Budurwa Mai Tsananin Sha'awa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum mallam dafatan ananan lfy don Allah inada tambaya mace ce budurwa bata taɓa aure ba, kuma tana da sha'awa gaskiya mai karfi domin ko sumbata ko kusancin mace da namiji tagani anayi sai taji hankalinta na tashi haryakai ga tanajin fitar wani ruwa mai yauki kumburin gaba dakuma sai taji kaman Abu ya tokaremata kofan gaban nata shin tokarewan alamace ta budurcinta cikakke ne saboda kaman kofan arufe take kuma shin wannan ruwan zaisa tayi wanka ne a duk lokacinda yafita?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

    Da farko Tsarki kawai za ki yi, Sannan Kuma Zaki nemi Miji kiyi Aure. Domin Wannan Matsalar Taki Tana da Alaka da Rashin Aure. Shi ne Abin da ya janyo Miki Wannan Karfin sha'awar. Amma da za ki yi Aure In shà Allahu Baki da Damuwa.

    Rashin Aure ga 'ya Mace babu Abin da baya Haddasa Mata Wallahi Har ciwon Hauka Yana Haddasawa ga Ya Mace ko Namiji, Shiyasa Idan Mukaga Mutum yana Da ciwon Hauka Muke Bayar da Shawarar a Aurar Dashi ga Mace irinsa ko a Aurar da ita ga Namiji Mai ciwo irin Nata kuma da ikon Allah, Idan an Kulla wannan Auren Za ka ga Abin Yayi Sauki. Koda ba Gabaki ɗaya Bane, Za ka ga Cewar Ba yadda Aka San shi ba.

    Sabida haka Rashin Aure ga Mai Hankali, Mai Lafiyayyan Kwakwalwa Mace ko Namiji. Ba Karamin Bala'I bane.

     A zamanin Sayyadina Umar. Da karfi da yaji Ake Kama Samari a ɗauki Dukiyar Baitil Mali A Aurar dasu ga Yan Mata Wadanda Suka Isa Aure. Sabida Daidaita Zamani. Domin Ba'a yin Aure Lalle Zamani Zai Rikice. Kuma za a Dinga Samar da 'yayan da Basu da Uba, za a dinga Tsintar Jinjirai a kwalabati ko a kan tituna ko a Kangon da ba'a gama Gineshi ba.

    Tabbas idan haka tana Faruwa Zamani ya Gurbace.

    Ya Allah ka bamu Mafita Akan Zamanin Mu da Zamanin 'ya'yan Mu da wadanda Zasu Zo bayansu. Allah ta'ala yasa mudace

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.