Addu'ar Ziyarar Makabarta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

SLM Malam wacce addua'a mamaci yafi bukata ? ko kuma Idan an ziyarci kabarin sa wacce addu'a za'a masa ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum as salam, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya shar'anta ziyarar makabarta saboda tana tuna lahira, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 3237, kuma Albani ya inganta shi.

Musulmi Yana da kyau ya Rika ziyarar makabarta, zuciyarshi zata cika da tausayi da imani, Sai kaga kana aikata ayyukan kwarai, Sai kaga Allah ya datar dakai kana yi mashi biyayya, kana lizimtar abubuwan da Allah ya ce ayi, kana nisantar abubuwan da Allah ya hana. Haka nan Kuma ziyarar musulmi zuwa makabarta tana sanya musulmi ya Rika tsoron wannan rayuwar ta duniya, musamman idan ya tsaya a gaban kabari tsayuwa ta dubo da tunani, kana tunanin halin da waɗanda ke cikin kaburburan suke a lokacin da suna duniya, suna Kai da kawo, suna ayyuka mabanbanta, Amma fa yanzu gashi basu iya aikata komai daga cikin abubuwan da suke aikatawa a duniya, abunda zai tseratar dasu kadai ayyukansu na Alkhairi da suka aikata a duniya, sannan Sai Kai kayi tunani a karan kanka, kaima Wani lokaci zaka kasance a cikin irin wannan halin. Wannan Sai ya taimakeka wurin yin aiki na kwarai a nan duniya, domin tseratar da kanka daga azaba a ranar hisabi.

Ana bukatar Mai ziyarar makabarta yayima mamatan dake kwance a cikin kaburbura addu’ah, kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ya koyar da sahabbanshi, addu’ar ita ce kamar haka

اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ.

Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota waɗannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan waɗanda suka gabata daga cikinmu da waɗanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku.

اللهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَاعْفُ عَنْهُ وَعَافِهِ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِمَاءٍ وَثَلْجٍ وَبَرَدٍ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلًا خَيْرًا مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجًا خَيْرًا مِنْ زَوْجِهِ، وَقِهِ فِتْنَةَ الْقَبْرِ وَعَذَابَ النَّارِ.

Ya Allah ka gafarta masa, ka yi masa rahama, ka kiyaye shi, ka yafe masa, ka karrama masaukinsa, ka yalwata mashigarsa, ka wanke shi da ruwa, da ruwan qanqara, da ruwan sanyi, ka tsaftace shi daga kurakurai, kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga datti, ka canja masa wani gida da ya fi gidansa, da iyalan da suka fi iyalansa, da matar da ta fi matarsa, ka shigar da shi Aljannah, ka tsare shi daga azabar qabari, da azabar wuta.

اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِحَيِّنَا وَمَيِّتِنَا وَشَاهِدِنَا وَغَائِبِنَا وَصَغِيْرِنَا وَكَبِيْرِنَا وَذَكَرِنَا وَأُنْثاَنَا. اللَّهُمَّ مَنْ أَحْيَيْتَهُ مِنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى اْلِإسْلاَمِ وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَّا فَتَوَفَّهُ عَلَى اْلِإيْمَانِ.

Ya Allah Ka gafarta wa rayayyunmu da matattunmu, da kanananmu da manyanmu, da mazanmu da matanmu, da halartattunmu da waɗanda basa nan daga cikinmu. Ya Allah wanda Ka raya shi daga cikinmu to Ka raya shi a kan Imani, Wanda kuma Ka matar daga cikinmu to Ka matar da shi a kan Musulunci. Ya Allah kada Ka haramta mana ladansa, kada kuma Ka ɓatar da mu bayansa.

Wannan addu'a ta kasance Manzon Allah yana yi wa mamaci idan ya zo yi masa sallar jana'iza. Don haka ya halasta a ci gaba da yi wa mamaci wannan addu'ar da makamantanta ko da bayan yi wa mamaci Sallah ne.

Allah muke roko daya gafartawa mamatanmu, mu Kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani. 🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments