𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Budurwa ceTa kawo wanda take so ta aure shi wanda ba
ya shaye-shaye ba ya komai, amma sai iyayenta suka ce a’a, domin wai ya taɓa yin aure kuma yana da
’ya’ya. Yaya za su yi ita da shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Abin da za su
yi guda biyu ne: Haƙuri da ƙoƙari
Su yi haƙuri wurin
bin maganar iyaye da yawaita addu’o’i ga Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala.
Kuma su
yawaita ƙoƙarin
yin bincike kan gaskiyar dalilin rabuwarsa da uwar yaran nasa.
Idan an gano
cewa rabuwarsu da ita ba zai iya cutar da zamantakewarsu ba, sai su ƙara
yin haƙuri
tare da ƙara
ƙoƙarin
sanar da iyayenta hakan, kuma da ƙara rarrashin su ta hanyar da ta dace
cikin ladabi, har su fahimci gaskiyar al’amarin.
Amma idan aka
gano cewa iyayen ba su son yarinyar ta auri wanda ya taɓa aure ne kawai, to wannan da farko dai ba
abu ne da shari’a ta hana ba. Hasali ma a halin da ake ciki yanzu, wanda ya taɓa yin aure na iya zama
shi yake iya riƙe matar fiye da wanda bai taɓa
ba, matukar dai mutumin kirki ne. Don haka, a nan ma dai sai a ƙara
ba iyayen haƙuri, a ƙara ƙoƙari wurin rarrashin su cikin ladabi da kyawawan kalmomi.
Sannan kuma da
haƙuri
wurin ƙara
yawaita addu’o’i.
Idan ba za su
iya tinkarar iyayen su da su kai-tsaye da maganar ba, suna iya sanya wasu
abokanan iyayen ko malamansu ko danginsu ko ƙawayensu ko dai sa’o’insu
da suke mutuntawa, su wuce musu a gaba, har su iya fahimtar da su irin abin da
suka kasa ganewa a cikin matsalar.
Wannan yana
daga cikin illolin fara neman aure ba tare da sanar da iyaye tun da farko ba.
Domin in da yarinyar ta fara sanar da iyayenta tun kafin ta amince da wannan
namijin a matsayin masoyinta wanda take son aurensa, kuma in da iyayen sun fara
gudanar da bincikensu a kansa tun nesa-da-ƙofa, to da kuwa, in shà Allâhu ba a samu wannan matsalar ba.
Dole ne matasa
a yau su san cewa, shari’a ba ta amince da irin waɗannan halayya na matasan zamanin yau ba: Inda
yarinya take yin gaban kanta wurin nema wa kanta namijin da take so ita da
kanta kaɗai. Wai sai
a bayan sun gama ‘fahimtar juna’ da shi ne sannan za ta kawo shi wurin
iyayenta! Kuma ta ɗauka
sai kawai su amince da ita kuma su sanya mata hannu, ba tare da bincike ko
dubawa ba, saboda kaɗai,
a ganinta: Ai ‘ba ya shaye-shaye, ba ya yin komai’.
Dole ne matasa
su san cewa, kamar yadda mawaƙin Hausa yake cewa
Aure ba abu ne
ba na wasa,
Bar neman
kyau, nemi nagarta.
Watau: Shi
aure wani ƙullin
zamantakewa ne na har-abada. Don haka yana buƙatar a samu gogewa da zurfafa bincike da
tunani da hangen nesa a cikinsa kafin a ƙulla shi.
Irin gogewa ko
ƙwarewar
da matasa ba su da ita, ko da kuwa sun haɗa
ƙarfi
da ƙarfe
a tsakaninsu don kai wa ga hakan.
Allaah ya faɗakar da mu, kuma ya ƙara
mana ilimi mai amfani.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.