Ticker

Hukuncin Auren Shege

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam menene hukuncin auren shege, Yana da karatun addini da na zamani, kuma ana yabon addinin shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullah Wabarkatuhu

Ma’anar SHEGE shi ne wanda aka samu cikinsa tun kafin a ɗaura wa iyayensa auren Sunnah a bisa ƙaidojin addinin musulunci.

A asali irin wannan ɗan ba shi da wani laifi a kan irin abin da mahaifansa suka aikata, har suka yi sanadin zuwansa duniya ta hanyar da shari’a ba ta amince ba. Mutane suna ƙyamar sa ne domin irin mummunar hanyar da aka same shi, kuma dayake a alada ba a samunsa da tarbiyya ko kyawawan ɗabi’u da halaye. Domin akasari ba ya zama abin ƙauna a wurin dangi da yan uwan iyayensa da sauran jamaar gari, wani lokaci ma har da su kansu iyayen. Duk inda ya bi sai a yi ta zunɗe ana kyara ana hantarar sa.

In dai shegantuwarsa ba ta shahara a tsakanin mutane ba, ta yadda nan gaba za'a dinga aibanta abin da kuka haifa tare, kina iya auransa, tun da mutumin kirki ne mai ilimi, kuma har ana yabon addinin shi, to ba za a ƙyamaci yin aure da shi ba. Tunda da ma abin da addinin ya tsara kenan cewa

إِذَا أَتَاكُمْ مَنْ تَرْضَوْنَ دِينَهُ وَخُلُقَهُ فَزَوِّجُوهُ

Idan wanda kuka yarda da addininsa da ɗabi’unsa ya zo muku, to ku aurar masa. (Sahih At-Tirmiziy: 886).

Mutukar ta yarda da addininsa da kuma dabi'unsa tana iya auransa kamar yadda hadisin Tirmizi ya tabbatar

Kasancewar an haife shi ba ta hanyar aure ba, ba laifinsa ba ne, Allah ba ya dorawa wani laifin wani.

Amma yana da kyau a saurari maganar iyaye tun farko kafin a amince da shi. Domin a cikin aure gida da gida ake haɗawa ba wai miji da mata kaɗai ba.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments