Ticker

Hukuncin Mijin Da Matarsa Ta Neme Shi Da Jima'i Ya Ƙi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

malam ina roko a taimaka min da amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matarsa don saduwa ita kuma ta ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijinta shi kuma yaki, shima ya aikata zunubi ne ko ko?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa "Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ba ta amsa masa ba, to mala'iku za su tsine mata har ta wayi gari" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1436.

Idan shi miji ne matarsa ta nemeshi yaƙi ya aikata Haramun, amma shi ba za muce mala'iku sun kwana suna la'antar sa ba, dan hadisi bai zo akan shi ba; shi mijin.

Kasancewar hadisi bai zo akan za ya kwana ana la'antar shi ba, ba shi kenuna baida laifi ba shi mijin. Tun da haƙƙi na saduwar Aure, haƙƙi ne ' MUSTARAƘ ' ( BAINAL RUJLI WAL MAR'AT ) , mace ta na da haƙƙi a wurin mijinta na ya kusanceta dan ya biya mata buƙatar ɗa namiji ba tare da ta yi sha'awar fasiƙanci ba. Haka shima yana da wannan haƙƙin a wurin ta.

Haqiqa acikin Qur'ani an bayyana haqqin mata akan mijinta kamar yadda aka bayyana haqqin Miji akan matarsa. Allah yana cewa

ﻭَﻟَﻬُﻦَّ ﻣِﺜْﻞُ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻦَّ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻟِﻠﺮِّﺟَﺎﻝِ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻦَّ ﺩَﺭَﺟَﺔٌ

Kuma sū matan Sunada misalin abinda yake akansu, yadda aka sani. Kuma maza sunada wata daraja akansu (su matan). (Suratul Bakarah,  228).

Allah maɗaukakin sarki ya ce: Matanku sutura ne a gare ku, ku ma sutura ne a gare su.  Mata suna da haƙƙi irin wanda mazaje su ke da shi a kan mata ɗin".

Dan haka kar namiji ya ɗauka tunda shi, hadisi bai zo a kan za a kwana ana la'antar sa ba, shi kenan ya yi duk abinda yaga dama. Lalle a kwai haƙƙi akansa wanda Ubangiji ( swa ) zai tambaye shi a ranar tashin ƙiyama.

Abinda malamai suke cewa shine: Namiji ba shi da laifi, idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin namiji da mace sun bambanta, saboda mace za'a iya saduwa da ita ko da ba ta da sha'awa, namiji kuwa sai yana da sha'awa, zai iya saduwa, sannan yanayi da al'ada ya tabbatar da cewa namiji ba zai iya saduwa da mace ba duk lokacin da ta name shi, wannan yasa malamai da yawa na sharia suka tafi akan cewa ba'a yiwa namiji Fyaɗe, tun da in azzakarinsa bai motsa ba, ba zai sadu da mace ba, mace kuwa an cimma daidaito za'a iya mata Fyaɗe saboda kamar tirmi take, in har an samu tabarya shikenan, wannan yasa za'a iya saduwa da mace tana bacci saɓanin namiji. don haka akwai bukatar ace yana da nishaɗi kafin ya iya jima'i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin da za ta iya.

Kasancewar an ce babu la'anta akansa idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba, ba ya nuna ya halatta ya cutar  da ita, yaki saduwa da ita a lokacin da yake da nishaɗi.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments