Ticker

Fitsarin Jariri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Macen da take sallah sai jaririn da take goye da shi ya yi fitsari har ya shafi jikinta, me ya kamata ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullah Wabarkatuhu

Malamai sun sha bamban a kan hukuncin gusar da najasa ga mai sallah. A lokacin da waɗansu suke ganin hakan sharaɗi ne, waɗansu malaman kuma suna ganin hakan wajibi ne kawai wanda kuma yake faɗuwa tare da mantuwa ko rashin iko.

Dalilin wannan maganar kuma shi ne: Hadisin da Al-Imaam Abu-Daawud (650) ya riwaito kuma Al-Albaaniy a cikin Al-Irwaa’u (284) ya inganta shi daga Abu-Sa’eed Al-Khudriy (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi sallah da takalma masu najasa a ƙafarsa. A ƙarshen hadisin kuma ya cigaba da sallar bayan ya cire su, ba a faɗi cewa ya maimaita ba.

Wannan ya nuna gusar da najasa daga tufafin mai sallah ba sharaɗi ba ne, domin in da sharaɗi ne to da kuwa ya maimaita sallar, kamar yadda Umar Bn Al-Khattab (Radiyal Laahu Anhu) ya maimaita a lokacin da ya yi sallah da janaba a bisa mantuwa.  (Tamaamul Minnah: 1/203-204)

A ƙarƙashin wannan maganar: Wabiji ne wannan matar ta kwance goyon, ta tafi ta gusar da najasar daga jikinta da tufafinta sannan ta dawo ta sake sallar, idan an ɗauki gusar da najasar sharaɗi ne. Amma ga wanda ya ɗauki gusarwar wajiba ce kawai ba za a ce sallar ta ɓaci ba. Don haka, tana iya cigaba da sallarta a haka, musamman ma idan ta ga ƙoƙarin fita don gyara tsarkin zai sanya lokacin sallah ya fita. Tun da dai malamai sun yarda cewa tsarewa ko kiyayewa a kan lokacin sallah ya fi kiyayewa a kan tsarki.

Allaah Ta’aala ya ce:

فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُمۡ وَٱسۡمَعُوا۟ وَأَطِیعُوا۟ وَأَنفِقُوا۟ خَیۡرࣰا لِّأَنفُسِكُمۡۗ وَمَن یُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Ku kiyaye dokokin Allaah da gwargwadon ikonku. (Surah At-Taghaabun: 16)

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments