ga Angwayen Auren Gata

    Kowa ya san samari da ‘yammata na son aure amma rashin kuɗi ne yake hana su. Ko Allaah SWT da Manzo SAWS sun yi zancen rashin kuɗi illa ne ga masu niyyar yin aure.

    To maimakon matasa mazan su fahimci wannan nusarwa su duƙufa wajen neman kuɗi su kuma ‘yammata su rage burinsu sai ka ga abin sau da yawa ya nemi ya gagari kundila.

    Ba ƙin taimakawa matasa su shawo kan sha'awarsu ba ne matsalar ba, a'a. Abin gudu a nan shi ne duk wanda aka yi masa auren gata amma ba shi da sana'a ko aikin yi to ba lallai ya iya rike matarsa ba.

    Kowa kuma ya san mata in har an auro su abin da zai biyo baya shi ne cefane, ba ni ba ni da dai auransu. Daga bisani sai haihuwa sai kuma ɗawainiya kalakala. Zancen gaskiya ke nan.

    In ka duba da kyau cikin natsuwa da tsanaki ba son zuciya ba ƙarya ba yaudarar kai sarrafa gida da biyawa mace buƙatunta na yau da kullum to samun kuɗin shiga na da babban muhimmanci.

    Don wAllaahi ba da haƙuri so da ƙauna da kuma hurewa mace kunne ba ya isa a fagen kula da hidimtawa iyali. Ko babu rashin lafiya da yin sutura da ilimantaewa wAllaah sai an samu wanda yake da zuciyar nema.

    In ba jajirtaccen namiji ba waye zai kasa yiwa kansa aure a yi masa na gata kuma ya iya riƙe matar da ‘ya’yan da za su biyo baya? A gaskiya sai an taki sa'a kuma sai anyi da gaske. Wannan ne fargaban dake akwai.

    Mu dai yanzu tunda Ubangiji Allaah SWT Ya tabbatar da auren nan na gata ga ‘yammata da zawarawa to ba mu da ta cewa sai dai mu yi musu fatan alkhairi da samun zuriyya ɗayyiba amin thumma amin 🤲🏾.

    From the Archive of:

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +2348067062960

    ©2023 Tijjani M. M.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.