Takarda da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na Ɗalibai masu karatun Digiri na Uku (PhD) a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Satumba, 2023
Fayyace Gurbin Da Sarauta Ta Mamaye A Cikin Fitattun Tatsuniyoyin Hausawa
Haruna Umar Maikwari
Tsakure
Tatsuniya hanya ce ta koyar da rayuwa ta yau da kullum. Kuma ita wani sashe ne daga
sassan adabi. Sarauta kuma tsarin mulki ne na gargajiya da aka sani tun kaka da
kakanni. Wannan jinga, tana da manufofi da suka hada da: Bayyana sarautu da
ayyukansu a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Fito da ayyukan fadawa da zaman fada
duk a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Fayyace neman auren ‘ya’yan sarakuna da yadda
ake ganinsu a tatsuniyoyin Hausawa. Hanyar da aka bi don gudanar da wannan
bincike ita ce ta karance-karancen littattafan matanoni na tatsuniyoyin
Hausawa, da wasu littafai da suka taimaka wajen samun makamar aiki da wasu
mujallu da aka buga na ilmi daban-daban da sauraron tatsuniyoyi daga wasu
mutane. An zaɓi a ɗora wannan bincike a (Literary theory wanda wasu suke ce ma
cultural theory). Shi dai wannan ra’in wani Baturen Jamus ne kuma masanin ilmin
Falsafa (Philosophy) mai suna Friedrich
Wilhelm Nietzsche wanda ya yi
rayuwarsa a tsakanin shekarun (1844 – 1900) ya samar da shi.. Sakamakon wannan binciken
kuma ya fito da ayyukan sarakunan dauri da fadawansu a cikin tasuniya da kuma
neman auren ‘ya’yan sarakuna.
1.0 Gabatarwa
Al’ada
ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Al’ada ita ce mutum, duk mutumin da
ya rasa al’ada, to ra yi hasarar abu mai muhimmanci na gudanar da rayuwa. Shi
kuwa adabi, shi ne hoton rayuwar al’umma. Idan al’ada ita ce rayuwa ta zahiri,
adabi shi ne hoton rayuwar zahiri. Kenan za a iya cewa al’ada ita ce mutum, shi
kuma adabi shi ne inuwarsa. Duk inda ka ga mutum ba za ka rasa ganin inuwarsa
ba. Sai ko wani dalili na daban. Ita kuma tatsuniya wani reshe ne daga rassan
adabi wanda ake samun cikin zube. Ita dai tatsuniya, ita ce hanyar da mutanen
dauri suke amfani da ita wajen koyar da ‘ya’yansu tsarin tafiyar da rayuwa kama
daga zamantakewa, jarunta, aure haihuwa mutuwa, buki, soyayya, hani da horo,
tsarin mulki, hukunce-hukunce, shari’a da makamantan su. Sarauta tsari ne na
shugabanci da ake gudanarwa tun lokaci mai tsawo. Wannan tsari shi ne wanda aka
sani tun kaka da kakanni. Sarki dai shi ne shugaba. Akwai waziri da sarkin fada
da shamaki da sallama da majikira da sarkin yaƙi da dai sauran sarautu da suke kewaye
da sarki. Kowane mai riƙe da sarauta yana da irin rawar da yake takawa daidai
matsayinsa.
1.2 Manufar bincike (Jinga)
Manufa
dai ita ce jigo ko abin da mai rubutu ya ƙudurci bayyanawa ko saƙo da mai
rubutu ko magana ya ke son ya isar ta hanyar da yake son ya isar. Wannan jinga
tana da manufofi da suka haɗa da:
a. Bayyana sarautu da ayyukansu a cikin tatsuniyoyin Hausawa.
b. Fito da ayyukan fadawa da zaman fada duk a cikin tatsuniyoyin Hausawa.
c. Fayyace neman auren ‘ya’yan sarakuna da yadda ake ganinsu a tatsuniyoyin
Hausawa.
1.3 Ra’in Bincike (Jinga)
An zaɓi a ɗora wannan bincike a kan ra’in (Literary theory wanda wasu suke
ce ma cultural theory). Shi dai wannan ra’in wani Baturen Jamus ne kuma masanin
ilmin Falsafa (Philosophy) mai suna Friedrich
Wilhelm Nietzsche wanda ya yi
rayuwarsa a tsakanin shekarun (1844 – 1900) ya samar da shi. Wannan masani an
haife shi a ranar 15 ga watan Oktoba a 1844. Shi ɗa ne ga Karl Ludwig da Franziska
Nietzsche. Mahaifinsa ya mutu tun yana ɗan shekara biyar, kuma ya mutu ya
bar shi da ƙaunarsa mai suna Elisabeth da wani ƙane ƙarami mai suna Friedrich,
wanda shi ma bai jima ba ya mutu ba zato ba tsammani. Haka kuma shi Nietzsche ya kasance yana amfani da
kayan kiɗa na Fiyano yana rera waƙa musamman waƙar Emerson da Friedrich da ta
Holderlin.
A shekarar 1864, Nietzsche ya shiga jami’ar Bonn. A 1865 kuma ya kasance
mabiyin Farfesa Friedrich Ritschl. Nietzsche ya samar da wannan ra’i tare
da taimakon wasu ‘yan ajinsu (Classmates) waɗanda suka haɗa da Paul Deussen, (wanda ya kasance cikin
sanannun masanan tsohon harshen nan na Sanskrit da Indic). Nietzsche
ya samu zama Farfesa a fannin ilmin harshen Girkanci da adabi a Jami’ar Basel
ta Switzerland.
Shi wannan ra’i ya kasance yana
mayar da hankali kan dalilin da ya sa a aka yi rubutu da kuma marubuci tare da
al’adar marubuci domin yanke hukunci game da abin da aka rubuta. Masu bin
wannan ra’i suna da ra’ayin cewa, ana gane haƙiƙanin ma’anar rubutu ne ba ta
hanyar duba gundarin rubutu ba, sai dai ta hanyar fahimtar al’adun mai rubutun,
da dalilin rubutun da kuma tarihin rubutun gaba ɗaya.
Wannan ra’in yana da dangantaka da aikin da za a gudanar, musamman idan aka
lura da cewa wannan aikin ana ƙoƙarin a fitar da al’adu a cikin rubutacciyar waƙa
ne. A wannan aiki ana ƙoƙarin fito da al’adu a cikin wasu zaɓaɓɓun rubutattun
waƙoƙi ne, yayin da wannan ra’in shi kuma yana goyon bayan cewa, nazartar
al’adar marubuci dole ne kafin a gane haƙiƙanin manufar rubutu. Lura da wannan,
za a ga cewa ra’in yana jaddada ra’ayin cewa akwai makusanciyar dangantaka
tsakanin abin da aka rubuta da kuma al’adar marubuci. Wannan ya nuna al’ada na
da tasiri kan rubutun marubuci, kuma rubutu na da tasiri kan al’ada.
An samu wasu waɗanda suka assasa wannan ra’in da suka haɗa da:
a. Terry Eagleton 1983, 1996 FOR Charles Swann
And Raymond Williams: Literary Theory- An Introduction Second
Edition.
b. Vince Brewton: Literary Theory
c. Andrew Bennett and Nicholas Royle: Introduction
to Literature, Criticism and Theory. Third Edition.
1.4 Hanyar Gudanar da
bincike (Jinga)
Wannan
jinga za ta yi amfani da hanyar sauraron wasu tatsuniyoyi daga wasu mutane tare
da fito da abin da ake nema a ciki. Haka kuma za a yi amfani da karance-karancen
littattafan matanino na tatsuniyoyin Hausa da suka haɗa da Jagoran Nazarin
Tatsuniya na Hadiza Salihu Koko da Tatsuniya a rubuce na Sa’idu Muhammad Gusau
da Kunne ya Girmi Kaka da Taskar Al’ada da Tarihi da Nishaɗi na Salisu Ahmed
Yakasai da Tatsuniyoyin Hausawa na Bukar Usman da dai sauransu. Akwai kuma
littattafai da suka taimaka wajen gudanar da wannan bincike da mujallu da dai
sauran abubuwan karantawa kamar kundaye da makamantansu.
1.5 Ma’anar Tatsuniya
Yahaya (1971) yana cewa “Tatsuniya ko
gatana, wani ƙagaggen labari ne wanda al’adu da tunanin al’umma suka ƙirƙiro
daidai da tunanin ‘ya’yansu (yara) domin tarbiyantar da su, cikin nishaɗi da
kuma halayyar da ta dace da irin tarbiyyar”. Abin nufi a nan shi ne ita dai tatsuniya ta tafi kan
daidai da yadda al’umma ke kallon rayuwa gaba ɗaya. Sannan kuma tunanin da ake
cikinta da halayyar da aka ganta da ita, kai hatta da salon da ake yin amfani
da shi domin isar da saƙon da take ɗauke da shi, duk masu dacewa ne da tunani
na duniyar yara.
Umar, (1987), ya bayyana
cewa, “Tatsuniya ƙagaggen labari ne da magabata kan shirya
musamman don tarbiyya bisa ga tsarin gargajiya”. Muhammad, ya ƙara da cewa “romon
kai ce ko ba da labarin wani bai ɗaya, da bai faru ba a zahirin haka nan kuma a
wannan labarin yana da tsohon tarihi saboda kaka da kakanni suka ƙirƙira shi
suka sadar da shi zuwa gare mu a tsawon lokaci.
Wani abu muhimmi da ma’anar ta zo da shi, shi ne ƙagaggen
labari na kaka da kakanni. Sun ƙirƙira shi ne a matsayin wata hanya ta cusa wa
‘ya’yansu tarbiyya domin su ta shi a matsayin Hausawa masu tunani da ɗabi’u da
halaye masu bin al’adun waɗanda al’ummar ƙasar Hausawa ta yarda da su.
A CNHN (2006) kuwa an bayyana cewa “tatsuniya labari ne da ake ba wa yara
na hikima na hikima don hira.”
Bisa ga ma’anonin da aka tattara za a iya cewa “tatsuniya ƙagaggen labari ne da Bahaushe ya tsara domin ya tarbiyantar da
‘ya’ya a kan lamurran duniya da kuma al’adunsu.
1.6 Sarauta a Ƙasar Hausa
Babu
shakka ƙasar Hausa kamar sauran ƙasashe na duniya akwai tsarin mulki. Wannan
tsari na sarauta tun asali shi aka sani. Shugabanci ne da aka fara sani a ƙasar
Hausa. Ita sarauta kamar yadda Alhassan, (1985:74) ya bayyana cewa “sarauta ita
ce wata dama ko sarari ko iko ko mulki ko jagoranci da wani ko wasu ke da shi a
kan wasu mutane musamman abin da ya shafi bayar da umarni bisa kyakkyawa ko
kuma hani bisa aikata mummuna.” Shi kuma Zarruƙ, da wasu (1988), sun bayyana
cewa” sarauta ita ce a yi wa mutane jagoranci ko jan ragama.”
Shi
kuwa Yahaya, (1992), yana ganin “sarauta ita ce mulki ko iko, wato ɗaukar
nauyin jagorancin a’umma, wanda ya haɗa da yi masu shugabanci ta hanyar tsara
hanyoyin kiyayewa da lafiyarsu da ta dukiyarsu da ma shirya masu ƙa’idojin
zaman tare ta fuskar shari’a da gudanar da hulɗar ƙasarsu da ƙasashen maƙwabta
da ƙasashen waje.
Shi
kuma Gulbi (2000) yana ganin sarauta ita ce sababbiyar hanyar da Hausawa da ma
waɗanda ba Hausawa ba suka gada tun kaka da kakanni ta amfani da wakiltar wani
mutum daga cikinsu domin ya jagorance su tare da ƙoƙarin ƙwato haƙƙin wani idan
buƙatar hakan ta taso.
Sarauta
tsarin mulki ne na gargajiya da aka san al’umma da shi tun farko. Wannan tsarin
mulki wani daga al’ummar ke shugabanta. Kuma galibi yana da mataimaka da su ke taya
shi gudabar da sarautar. Daga cikin mataimakan akwai; waziri, sarkin fada,
jakada, maji kira, shantali, shamaki, sarkin yaƙi, dogari, da dai sauransu.
Kowace sarauta na da tsarin yadda ake tafiyar da ita. Kowane daga cikin masu
riƙe da sarautar yana da aikin da yake yi wato yana da rawar da yake takawa
daidai da matsayinsa.
1.7 Sarautu a cikin
Tatsuniyoyin Hausa
Babu
shakka sha’anin sarauta al’ada ce da ta cuɗanyi al’umma. Duk da cewa a yau
akwai tsarin mulkin siyasa wannan bai hana a samu masu sarauta ba. Hasali ma
kusan dukkan shugabannin da ake yi na siyasa, sai da sa hannun masu riƙe da
sarautu. A wasu yankunan ma masarauta ke bayar da ɗan takara.
Wannan
tsari na sarauta ya yi tasiri har a cikin adabinmu na gargajiya. Ana ganin
sarauta a dukkan sassan adabin kowace al’umma.[1] A al’ummar
Hausa kuwa, kusan dukkan al’adunsu na bayyana a cikin adabin su. Wannan tsari
na al’ada, wato sarauta ana ganinsa a cikin tatsuniyoyin Hausawa kamar dai
yadda za mu gani.
1.8 Bayyanar Sarauta da
Aikin Sarki a Cikin Tatsuniyoyi
Tatsuniyoyin
Hausawa cike suke fal da tsarin sarautunsu. A zamanin dauri sarakuna su ke
tafiyar da mulki kuma komai yana ƙarƙashin kulawarsu. Wannan ya sa kusan
tatsuniyoyin da ake yi a dauri duk suna ɗauke da hotunan sarautu a cikinsu. Akwai
tatsuniyoyi irin su; tatsuniyar Yara da Kada, Ɗan Naturke, Daskin Dariɗi,
Jarumin Sarki, Sarauniya, Ɗan Agwai da Kura, Marainiya da sauransu.
1.8.1 Adalcin Sarakuna
A
tatsuniyar Yara da Kada an nuna cewa wasu yara suka je rafi wajen wanka kuma ga
shi a wannan rafin akwai kada mai haɗiye mutane. Da zuwan su sai kadan ya fito
ya fara da rabon su da waƙa yana cewa:
Maraba-maraba da
yara,
Yara sun zaka
wanka,
In ci kwai-kwai, in ci kwai-kwai.
Sai kada ya haɗiye su.
Bayan an jima ba a ga yara ba sai Innarsu ta ce wa yannan yaran
nan su je su dubo yaran nan a rafi wajen wanka da suka je ba su dawo ba. Da
suka je sai su ma kadan ya fito ya tare su da waƙar kamar haka:
Maraba-maraba da yannai,
Yannai sun biyo ƙannani,
Ƙannai sun zaka wanka,
In ci kwai-kwai, in ci kwai-kwai.
Sai kada ta haɗiye yannan yara.
Su ma yannan da aka ga ba su dawo, sai Innar su ta biya.
Ita ma kadar ta fito ta tarbe ta da waƙa ta haɗiye. Baban ya je ya bi Innar shi
ma kadar ta haɗiye shi sai sarkin garin ya tura fadawa, da suka je sai kadar ta
haɗiye su. Daga ƙarshe dai sai sarkin ya je da kansa don ya ceto su. Da kadar
ta fito sai ta fara waƙar:
Maraba-maraba da Sarki,
Sarki ya biyo fada,
Faada ya biyo baaba,
Baaba ya biyo Inna,
Inna ta biyo yannai,
Yannai sun biyo ƙannai,
Ƙannai sun zaka wanka,
In ci kwai-kwai, in ci kwai-kwai.
Sai sarki ya fito da sandarsa ya kwaɗa wa kadar. Da ta
ƙara sai ta ce na tuba ka yimin rai, sarki ya ce to fito da mutane na. Ta amayo
fadawa, ya ƙara kwaɗa mata sai ta amayo baban yaran, ya ƙara kwaɗa mata, ta
amayo Innar yaran, ya ƙara kwaɗa mata, ta amayo yannan yara, sai ya ƙara kwada
mata ta amayo yaran da ta haɗe da farko.
Wannan tatsuniya ta fito da hoton adalcin sarakuna. Domin
kuwa a madadin sarki ya kasance yana mai zaluntar al’ummarsa, sai ga shi da
kansa ya tafi wajen taimakon talakawansa.
A wata tatsuniyar kuma, an samu sarki ya yi adalci wajen
yanke hukunci a kan wanda ya kashe ɗan uwansa shi ma aka kashe shi. Misali:
Sai sarki ya ce to, a kira yaron wato yayan wanda aka
kashe, ya zo aka ba shi ƙashin ƙanensa, da ya fara busawa sai ƙashin ya ce:
“...Kai yayana, kai yayana,
Ƙashi na ne kake hurawa,
Baba ya aike mu a
daji,
Mu samo huranni,
Wana sun fi naka
kyau,
Sai ka ɗauke nawan ka
kashe ni.
Sai sarki ya ce to a akama yaron shi ma a kashe shi. Aka
kama shi aka kashe. Shike nan an yi maganin wanda ya ci amana.”
1.8.2 Jaruntar Sarakuna
Daga
cikin abin da ke sa a gane sarki ya cancanta a dauri akwai jarunta. Idan sarki
na da jarunta, yanada da duk abin da ake so a wancan lokaci. Bukar Usman ya zo
da wata tatsuniya mai suna Jarumin Sarki.
Wannan tatsuniya ta fito da jaruntar sarakuna inda suke fita yaƙe-yaƙe domin faɗaɗa
ƙasarsu. Wannan jarumin sarkin ya fita fagen daga inda yake ta famar kashe
abokan gaba.
“.......wannan
sarki ya shahara wajen yaƙe-yaƙe. Domin kuwa da ya fita fagen daga sai kashe
abokan gaba yake yi......”
(Tatsuniyar
Jarumin Sarki na Bukar Usman)
Jarunta ke sa a yi sarauta a lokacin dauri. Haka kuma yin
yaƙi wani abin bugun gaba ne ga duk wanda ya yi nasara a kansa.
1.8.3 Zaluncin Sarakuna
A
wancan lokaci duk wani abu mai kyau a gidan sarki ake kai shi kama daga mata,
dabbobi, hatsi, wata dukiya da makamantan su. Wannan zalunci ya bayyana a
tatsuniyoyin Hausawa kamar: Tatsuniyar ‘Yar Amana, Ɗan Naturke da makamantan
su.
1.8.3.1 Zaluncin Sarakuna a
Cikin Tatsuniyar Ɗan Naturke
A wannan tatsuniya an bayyana cewa akwai wata tsohuwa
wadda ta turke wani bajinin sa (Maraƙi) ya girma har ya kai maƙura. Ga misalin
abin da ya bayyana a wannan tatsuniya:
“.....A
lokacin da almajiri ya je bara gidan wannan tsuhowa, sai ta kira shi ta ba shi
abinci. Da ya shiga sai ya ga wannan babban sa a turke. Yana fita sai ya nufi
gidan sarki. Da shigar sa sai ya ce “sarki-sarki yanke min kunne na”. Sai sarki
ya ce, “idan na yanke maka kunne da me za ka jiyo mini labari?” sai ya ce, “Na
ga wani sa a gidan wata tsuhuwa wanda bai dace da kowane gida ba sai da
gidanka.” Nan take sarki ya ce a je a zo masa da wannan sa.
Da suka zo ɗaukar san sai suka fara kwance shi, ashe san
baya kwantuwa.
Sai aka bugi tsohuwar aka sauɗa mata bulala ta ce:
Kwantu-kwantu Naturke,
Ban so rabuwa da kai ba,
Sarakan bana kwaɗai gare su,
Abu kaɗan su kai ka fada,
Can fada, can fada garkar sarki.”
(Tatsuniyar Ɗan Naturke)
Wannan tatsuniya ta fito da zalunci sarakuna a fili. Da
yake a wancan lokaci sarakuna suna ƙarfi da ikon karɓe duk abin da yake ga
talaka kamar yadda ya bayyana a tatsuniya.
1.8.3.2 Zaluncin sarakuna a
Tatsuniyar Azzalumin Sarki
Ko
shakka babu da jin sunan tatsuniyar cewa “Azzalumin Sarki”. Akwai zalunci a
ciki. A wancan lokaci sarakuna sukan yi zalunci ga talakawansu. Babu mamaki
idan shugaba ya zalunci talakansa, domin kuwa ko a wannan zamani zalunci ya
zama ruwan dare ga shugabanninmu. A wannan tatsuniya an bayyana cewa akwai wani
sarki azzalumi da yake aikawa a kamo masa baƙi ya ƙwace duk abin da suka samu
su kuma ya kai su ga zaki da ke ɗaure su canye. Ga dai yadda abin yake:
.... a wani zamani an yi wani azzalumin sarki da yake sa
fadawa su tare masa baƙi ya amshe masu dukiya su kuma ya kai su ga zaki da ke ɗaure
sai zakin ya canye mutanen daga nan dukiya ta zama tasa. Wata rana sai fatake
suka biyo ta wannan garin sai sarki ya sa aka kama su, ya ƙwace dukiyarsu, ya
kai ya aje da nufin su kuma idan safiya ta waye sai ya kai su ga zaki. Ashe a
cikin jikkuna fataken nan akwai biri, sai birin da ke ciki ya kwance jikka ya
fita ya nufi inda zaki yake sai ya kwance zaki. Zaki ya fita ya afka fada ya
cinye sarki. Su kuma fatake suka kama birinsu, suka ɗauki kayan su daga nan sai
aka kawo ƙarshen zalunci wannan sarki.
Wannan
tatsuniya kai tsaye kamar yadda na faɗa tana nuna zalunci sarki ne. Akwai
tatsuniyoyi ire-iren waɗannan da ke bayyana zaluncin sarakuna.
1.8.3.3 Zalunci Fadawa.
Bafade
shi ne wanda yake zaune a majalisar fadar sarki a kodayaushe ana zaman fada da
shi. Su dai fadawa suna da sarki wanda ake kira da sarkin fada.[2] Fadawa sun
bayyana a cikin wasu tatsuniyoyin Hausawa. Galibi halayen Bafade da aka sani su
ne yin sharri da nisanta wani ga sarki a wancan zamani. Idan aka ce ma mutum
Bafade an siffanta shi da wata halayya marar kyau kenan. Fadawa sun bayyana a
cikin tatsuniyoyin Hausa kamar: Tatsuniyar Mugun Bafade.
1.8.3.3.1 Zaluncin Bafade a
Tatsuniyar Mugun Bafade
Da jin
sunan wannan tatsuniya, ya bayyana mina zaluncin ne wani Bafade ya yi. Kamar
yadda aka sani akwai fadawan da suke ba wa sarki shawara musamman idan suka ga
cewa za su ribatu da wani abu. Duba
misali a wannan tatsuniyar:
... A wani gari wai shi Katano, an yi wani sarki da
wazirinsa. Wannan waziri Bafillace ne kuma maƙetaci. A kusa da fadar sarki
akwai wani gina na wani attajiri. A bayan gidan attajirin akwai wata ƙatuwar
itaciyar kuka wadda ke da kogo. Akwai tururruwa, maciji, shamuwa da shaho da
aljani. Kullum safe sai attajirin nan ya je sun gaisa da wadannan abubuwa kuma
ya ba su abinci.
Waɗannan ƙwari sun nemi wannan attajiri da su riƙa yi masa
bauta ya ce “a’a”. Ana nan, ana nan sai wazirin sarkin nan ya kai suka
attajirin nan ga sarki kuma ya riƙa ƙulla masa makirci kala-kala. Ran nan sai
waziri ya ce wa sarki ya kamata a nuna wa attajirin nan ba kowa ba ne. Sai
sarki ya amnita. Aka haɗe buhuwan gero da dawa da masara da wake aka kira shi
ya rarrabe su. Mutumin nan ya ɗauka zuwa rarrabewa sai tururruwa ta gani ta ce
ya bari ta yi wannan aiki. Ta kira sauran danginta suka zo suka rarrabe kafin
safe sun gama. Da aka kai sai kuma wazirin bafaden nan ya ce a ce masa ya nemo
tumu, kuma ga shi ga rani ne. Sai shamuwa ta je wani yanki inda ke da damana ta
samo tumu. Da ya ga bai yi nasara ba, sai ya ce a ɓoye zoben sarki aka kira shi
aka ce zoben sarki ya ɓata ya je ya nemo shi. Sai aljani ya nemo ya kawo. Ana
haka sai maciji ya ce shi zai sari ‘yar sarki, idan aka ce meye magani sai ya
ce a kawo antar Waziri Bafillace......”[3]
1.8.4 Neman Auren ‘Ya’yan
Sarakuna
‘Ya’yan
sarakuna kamar sauran al’umma, sukan nemi aure. Galibi sukan auri wasu ‘ya’yan
sarakuna ko daga cikin talakawansu. Ana samun ‘ya’yan sarki su nemi wanda yake
talaka ko mummuna ce. Amma kuma galibi idan suka nema daga baya abin kan zamo
alheri gare su. Wasu sukan yi aure ta hanyar gasa, wasu kuma sukan yi ta hanyar
bin maganar iyaye ko ta hanyar haƙuri da dai makamantansu. Tatsuniyoyin gasar
auren ɗiyan sarakuna misalinta shi ne tatsuniyar “Daskindariɗi.” Ita wannan
tatsuniya ta zo da gasar sai an faɗi sunan ɗan sarkin, kafin ya aminta da wadda
za shi aura.
A
wannan tatsuniya an bayyana cewa wannan ɗan sarki ya ce shi zai zaɓi matar da
zai aura da kansa. Don haka sarkin ya ba shi damar haka, ya kuma ba shi dukiya.
Ɗan sarkin nan ya bar garinsu ya nufi wani gari kuma ya sauka a gidan wata
tsohuwa. Ya gaya wa tsohuwar nan abin da ke tafe da shi. Da tsohuwa ta ji haka
sai ta shiga gari wajen cigiyar mata. A daidai wannan lokaci akwai wasu mata da
suke a gida guda. A wannan gidan akwai Dawa, Gero Maiwa Shinkafa da Burtuntuna.
A cikin waɗanan ‘yan matan Burtuntuna ce ba ta da gata, saboda ba ta da uwa a
gidan.
Muhallid
shahid dai ita ma ta samu zuwa gasar da aka shirya duk wanda ya zo sai ya shiga
daga ciki ya yi waƙa kamar haka:
Dawa: Ahuwanka dai ɗan
yaro,
Ahuwanka dai,
Ɗan sarki: Wace ce
nan take mani, ahuwanka dai?
Dawa: Dawarka ce take maka ahuwanka dai,
: Mai tuwo
da daɗi,
: Ni Dawa
mai fura da daɗi.
Ɗan sarki: Na ji naki suna yarinya, ba ni nawa suna.
Dawa: Ban san ka
ba, ɗan yaro,
Ban san ka ba.
Ɗan sarki: Da ba ki
san ni ba, yarinya,
Koma da baya ki sha
kuka.
Bayan da Dawa ta shiga ɗaki don gabatar da gasar, sai ta
fito ba ta yi nasara ba don ba ta san sunansa ba. Sauran duk sun shiga abin da
ya faru da dawa shi ya faru da su. Ana nan sai ga Burtutuna ta shigo sai suka
fara tsegumi cewa wa ma ya ara mata kaya. Da ta shiga sai ta faɗi sunan. Ga dai
yadda gasar ta kaya ita da shi ɗan sarkin:
Burtuntuna: Ahuwanka
dai ɗan yaro,
Ahuwanka dai,
Ɗan sarki: Wace ce
nan take mani, ahuwanka dai?
Burtuntuna: Burtuntunarka ce take maka ahuwanka dai,
: Mai ɓata
tuwo,
: Ai ni ce
mai ɓata fura.
Ɗan sarki: Na ji naki suna yarinya, ba ni nawa suna.
Burtuntuna: Daskin-da-Riɗi
ɗan yaro,
Daskin-da-Riɗi
Ɗan sarki: Buɗe ki
shigo,
Yarinya buɗe ki shigo.
Wannan gasa dai ɗan sarki ne ya shirya ta don ya samun
matar da zai aura. Sharaɗinsa na cin wannan gasar kuma shi ne wanda ya san
sunansa. Ita ma wadda ta san wannan sunan ta sani ne ta hanyar taimakon da ta
yi wa wata tsohuwa. Wannan tatsuniyar dai ba gasar ce jigonta ba amma kuma ita
ce ta fi haska tatsuniyar.
Bayan
ta fannin gasa kuma, akwai ta hanyar biyayya ga iyaye. Wato a wannan tsari.
Idan muka duba abin da ya faru a tatsuniyar Gwaidayara. A wannan tatsuniya dai
anbayyana cewa wani mutum ne yake da mata huɗu, kuma duk yana son su ban da ta
huɗun. Sai suka samu ciki suka haihu aka samu yara mata har huɗu. ya raɗa wa
ukun suna: ga dai misali daga abin da ya auku:
“...Da matan nan huɗu suka haihu sai ya raɗa wa ukun suna
wato Halima da Jummai da A’isha. Ita kuma ‘yar matar ta huɗun bai raɗa mata
suna ba. Da uwar yarinyar nan da ba a raɗa wa suna ba ta matsa da tambaya sai
ya ce ta tafi sunan ɗiyarta Gwaidayara. Kuma haka aka ci gaba da kiranta. Da
yaran nan suka kai munzalin aure, ya yi wa kowace aure, amma ban da Gwaidayara.
Da mahaifiyar ta ga haka sai ta tambayi dalili. Inda mahaifin ya umarci
yarinyar da ta riƙa binsa a jeji. Wata rana a cikin jejin sai suka ga wani
baƙin maciji ya wuce, sai uban ya ce ta bi wannan maciji. Haka kuwa aka yi
saboda ɗa’a da biyayya da yarinyar ta ke yi wa mahaifinta ta bi shi sau da
ƙafa. Da ta bi macijin sai ya rikiɗa ya koma mutum saurayi kyakkyawa son kowa
ƙin wanda ya rasa kuma ga shi ɗan sarki. Da ganin yanayin da Gwaidayara take
ciki, sai ya yi alƙawarin zai aure ta. Haka ko aka yi.
Wata rana mahaifinta ya zo garin da take aure sai ya same
ta cikin ni’ima da walwala a sanadiyyar ɗa’a da biyayya da ta yi wa mahaifinta.
Da ya dawo gida sai ya sa aka kira dukkan ‘ya’yansa da mazansu aka tarar kowace
na cikin halin talauci da ƙunci ita da maigidanta....”
Wannan
aure da ɗan sarki ya yi na Gwaidayara, ya yi sa ne ba don komai ba sai don
biyayyar da ita yarinyar ta yi wa mahaifinta. Haka dai al’adu suke bayyana
cikin tatsuniyoyin Hausawa. Da ma dai adabi shi ne hoton rayuwar al’umma. Don
haka ba abin mamaki ba ne idan aka ga wata rayuwa ta bayyana a cikin wani reshe
na adabi.
1.9 Kammalawa
Tsarin
mulkin Hausawa wani reshe ne daga cikin rassan al’adunsu. Su kuma al’adun suna
bayyana ne a cikin dukkan sha’anonin rayuwa na Hausawa. Al’adun sun mamaye
adabinsu kusan dukkan rassan adabin Hausawa suna ƙunshe da al’adunsu. Tatsuniya
hanya ce ta koyar da tarbiyya tun a zamani dauri. Don haka al’adun da suka
shafi sarauta sun ka bayyana a cikin tatsuniyoyin Hausawa. Wannan bincike ya
gano cewa akwai sarautun Hausawa ƙunshe cikin tatsuniyoyinsu. Kama daga adalci
shugabancinsu da akasinsa, da ayyukan fadawa da auren ‘ya’yan sarakuna.
Binciken ya ratsa wasu tatsuniyoyi da suka haɗa da: Tatsuniyar yara da kogi,
tatsuniyar jarumin sarki, tatsuniyar Gwaidayara, ‘Yar Amana, Azzalumin Sarki,
Mugun Bafade, Daski-da-Riɗi da da makamantansu.
Manazarta.
Alhassan H. da Zarruq, R. (1985). Zaman Hausawa. Lagos: Academy
Press Limited.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.
Gulbi, A. S. (2000) “Sarautar Gargajiya a Ƙasa Gummi Jiya
da Yau”, Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
Ibrahim M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini:
Tasirin Musulunci a Kan Rayuwar Hausawa
ta Gargajiya.” Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero Kano.
Umar M.B. (1987), Dangantakar adabi da al’adun Gargajiya.
Triumph Publishing Company Kano.
Umar , M. B. (1982) “Dangantakar Adabi da Al’ada”. BA
Dissertation BUK.
Vince, Brewton (ND). Literary
Theory. Alabama: University of North. Ciratowa a shafin google a Ranar 5, ga Febrairu, 2019. https://www.google.com/2017/11/
Yakasai, S. A. (2012) Taskar
Al’ada da Tarihi da Nishaɗi
Yahaya, I.Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun
Sakandare. Littafi Na Ɗaya. Ibadan: University Press Plc.
Yahaya I.Y. (1971), Tatsuniya Da Wasannani 1-6, Ibadan Oɗford
University Press.
Yahaya I.Y. (1992) Darussan Hausa Dom Manyan Makarantun
Sakandare. University Press Ibadan.
Zarruk R.M. da Wasu,(1988), Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don {ananan Makarantun Sakandare, University Press Ibadan.
[1]
Sanin al’umma ne cewa kowace al’umma
tana da shugaba wanda ke shugabantar ta. Haka kuma suna da adabi wanda da shi
ake gane wannan al’ummar.
[2]
Akwai wasu mutane da suke zaune a majalisar
sarki. Kuma su wadannan mutane su ke aiwatar da umarnin sarki. Wasu sukan ba
sarki shawara ko kuma sarkin ya haɗa da su wajen aiwatar da wani abu mai kyau
ko akasinsa.
[3]
A duba Jagoran Nazarin Tatsuniya na
Hadiza Salihu Koko wanda aka yi a shekarar (2009) a shafi na 61-62.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.