Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
488. Zarce masu yin sa su ne gogaggu,
Kuma su sun wuce a
ce masu jemagu,
Ilimi ag garesu sosai
sun gogu,
Sun zama malamai,
ga ilmi sun tsawgu,
Masana mazhabar
rubutun Hausawa.
489. Ba a saka shi sai wurin adana zance,
Sai a saka shi,
don alamar mu ta zarce,
Sannan ma akwai shi
har ma a magance,
Amma dai a nan da
aikinsa rubuce,
Daidai gun gaɓa a bar ka da idawa.
490. Sarki goma... sai a bar ka a ƙyale nan,
In ka karanta
tambaya biɗo amsar nan,
Kuma sai wadda za
ta dace da wurin nan,
A zato na da Hausa
ka san tsarin nan,
Amsa zamunansa
goma ga Hausawa.
491. In aka sa shi mai karatu ya kiyaye,
Dole ya nemo tasa
amsa kai waye,
Kuma ai dai ana buƙatar ko waye,
Ya kula don rubuta
amsa ba ɓoye,
Shi aka son ya ƙarasa don ganewa.
492. Saɓaninsu gun karan-ɗori lura,
Aikinsu daban
tsaya nan saurara,
Zarce ba ya ɗora kalmomi sara,
Bai kuma tara zuntukanmu ya ɗoɗɗora,
Ba ya biɗar wurin da za a yi nunkawa.
493. Ba ya zuwa a tsakkiya sai dai ƙarshe,
Can aka sa shi za
ka hango shi a tarshe,
Bai da kama da
tarinmu na kwashe,
Ɗan layi ake gaban kalmar ƙarshe,
Jimlar ta ƙire a neme ka cikawa.
494. Ba a saka shi sau guda don a kula shi,
Dole a ɗiɗɗiga shi nan ga muhallin shi,
Haka ne zai fi
kyau ga doka a kula shi,
Kar a yi ɗan guda hakan na kwaɓe shi,
Sau uku ko aji
biyar ba a hanawa.
495. An ce kog ga raƙumi, shi ga..... to ida,
An so wanda zai isar da jawabin da,
Yai lura da yadda zai sa ga takarda,
Kar ya yi ɗan guda, ya ƙara gaba sada,
Zarce ne guda biyar to shiga ƙyargawa.
496. Masu bugun ƙasa, a jinsi na mutane,
Mu nan Hausa yanzu boka Arne ne,
Shi muka ba irin
cikon jimlar gane,
Yau ƙarya ƙasa take in ji... su wane,
Mai duba da yag ga yau za shi macewa.
497. Zarce ukku an ka sa nan ga rubutu,
Ba laifi a sa su
don masu karatu,
Su sani ba
turaddadin ko ɓaɓatu,
Ko da fiye ma abin
nan ya kyautu,
Ko haka an ka yi shi duk ba a hanawa.
498. Labari na zuciya tambi.. abokai,
Wansu su zana
fuska kuma ba kai,
An kuma tsara duk
abin an bi matakai,
Doka ce ta ayyana
kar ka bi son kai,
Ko biyu an ka sa
abin bai sauyawa.
499. Zarce ba a yin sa sau ɗaya ko ƙaƙa,
Kul kul kar a sa
guda don sauƙaƙa,
In ka sanya ɗan guda ka kitsa
tufƙa,
An saɓa wa ƙa’ida an saka sarƙa,
In aka yi shi sau guda
sai sokewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.