Ticker

Hukuncin Maganin Ƙarfin Ango

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Menene matsayin maganin ƙarin ƙarfi da sabon ango yake sha kafin ranar tarewa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Abu na-farko da malamai suka ambato a cikin Ladubban Tarewar Aure shi ne

Ango ya tausasa wa amarya a daren farko: Saboda hadisin Asmaa’u Bint Yazeed (Radiyal Laahu Anhaa) wadda ta ce: Na yi wa A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) ado da kayan kwalliya a ranar tarewarta domin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), sannan na kira shi domin ya ganta ba a cikin hijabi ko lulluɓi ba. Sai ya zo da ƙwaryar madara, kuma ya zauna kusa da ita. Ya sha, sannan ya miƙa mata. Sai ta sunkuyar da kanta saboda kunya. Ni kuma sai na tsawace ta, na ce:

خُذِي مِنْ يَدِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ

Ki karɓa daga hannun Annabi (Sallal Laahu Alaihi wa Alihi wa Sallam)!

Sai ta karɓa, ta sha ɗan kaɗan. (Al-Imaam Ahmad ya fitar da shi, kuma Al-Munziriy ya ce: Yana da isnadi nagartacce, in ji Al-Albaaniy a cikin Adaabuz Zifaaf).

Daga wannan hadisin ya fito fili cewa

1. Abu ne mai kyau a yi wa amarya kwalliya a ranar da za a kai ta ta tare a gidan angonta. Amma a kula, kar kwalliyar ta wuce ƙaida da dokokin da shariar musulunci ta shimfiɗa.

2. Babu sanya hijabi ko lulluɓi ga amarya a lokacin da ango zai shiga ɗakinta a ranar tarewa.

3. Ƙin yin maganar amarya ga ango da aladar sayen-baki duk ba koyarwar Sunnah ba ce.

4. Amarya ta zama mai kunya a ranar tarewarta abu ne mai kyau wanda kuma ya dace da Sunnah.

5. Miji ya shiga wurin amarya da wani abin ci na marmari, kamar kazar amarya ta al’ada, daidai ne.

6. Miji ya yi ƙoƙarin tausasawa da kwantar da hankalin amarya da natsar da zuciyarta a wannan ranar Sunnah ne.

A ƙarƙashin wannan:

(i) Dole ne ango ya zama mai lura da taka-tsantsan a wurin saduwa da amarya a karon farko, musamman sabuwar budurwa.

(ii) Lallai ya tabbatar ya gama motsar da sha’awarta da farko kafin farawa, kuma ya yi mata a hankali, ban da gaggawa.

(iii) Galibi a wannan ranar tana cikin tsoro da rashin natsuwa da damuwa saboda rashin sanin yadda abin zai kasance a tsakaninsu, don haka ba lallai ya samu haɗin kanta a ranar ba.

(iv) In aka samu haka, lallai ya yi haƙuri har zuwa lokacin da alamura za su daidaita, ya samu haɗin kanta ga buƙatarsa.

(v) Zai iya yiwuwa cewa a saduwar farko ya ji mata ciwo a wurin, don haka dole ne ya ba ta lokaci har ta samu wurin ya warke kafin ya dawo ya cigaba.

Don Allaah! Wanda ya je ya sha maganin ƙarin ƙarfi tun kafin ranar tarewa ta yaya zai iya tuna waɗannan abubuwan, balle har ya tausaya wa amaryarsa budurwa sabuwar balaga?

Yaushe zai san cewa tana cikin ciwo da raɗaɗi ko zogi a bayan saduwar farko, balle har ya iya barin wai sai ta warke kafin ya komo?

Kuma menene fa’idar maganin da tun a farkon haɗuwa zai haifar da ƙyama da tsoron amarya ga ango waɗanda kuma wai auren soyayya aka yi musu?!

A gaskiya muhimmin abu ne, musamman a wannan zamanin, a riƙa zaunar da matasa masu neman auren juna, ana wayar musu da kai a kan waɗannan abubuwa tun kafin tarewa.

Kuma dole ne mutanenmu su san cewa, yawancin waɗannan magungunan suna da ɓarna ko ta’adi da suke haifarwa ga lafiyar jiki. Allaah ya datar da mu

WALLAHU A'ALAM

Shaikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments