𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul
Laah. Mutum ne yake neman yarinya da aure, amma kafin a kai ga sanya musu rana
sai kawai ya ji ta fita a ransa, ba kuma don wani laifi da ta yi ba. To wai
idan ya daina cigaba da neman za a ce ya cuce ta? Kuma ko zai iya sake samun
wata irinta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Bai kamata wani daga cikin masu
neman auren juna ya jawo abin da zai sa a fasa cigaba da neman auren da aka
fara ba, sai fa in da wani ƙwaƙƙwaran dalili ne da shari’a ta yarda. Saboda yin
hakan yana daga cikin siffofin munafukai ne. Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam)
ya ce:
Alamomin munafuƙi
guda uku ne:
إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ ، وَإِذَا ائْتُمِنَ
خَانَ ، وَإِذَا وَعَدَ
أَخْلَفَ
Idan ya zo bayar da labari sai ya
yi ƙarya,
kuma idan aka amince masa sai ya yi yaudara, idan kuma ya yi alƙawari
sai ya saɓa. (Sahih
Al-Bukhaariy: 35, Sahih Muslim: 59).
Amma idan akwai dalili, to ai ba
ma a lokacin nema kafin ɗaurawa
ba, har a bayan ɗaurawa
da tarewa ma ma’aurata suna iya rabuwa da juna kamar yadda aka sani ta hanyar
saki, a bisa ƙa’idojin
Shari’a. Watau dai
yana iya fasa neman aurenta, kamar yadda ita ma take iya fasa yarda da nemansa,
in akwai wani dalili na Shari’a.
Bayan rabuwarsu malamai sun yi
bayanin matsayin kyautar da ya shiga tsakaninsu kamar haka
(i) Idan abin da ya bayar ya
kasance a matsayin wani sashe ne na sadakin auren, to idan auren bai yiwu ba
sai a dawo masa da kyautarsa, ko da kuwa fashin yin auren daga wurinsa ne.
(ii) Amma idan abin ya zama wani
kyauta ne kawai a tsakaninsa da wadda yake nema da manufar ƙara
jawo hankalinta da soyayyarta kawai zuwa gare shi, to yanzu da auren bai yiwu
ba sai ta dawo masa da abin da ya saura na kyautarsa, muddin dai fashin yin
auren daga wurinta ne. Domin dai ai bai kamata a haɗa masa zafi biyu ba: Ga mari kuma ga tsinka
jaka?! An ce ba a sonsa, kuma an riƙe masa kyautarsa?!
(iii) Idan kuwa fasa yin auren
daga wurinsa ne, to bai kamata ya nemi ta dawo masa da kyautar ba, domin ai ba
girmansa ba ne. Da wanne za ta ji: Da zafin fashin auren ko kuwa da zafin karɓe kyautarsa? Sannan kuma
ga Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce:
Mai karɓe kyautarsa kamar kare ne ya yi amai kuma ya
koma ya lashe shi! (Sahih Al-Bukhaariy: 2622).
Sannan kuma fashin yin aure ai
bai kamata ya zama dalilin aukar da rashin mutunci, ko samar da gaba ko ƙiyayya
a tsakaninsu ba.
A ƙarshe kuma ba za a ce wai ba zai sake
dacewa da wata mace ta gari ba a cikin rayuwarsa ta gaba, matuƙar
dai ba da wani mummunan nufi na cutarwa ne ya rabu da waccan da ya fara neman
ba. wannan na Allaah ne.
Allaah ya datar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
08164363661
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.
com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook.
com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.