𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul
Laah. Ko ya halatta mayar da kan ta irin na ‘dada’?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laahi Wa Barakaatuh.
Kodayake asali a musulunci, babin
kwalliya da ado yana sashen halacci ne, wanda mutum yana iya yin duk abin da ya
so har sai an samu wani dalilin da ya hana aikata hakan a shari’a. To sai dai
kuma malamai sun tattauna a kan mas’aloli guda biyu
1. Zaƙewa da zuce iyaka ko ƙa’ida a wurin kwalliya, mai
kai wa ga sauya halittar Allaah.
2. 4886, Sahih Sai kuma koyi da
wanda ba musulmi ba a cikin kaya da nau’ukan kwalliyarsu.
Duk waɗannan kuwa abubuwan hanawa ne a shari’a. Abdullaah
Bn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) ya samo hadisi daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) cewa
لَعَنَ اللَّهُ الْوَاشِمَاتِ وَالْمُسْتَوْشِمَاتِ وَالنَّامِصَاتِ وَالْمُتَنَمِّصَاتِ وَالْمُتَفَلِّجَاتِ لِلْحُسْنِ الْمُغَيِّرَاتِ خَلْقَ اللَّهِ
Allaah ya la’anci mata masu yin
zane a fatar jiki da masu neman a yi musu zanen, da mata masu aske gashin gira
da masu neman a aske musu gashin, da mata masu yin feƙe haƙora
don yin wushirya, masu sauya halittar Allaah. (Sahih Al-Bukhaariy: 4886, Sahih
Muslim: 5695).
Don haka duk kwalliyar da ta kai
ga sauya halittar Allaah an haramta ta, kuma tana da la’anar Allaah a kan ta. A
fili yake kuwa cewa mayar da gashin kai irin wannan sauya halittar Allaah ne.
Allaah ya shiryar da mu.
A kan mas’ala ta-biyu kuwa, watau:
koyi da waɗanda ba
musulmi ba, akwai hadisi sahihi daga Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya
riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa
وَمَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ
Kuma duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to shi yana
tare da su. (Sahih At-Targheeb: 2089).
Waɗanda
ake koyi da su a kan wannan abin a yau kuwa, idan ma ba kafirai ne tantagarya
ba, to kuwa fasiƙai ne masu ficewa daga ɗa’ar
Allaah Ta’aala, waɗanda
kuma sam! addini bai yarda a yi koyi da su ba.
Sannan kuma ana koyi da irin waɗannan mutanen ne kawai
saboda dalilin ƙauna da soyayyar da ake yi ga ɗabi’unsu
da hanyarsu. Wannan kuwa mummunan abu ne mai hatsari a rayuwar musulmi. Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« الْمَرْءُ مَعَ مَنْ أَحَبَّ »
Mutum yana tare da wanda yake so.
(Sahih Al-Bukhaariy: 6168, Sahih Muslim: 6888).
Ban kuwa san wani musulmin
gaskiya da yake sha’awar a tashe shi a ranar Al-Ƙiyamah tare da wani daga cikin Kafirai ko
fasiƙai
ko munafukai ba!
Allaah ya shiryar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat. whatsapp. com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.