Girman Rana Ya Zarce Yanda Muke Tunani

    TAMBAYA (101)

    Wasu mutanen suna cewa rana tafi duniya girma. Me yasa muke ganinta karama a sararin samaniya

    AMSA

    Masana kimiyyar sararin samaniya (Astronomers) sunce rana (ash-Shams) tana da girma wanda yakai na duniya sau 1,300,000. Kenan da za'a jefa irin duniyar nan tamu guda miliyan daya da dubu dari uku a cikin rana to zasu samu gurbin zama a cikinta. Allahu Akbar! Idanunmu ne suke ganin rana kamar wata yar karamar ball (kwallo) kamardai yanda muke hango jirgi acan qololuwar sama alhalin babba ne a zahiri. Zafin doron rana yakai 6,000 (degree celcius dubu shida), zafin cikinta kuma ya zarce 16,000,000 (degree celcius million sha shida)? Domin gane matsanancin zafin, ka tafasa ruwa, idan yakai 100°C zai fara tafasa (saboda yakai boiling point). Wani masanin kimiyya a sararin samaniya mai suna Johannes Kepler yace: "Da'ace za'a matso da rana kwatankwacin kilometer 1 da kowa dake duniyarnan ya qone saboda tsananin zafi haka kuma da'ace za'a nesantata damu misalin kilometer 1 da sai kowa ya zama qanqara saboda tsananin sanyi. Sai yayi tambaya menene dalilin dayasa aka samu tazarar kilometer 150,000,000 tsakaninmu da rana?

    Wanda Dr Brian Greene yace tambayace rhetorical ma'ana wadda bata buqatar amsa saboda kamata yayi yace mu mutane menene yasa muka tsinci kanmu a duniyarda takeda tazarar 93 million miles tsakaninta da rana (Ash-shams) wadda again itama wannan har yanzun sun gaza gano amsarta. Wanda mu kuma a matsayinmu na musulmai munsan amsar tambayoyin gaba daya: amsar tambayar farkodai tanada nasaba da wani littafi wanda Dr. Mario ya rubuta mai suna "Is God A Mathematician?" Ma'ana shin Ubangiji mai ilimin lissafine, wanda amsar hakan tana cikin sunayen Allah SWT tsarkaka 99 dinnan wato "ALHASIBU", ma'ana mai qayyadewa kokuma gwanin lissafi a ranar sakamako (Ranar lahira)

    Amsa ta 2 kuma tanada nasaba da wani maudu'i da dan uwa Shaykh John Fontain (Wanda na hadu dashi a wani program da aka gabatar a The Afficient, Kano. Malami ne a Jami'ar Manchester dake kasar England), maudu'in da ya fitar mai taken "Is Life Just A Game?" Ma'ana "Shin Rayuwarmu Anyitane Don Wasa?" wanda ya karade Clubs din Celebrities yana jefa musu wannan tambayar, wasu sun sauraresa wasu kuma sunce basuda lokacinsa. Abinda nakeson fada anan dai shine, rayuwa tanada purpose wato manufa wadda tuni Allah SWT ya fadamana a cikin Suratu Dhaariyat ayata 56;

    ( وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ )

    الذاريات (56) Adh-Dhaariyat

    Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.

    Sannan kuma munsan cewar Allah ya yalwata wannan duniyar tamu da ma'adanai (natural resources) wadanda ya tanadar domin amfani ga bayinsa kamar yanda ya fada a cikin Suratul Ankabut ayata 56;

    ( يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَةٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ )

    العنكبوت (56) Al-Ankaboot

    Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã ce, sabãda haka ku bauta Mini

    Amsar Brian Greene ta fito anan wato abinda yasa muke rayuwa a duniyar Earth (Al-ard) shine: Mu bautawa Ubangijinmu Allah SWT domin kuwa idan da ya halicci Annabi Adam AS a duniyar Mercury (kamar yanda Astronomers sukace) rayuwa bazata yiwu ananba saboda kusancin duniyar da rana domin kuwa doron kanta zabalbala yake kamar talgen tuwo, kuma kamar yanda masana din suka gano cewar average temperature ta bani Adam itace 37°C, haka kuma da ya haliccesa ya saukardashi a duniyar Neptune shima rayuwar bazatayiwu ba saboda nisan duniyar Neptune din da rana, sanyin dake kanta kadai azabane. Wancan a kimiyyance kenan ammanfa mu sani cewar babu abinda yake gagarar Allah saboda fadarSa a cikin Suratul Mulk ayata 1;

    ( تَبَارَكَ الَّذِي بِيَدِهِ الْمُلْكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ )

    الملك (1) Al-Mulk

    (Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.

    Allah SWT shine "ALHASIBU" mai qidaya komai da ajesa a muhallinsa, amsa ta fito, shakka ta fita

    Kada mu manta cewar a ranar lahira, haka za'a sauko da ranar (Ash-shams) bisa kawunan mutane (tazarar 1mile) alhalin a yanzun haka kilometer million 150 ne tsakaninmu da inda take kuma nauyinta ya zarce tonne 200,000,000,000,000,000 (A sauqaqaqqen harshe zaka iya cewa tonne septillion 200). Kasani cewar daga inda nake (Rijiyar Lemo, zuwa Zariya kilometer 157 ne kacal, zuwa Kaduna 230km, zuwa Abuja kuma 415km ne kacal, zuwa doron kan wata kuma 400,000km ne. Tafiyace ta nisan nisa, wadda saika fita daga hydrosphere, lithosphere, mesosphere, ionosphere, exosphere, troposphere, thermosphere, stratosphere har zuwa atmosphere

    Hasken rana ya ninka hasken wata sau 400,000 ko dayake daman shi wata bashida hasken kansa, domin kuwa ranto haskensa yake daga ranar kamar yanda Allah SWT ya fada a cikin littafinsa mai girma cewar shi wata (Al-qamar) Noor ne itakuma rana (Ash-shams) Siraj ce. Akarshedai abu 1 ne cikin 2 zai faru, kodai muyi ayyukan da zasu sa Allah ya sakamu a inuwar al'arshi kokuma la shakka sai munsha zafin ranar nan wanda saboda gumi sai raquma 100 su iya sha basu koshi ba, kamar yanda hadisin yazo a littafin Shaykh Abubakar Alhafiz ibn Khatheer mai suna "Albidaya wan Nihaya". Wai kuma ahakanfa wasu suketa tara haram. Shin muna tunanin a banza Mala'ila Jibrilu zai share shekaru 23 yana kawowa Ma'aiki wahayi akan hukuncin Halak da Haram? To Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya

    Muna roqon Allah Azzawajallah ya kiyaye imaninmu ya rabamu da bidi'a sannan ya yafe mana kurakurenmu

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.