Ticker

Zan Iya Sauraron Wakar Bege Ko Ta Soyayya

TAMBAYA (96)

Assalam alaykum wa rahmatullah wa barakatuhu mlm da ftn an tachi lafiya tambayar ita ce chin ya halalta sawraren wakar soyayya ko ta fadar bège

AMSA

Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuh

Alhamdulillah. Yar uwa amsarki tana cikin wasiqar da na rubutawa mawaqa

WASIQA ZUWA GA MAWAQA

@Usmannoor_As-salafy

Salamu alaikum. Warahmatullahi. Wabarakatuhum.

Nasha amsar saqonnin tambayoyi akan hukuncin sana'ar waqe-waqe da kide-kide a addini. Zanso kowanne mai sauraron kade-kade ya nutsu ya karanta wannan saqon a matsayin amsar tambayoyinsu

Akwai wasiqar da na taba rubutawa wani mawaqi (wanda bazan kama sunansaba) saidai zan iya bayyana saqon da ta kunsa maybe hakan yazamo silar shiriyar dubban mawaqa masu saka kida a cikin waqarsu, fatana duk mai jin kade-kade ya tuba ya daina silar karanta wannan saqon. Ga wasiqar kamar haka;

Innal hamda lillah, nahmadahu wanastainuhu, wanastaghfirhu, wanauzu billahi min shururi anfusuna, wamin sayyi ati aamalina, man yahdiyallahu fala mudillana, waman yahdil fala hadiyala, wa ash hadu anla ilaha illallah, wahdahu la sharikala, wa ash hadu anna muhammadan abduhu warasulahu, amma baad

Fainna asdakal hadis kitabullah, wa khairi hadi, hadi Muhammad SAW, washarril umuri muhdisatiha, wakullu muhdasatin bidia, wakullu muhdasatin dalala, wakullu dalalatan finnar, aazanallahu minannar. Amma ba'adu

️Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhum

Na rubuto wannan wasiqa ne domin tabbatarda cewar alaqar dake tsakanina dakai babu karya a ciki domin kuwa duk mai son ka shine zai fada maka abinda zai fissheka fiddunya wal akhira

Ka kasance mutum mai magoya baya sama da (...) a instagram page, shawarar da zan bada anan shine, shin mezai hana ka daina saka kida a waqoqinka domin kuwa hakanne yake sa yan mata da zawarawa da matan aure suke tiqar rawa a tik-tok kai kuma kana daukar video dinnasu kana posting, wanda maybe nangaba yayansu ne zasu ga videos din kuma tabbas sai sun tsinewa mawaqin da ya zama silar rawar tasu, anan shaidan yayi nasara kam

Burina shine (...) ya ji sautin waqar matan Hurul Ayn a Aljannah (Alfirdous in particular) to ammanfa hakan bazata yiwuba sai an koma hadisin ma'aiki SAW wanda ya gargadi al'ummarsa akan sharrin sauraren kade-kade

Idan har ka goge videos din wanda Shi Allah SWT mai gafarane, zai iya gafartawa bawansa idan yaso matuqar bai mutu yana shirka ba. Zaiyi wuya ka daina saka kida a waqenka ni shaidane kaima kasani domin kuwa ka saba amman idan baka mantaba akwai manyan mawaqan da duniya ta sansu kuma sun maye gurbin sana'arsu ta industry da neman ilimin addini ka'in da na'in dakuma yada ilimin ga masu sauraro da ganinsu, kamar irinsu Shaykh Bilal Philips wanda kafin ya musulunta dacan ya kasance makadin guitar ne a kasar amurka, ga abin koyi Shaykh Yusuf Estes wanda ya musuluntarda dubunnan Christians wanda dacan mawaqine a Catholic Church a kasar amurka, celebrities kamar irinsu: Peggy Melati Sukma, Teuku , Kartika Putri

Hakama mawaqiyar Irish Sinead O'Connor wadda ta musulunta a shekarar 2018 ta maida sunanta Shuhada Sadaqat, wadda ta rasu a shekararnan da muke ciki, 2023 (Allah ya jikanta tareda sauran musulmai baki daya)

Kamar irinsu mawaqi Noor Al-Kautsar, Ucay wanda suka bar sana'ar a 2013 suka koma yada da'awar musulunci. Irinsu Derry Sulaiman tsohon makadin jita, a yanzun dukkansu suna amfanida sana'arsu wajen janyo hankalin mutane su san addinin musulunci

Idan kuma ka koya musu ko da Hadisi daya ne to tabbas zaka samu ladansu idan suka aikata aikin da yake a cikin Hadisin, daukakarka anan duniya ga kuma lada mai tarin yawa a lahira. Bazaka iya dainawa a lokaci daya ba saboda nisa a cikin harkar amman a hankali a hankali zaka ga komai ya sauya idan ka kyautata niyyarka hade da neman addu'ar iyaye, to ammanfa akwai qalubale mai tarin yawa idan ka guji masu ra'ayi sabanin naka wato yan Kannywood. To amman ai Allah zaiji dadin haka hakama malamai masu jan hankali akan illolin kide kiden dakuma rawar tik-tok din

Zanso ace wannan shawarar kayi amfani da ita la'akarida gaskiyace nake fada ko da kuwan hakan bazai maka dadiba saboda duk mai son ka don Allah to kamata yayi ya fada maka abinda zai amfaneka fiddunya wal akhira. Kuma na tabbatar da idan kayi hakan to daukakar da Allah yabaka saidai tayi sama ba kasa ba, domin kuwa duk wanda ma baya son ka to silar haka saikaga Allah ya saka masa son ka. Da zaka dau wannan shawarar kuwa da kaine zaka fara karya record din haka a tarihin mawaqan hausa baki daya, daukaka bisa daukaka fiddunya wal akhira. Domin kuwa nidai ban taba jin labarin wani mawaqi da yabar waqa domin Allah ba saidai zamani ya shudar da shahararsa. Burin shatan waqa (Allah yajikan rai) shine kada yayansa su fada harkan waqa, haka sukaita takun saqa da dansa wanda yayi qoqarin shiga harkan, a karshedai Allah ya qaddara ba wanda zai gajeshi a cikin yayansa

A iya dan bicikena na bincika, a gaba dayan malaman Ahlus Sunnah babu wanda yake goyon bayan sana'ar kide kide, saidai ma suna hani ne akan hakan la'akarida illolin da hakan ya haifar ga al'umma kuma zai haifar ga yayan musulmai masu tasowa

Yanzu dai kaduba kaga wancan quote din wanda na gani a kofar studio din daya daga cikin yaranka, an rubuta "Only in the listening of the music does heart find peace" ma'ana "Da sauraron kidane zuciya take samun nutsuwa" wanda hakan yaci karo da ayata 28 cikin Suratu Ra'ad wadda Allah yace: "Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa," to kaga wannan idan ya rubutane a rashin sani to yakamata ka nusar dashi illar hakan

(...), kai kanka kasandai da yawan ambaton Allah zuciya take samun nutsuwa to amman meyasa a cikin studio din yasaka "Da yawan sauraron kida da waqa zuciya take samun nutsuwa"?

To wannan dalilin ne yasa naje dakaina domin bashi shawarar ya cire wannan "quote" din, lokacin da naje wajen 10 na dare, ban tarardashi ba amman hancina shine yayimin maraba da warin wiwi da wani yaron yaronnaka yake nannadawa (Kuma a goman karshen watan ramadana), nace masa ina wane-wane yace ya tashi saidai wane shima yaje wani waje uzuri yana tafe, na jira a waje inata tuno wani hadisin da Ma'aiki SAW

Sahihin Hadisin yana cikin Ibn Majah yace: "A karshen zamani (kafin alqiyama ta tsaya) al'ummata zasu dinga shan giya su kirata da wani sunan, zasu dinga saka kayan kide-kide a kunnuwansu, Allah zai sanya kasa ta hadiyesu sannan ya maidasu birrai da aladu"

A lokacin sai na tuno da cewar qwaqwalwar mutum ta rabu kaso hudu (Temporal lobe, parietal lobe, occipital lobe dakuma fore lobe) shikuma fore lobe dincan shine inda ake tattara ayyukan zunubban mutum sabanin occipital lobe wajenda ake adana danasani wanda hausawa ma kance danasani qeyace, shiyasa ma Allah ya gargadi Abu Jahal a cikin Suratul Alaq ayata 15 da ta 16, sakamakon karyar da yake yiwa addinin musulunci

"A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba (yin qarya), lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa (qwaqwalwa)"

"Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi"

Nan take kuma na tuno da binciken da masana qwaqwalwa sukai na cewar bangaren lymphatic system a fore lobe dake qwaqwalwa shine yake adana son shaye-shaye kamarsu giya, cocaine, wiwi, ananne kuma ake adana zunubban zinace-zinace dakuma sautin kide-kide dalilin dayasa ake rawa, silar zubewar mutuncin kamilallen dan Adam

Sai nace a raina "Sadaqa rasulullah SAW", tabbas ma'aiki SAW yayi gaskiya. Harkar mata tayi yawa a industry, shaye-shaye abin burgewa ne a harkar sannan kuma jin kade-kade shine ummul-aba'isin dake janyo faruwar ragowar laifuffuka

Idan kayi sanarwar cewar ka daina saka kida a waqenka to tabbas wasu daga cikin yaranka zasu daina kaga kenan tun anan ka fara samun lada da kuma qima a idon duniyar musulmi. Shin ka tuna abinda (...) daya daga cikin fans dinka ya fada maka wani lokaci da yazo sabon studio dinka yana sanye da (...) irinnaka da shiga irin taka yace "Gaskiya (...) da ace yanda muke sauraren waqoqinka haka muke sauraron karatu da tuni munyi sauka". To kaga wannan fan din naka yanzun a shirye yake ya fara koyon Hadisan Manzon Allah SAW daga wajenka, kuma ko kasan cewar zata iya yiwuwa nine na canza masa ra'ayi akan son kide-kide harma ya fada maka hakan?

Allah SWT yace a cikin Suratu Luqman ayata 6: "Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa."

Waqar da kake danasanin fitarta itace "(...)", kamar yanda ka fada lokinda akai interview dakai wadda har yanzu nasan kana danasanin fitarta duniya kuma kullum za'ayita saurarenta har komawarka ga Allah, ko kasan maybe idan ka daina saka kida din a waqoqinka Allah zai kankare maka zunubbanka?

Ko kasan shahararriyar jarumar Bollywood, Sana Khan (wadda sukai film din Jai Ho da Salman Khan, haka kuma sunyi film da Shahru Khan) ta fito duniya tace daga yau na daina film, an tambayeta dalili tace mafarki nayi ana ganamin azaba kala-kala a kabarina sakamakon harkar film da kide-kide da raye-raye da nakeyi. Naga interview dinta a Indian News, tana kuka tana bayani. Harma Shaikh Dr. Zakir Naik yace yayi matuqar farin ciki da Sana Khan ta tuba ta gano kuskurenta. Wanda Mufti Menk ma yayi reacting akan lamarin tareda nuna farin cikinsa. To kaga anan Allah ne yakesonta da alkhaeri da harma aka nuna mata makomarta idan bata tuba ba, a yanzu haka ta auri shahararren mai kudinnan Mufti Anas, wanda sukaje aikin Hajji tare, alhalin da Umrah take zuwa tana dawowa ta cire hijabinta ta ci gaba da film amman yanzu da ta tuba sai gashi har aikin Hajji tayi. Ka duba tarihinta idan ka samu lokaci

Abul-sahba yace: na tambayi Ibn Mas'ud ma'anar waccan ayar ta 6 dake Suratul Luqman saiyace: Lahwal hadis na nufin waka wato al-ghina (Ibn Jarir 21/62 dakuma Hakim 2/411 da isnadi sahihi)

Ibn Abbas RTA ma ya fassara al-ghina a matsayin waka da makamantansu

Sa'ad Ibn Yasar ya tambayi Ikhramah ma'anar lahwal-hadis yace waka ake nufi, Al-hussain, Sa'id Ibn Jubayr, Qatadah da Ibrahim al-Nakh'i duk sun tabbatarda lahwal-hadis na nufin waka

Abdullahi Ibn Umar RTA yaji sautin sarewar makiyaya, sai ya saka yan yatsunsa a cikin dukkan kunnuwansa, ya karkatar da abinda yake hawa ya kauce daga kan hanyar. Yace: Ya Nafi', anajin sautin har yanzu? Yace: Na'am. Yacigabada tafiya yana tambaya har saida Nafi' yace yanzu ba'ajin sautin, sannan sai Ibn Umar ya sauke hannayensa ya dawo kan hanya. Sannan yace: Naga Annabi SAW yayi hakan a lokacinda yaji ana busa sarewa (Abu Dawud 4925 dakuma Bayhaqi 10/222 da isnadin mai kyau)

An rawaito daga Abdurrahman Ibn Auf RTA cewar: Manzon Allah SAW yace: "An haneni da sauraron saututtuka biyu, sautin sarewa a lokacin farin ciki da kuma sautin kuka yayin afkuwar wani iftila'i" (Tirmidhi 1005 da kuma Tayalisi 1783 da isnadi ingantacce)

Malamai sukace indai har haka magabata suke taka tsantsan da idan sukaji sautin kida to ya zasuyi kenan idan suka tsinci kansu a wannan zamanin namu?

A qarshe ina son ka qara duba wannan wasiqa sannan ka tambayi shawarar mutane nagari a cikin makusantanka, sai kayi amfani da abinda suka ce. Kafinnan kuma zanso ka karanta tafsiran ayoyin da sukai magana akan "Lahwal hadis" da "Al-lagwu", sannan ka duba littafin Ibn Al-Qayyim mai suna "The Evils of Music: Devil's Voice and Instrument" da kuma wani littafi mai suna "Music Made Me Do It" wallafar Dr. Gohar Mustaq da kuma littafin "Talbis iblis" wallafar Ibn al-Qayyim

Wannan wasiqar na rubuta ta ne da kyakkyawar niyyar kawo gyara a rayuwarka kuma ba ina nufin na fika tsoron Allah bane, maybe ma ka fini kusanci da Allah ta wani bangaren, wallahu aalam, kawaidai nayi amfanida abinda yake na zahiri ne don kawarda bidi'a a matsayin dan uwanka musulmi. Musamman la'akari da yanda yayanka suke tasowa da ilimin addini, kuma gashi (...) tana miming waqarka ana dorawa a media platforms, kuma sauraren waqa baya haduwa da karatun Qur'ani kamar yanda Ibn Al-Qayyim da magabata suka fada, gwara ayiwa tufkar hanci tunda ice tun yana danye akan iya tankwarashi. Allah ya yafe maka, nima ka tayani da addu'a Allah ya yafemin zunubbaina. Zanso ka sauka daga layinnan mara bullewa, ka maida hankali wajen business dinka. Roqona Allah yasa da ni dakai da sauran musulmai mu saurari waqe da kidan Hurul Ayn a Aljannatil Firdous

Wabi hazal qadri kifaya. Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

SHARHI: Kamar yanda na fada da farko ba saina kama sunan shahararren mawaqin ba to amman musabbabin da yasa na fitarda bayanan yanada alaqa da zamanin da muke ciki wato zamanin social media wanda Allah ne kadai yasan adadin mutanen da zasu karanta wannan wasiqa inmadai mawaqan ko kuma masu sauraren kade-kaden, burina hakan yazama silar kawo sauyi ga rayuwar wadanda shaidan ya qawata musu sauraren kida. Mutum ya karya rodi da haqoransa shine yafi sauqi akan son zuciyarsa. Ya Allah ka rabamu da son zuciya. Amsar tambayarki shine: Tabbas kida yana kawo munafunci a mu'amalance, kuma yana kawo cututtukan qwaqwalwa a kimiyyance sannan yana kawo raguwar imani a addinance, maganin hakan shine sauraron karatun al-Qur'ani mai girma. Allah ya bamu ikon gyarawa

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments