Banbancin Annabi Da Manzo

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum mallam mene ne banbancin Annabi da Manzo?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullah Wabarkatuhu.

    Malamai sunyi maganganu dayawa akan banbancin Annabi da manzo.

    Dukkan manzo Annabi ne amma ba dukkan Annabine manzoba.

    Banbancin Annabi da manzo shi ne

    MANZO shi ne wanda Akaiwa wahayin Shari'a sabuwa aka umarce da isar da ita,

    ANNABI shi ne wanda akaiwa wahayin shari'a amma ba'a Umarceshi ya isar da ita ga mutane ba, saidai wannan ban-bancin baya kubuta daka matsala da rikitarwa, Domin Annabi ma An Umarceshi da Da'awa dakuma Isarda sako ga mutane, dakuma hukunci, saboda haka Shaikul Isalam Ibnu taimiyyah ya ce

    Abunda yake dai-dai Shi ne:

    MANZO shi ne: wanda aka aiko zuwa wasu mutane kafirai Waɗanda suke karyatashi.

    ANNABI Kuma shi ne: Wanda aka aiko zuwa wasu mutane muminai da shari'ar Annabinda yagabaceshi yasanardasu yayi musu hukunci, kamar yanda Allah madaukakin Sarki ya ce: Surah: Al-Maaida, Ayat: 44

    اِنَّاۤ اَنْزَلْنَا التَّوْرٰٮةَ فِيْهَا هُدًى وَّنُوْرٌۚيَحْكُمُ بِهَا النَّبِيُّوْنَ الَّذِيْنَ اَسْلَمُوْا

    Mun saukarda Attaura acikinta akwai shiriya da haske Annabawa Suna hukunci da ita, gawadanda Suka Mika wuya, sukai imani

    Annabawan Banu Isra'ila Suna Hukunci da Attaurar da Aka saukarwa Annabi Musa Alaihissalamu

    Amma fadin Allah madaukakin sarki

    (وَخَتَمَ النَّبيِّينَ)

    Cika makin Annabawa

    Dangane da Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam, baice cika makin manzanni ba.??

    Saboda cika Manzanci baya Nufin cike Annabta, Amma rufe Annabci yana Nufin cike Manzanci da Annabta saboda haka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce

    ( Babu Wani Annabi Abayana) Baice ( Babu wani Manzo Abayana ba).

    Saboda yasan Babu wani manzo ko Annabi abayansa shi ne cika makin Annabawa da Manzanni Sallallahu Alaihi wasallam.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.