Ticker

    Loading......

Zato Zunubi Ne

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Shi wai zato (suspicion) yana daga cikin manyan kaba’irai na zunubi ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Zato iri na biyu ne: Kyakkyawan zato da Mummunan zato.

(1) KYAKKYAWAN ZATO shi ne: Yi wa musulmin da ba a san shi da wani mummunan aiki ba kyakkyawan tunani, da kawar da duk wani zargi na aikata ba daidai ba daga gare shi har sai abin ya bayyana a fili ƙarara daga gare shi. Kamar abin da Allaah ya faɗa a kan ƙissar ƙazafin da munafukai suka yi wa Nana Aishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa:

لَّوۡلَاۤ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ ظَنَّ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَـٰتُ بِأَنفُسِهِمۡ خَیۡرࣰا وَقَالُوا۟ هَـٰذَاۤ إِفۡكࣱ مُّبِینࣱ

Meyasa a lokacin da kuka ji shi muminai maza da mata ba su yi zaton alkhairi ga rayukansu ba, kuma suka ce wannan kiren ƙarya ne mabayyani? (Surah An-Nuur: 12).

Kuma Al-Bukhaariy (6061) ya riwaito daga hadisin Sahabi Abu-Bakrah (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

 « إِنْ كَانَ أَحَدُكُمْ مَادِحًا لاَ مَحَالَةَ فَلْيَقُلْ أَحْسِبُ كَذَا وَكَذَا . إِنْ كَانَ يُرَى أَنَّهُ كَذَلِكَ »

Idan ya zame wa ɗayanku lallai sai ya yi yabo ga wani, to ya ce: ‘Ina zaton sa kaza da kaza.’ Idan yana tsammanin shi haka ɗin ya ke.

Waɗannan nassoshin sun nuna:

(i) Haƙƙin musulmi ne a kan sauran musulmi su kare mutuncinsa, kar su amince da duk wani zargi na zubar da mutunci da ake yayatawa a kansa, har sai abin ya bayyana a fili ƙarara.

(ii) Ba a yarda musulmi ya zaƙe wurin yin yabo ga wani musulmi ba, don kar ya cutar da shi ta hanyar ɗaukaka shi da ƙoƙarin wanke shi, wanda hakan kan iya kai shi ga hallaka.

(iii) Yi wa musulmi na-gari kyakkyawan zato har a lokacin da ya aikata kyakkyawa, domin ba a san haƙiƙanin abin da yake ɓoye na al’amuransa ba.

(2) MUMMUNAN ZATO kuwa shi ne: Yi wa musulmin da aikin sharri bai bayyana daga gare shi ba tunanin cewa yana munana aiki a ɓoye. Daga nan kuma a cigaba da mu’amalantar sa a kan hakan. Allaah Ta’aala ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَبْ بَعْضُكُمْ بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَنْ يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَحِيمٌ ٢١۝

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato zunubi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan´uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai. (Surah Al-Hujuraat: 12).

Kuma Muslim (6701) ya riwaito daga hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ »

Ku yi nesa da zato. Domin dai zato shi ne mafi ƙaryar labari.

 

Waɗannan nassoshin kuma sun nuna:

(i) Ma’anar Sashen Zato shi ne mummunan zato ga musulmin da ba a san shi da bayyana munanan ayyuka ba.

(ii) Bai halatta ga wani musulmi ya yi wa irin wannan musulmi mummunan zato ba, balle kuma har ya je bincike da neman sanin halinsa.

(iii) Malamai sun nuna wajibi ne a nisanci irin wannan zaton a kan irin wannan musulmin da ba a ga wata alama a kan yana munana ayyuka ba.

(iv) Ƙin bin wannan umurnin na nisantar irin wannan mummunan zaton ya zama haram kenan ga musulmin da ya aikata shi.

(v) A ƙarƙashin wannan, maganarsa cewa: Zato Zunubi ne ya zama babban zunubi kenan, ba ƙaramin zunubi ba, irin waɗanda sallah da sadaka suke kankarewa.

(vi) Kodayake wannan irin zaton bai shiga cikin mafiya girman zunubai masu fitarwa daga musulunci kamar shirka da kafirci ba, amma dai dole mai aikatawa ya yi tuba da sharuɗɗanta kafin mutuwarsa.

(vii) Yana daga cikin siffar Imani mutum ya nisanci irin wannan mummunan zaton ga musulmi, idan dai ba wani abu ne da ya bayyana a fili ba.

Allaah ya ƙara mana kariya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments