Hammad

    1.
    Na gode Sarki Allah
    Mai Arziki da Jalala
    Shi É—ai ya ke da Kamala
      Kuma shi mu ke ma bauta.

    2.
    Na gai da Manzon nasa
    Mahmudu baƙon Aƙsa
    Angon Khadija da Hafsa
       Baban su Fatima Binta.

    3.
    Ga 'yar ƙasida na yi
    Manya da su nai koyi
    Domin nishaÉ—i nai yi
       Dangi ku zo ku karanta.

    4.
    Na jera baiti-baiti
    Tamkar gini da siminti
    Kuma na aje su a saiti
       Su goma 'yan matsakaita.

    5.
    Hammadu yaron Umma
    Gaishe ka sannu da himma
    Ga É—an da ya wuce goma
      Gun hankali da nagarta.

    6.
    Hammadu yaron Abba
    Wai kai da shi kas saba
    Muddin idan ka duba
       Ka gan shi, rai ya faranta.

    7.
    Kai duniya mai sauri
    Jiya nan ka ke jariri
    Amma kamar É—an shuri
       Ka girma sai makaranta.

    8.
    Hammadu na gaisheka
    Na tabbatar ba shakka
    In dai ka jure shuka
      Girbinka za ya yawaita.

    9.
    Gaishe ka yaron kirki
    Na san fa ba ka raki
    Sannunka sannu da aiki
      Hammadu É—an makaranta.

    10.
    Roƙo ga Al-Mannanu
    Allahu Ar-Rahmanu
    Ya sa ma É—an nan hannu
       Don rayuwa ta rabauta.

    Mustafa Adamu
    18.11.2023
    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.