Hukuncin Iskar Da Ke Fita Ta Farjin Mace

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene hukuncin Iskar da ke fita ta Farjin Mace, Shin tana karya alwala ko a'a?? Ta yaya zan rabu da tusan gaba a lokacin jima'i?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Malamai Ma'abota Ilimi sunyi Saɓani Dangane da hukunci akan Iskar dake fita ta gaban Mace, Mazhabin Hanafiyya da Malikiyya Sun tafi ne a kan cewa dukkan wani abu da zai fita ta gaban Namiji ko kuma ta gaban Mace wanda kuma asali abisa al'ada ba tanan ba ne hanyar fitarsa, wato kamar irin iskar da take fita ta farjin Mata a waɗan su lokuta ko kuma tsakuwa ko tsutsa ta fita ta wajen, Malamai sukace irin wannan ba ya warware alwala, domin wannan Iskar ba daidai take da Tusa ba, Sannan sukace ba a samu wani Nassi afili Ƙarara da yake nuna cewa wannan Iskar tana warware alwala, domin Mαnzon Allαh Sallallahu Alaihi Wasallam cewa yayi:

    "لا وضوء إلا من صوت أو ريح" (رواه الترمذي)

    MA'ANA:

    Ba a sake alwala Sai dai idan anji Sautin (fitar tusa) ko kuma anji warin (tusar):

    Amma Mazhabin  Shafi'iyya da Hanabila Sukace dukkan wani abu da zai iya fita ta Farjin Mace ko Zakarin Namiji koda kuwa a bisa al'ada ba hanyar fitarsa bace kamar irin wannan Iskar ko wani abun da yake Nadiran (abinda ba a saba gani yana fita ta wajen ba) sukace dukkan waɗannan abubuwa suna warware alwala, Sannan ita kuma iskar dake fita ta Farjin Mace sunyi kiyasin ta ne da tusar dake fita ta dubura, sukace tunda dai tusa tana karya alwala to duk hukuncinsu yazama ɗaya shi da na tusa kenan, dan haka dole a sake alwala.

    Amma zance mafi inganci shine dukkan wata iska da zata iya fitowa daga gaban Mace to bata warware alwala, amma inda ta fita ne daga duburarta to ko Shakka babu alwala ta warware domin dukkan Malamai Sunyi ijmā'i akan cewa tusar dake fita ta dubura tana karya alwala danhaka dole sai an sake wata kenan, Sai dai wasu daga cikin Malamai sukace idan Mace taji wannan iska ta fito daga Farjinta to abu mafikyau shine ta sake alwala don ta kubuta daga cikin Saɓanin da Malamai sukayi

    Shi tusan gaba yana faruwa ne a lokacinda iska ya shiga gaban mace a yayin jima'i. Duk motsin datayi iskan zai rika fita kamar tusa.

    Akasarin mata suna famadashi, ba wani abun damuwa bane musamman ga matan da suke da girman gaba sunfi fuskantar wanan matsalar, haka yin saduwa ta baya wato goho shima yana sa fitar tusa ta gaba sabida iska na samun shiga da fita.

    Hanya mafi sauki shi ne kiraka kula da gabanki sosai duk banyan kwanciya da mijinki. Yin ruwan dumi da hanyoyin matsai farjinki sune manyan hanyoyin magance shi.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.