𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, malam don Allah a warware mana abin da wannan matar take cewa : Ita
maganar rike hannu a salla sunna ce ta shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam. haka
nan sakin hannu kamar da yake a bukhari da muwadda duk sun nuna cewa Shugaba
Sallallahu Alaihi Wasallam a farkon rayuwarsa ya saki hannunsa a Sallah, daga
baya ya kama hannu daga Karshen Rayuwarsa ya cigaba da sakin hannu, to kunga
sunnar da Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam yayi sau biyu tafi wadda yayi sau ɗaya. Imamu Malik Imamu
Darul hijra a mazhabarsa rike hannu a Sallar Farilla Makruhi ne kuma shine
Malamin sauran malaman mazhabar da Saudiyya take bi, don haka sakin hannu bazai
zamo bidi'a ba, kuma ba zamu nunawa imamu Malik sanin Sunnar Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam ba. Ya kamata jama'a musan cewar in mutum bai rushe mana abinda
muke kai ba, be kamata mu, mu rushe masa nasa ba.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To 'yar'uwa
rike hannu a sallah Sunnah ne kamar yadda Wa'il ɗan
Hujr ya rawaito ya ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana yi a cikin sallah,
kamar yadda ya tabbata a SAHIHI Müslim a hadisi mai lamba ta: 401.
Babu ko hadisi
guda ɗaya Wanda ya
tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana sakin hannu a sallah, ko da
a kaddara ya saki a farkon musulunci daga baya ya rike, sakın ba zai zama
Sunnah ba, tun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana aiki ne da wahayi,
wahayi kuma a hankali yake zuwa, kamar yadda ba'a shar'anta sallah ba sai a
daren Isra'i, babu kuma wanda zai ce barin sallah ya halatta tunda babu ita a
farkon musulunci.
An rawaito
riwayoyi daban-daban daga Imamu Mâlik akan rike hannu a sallah, daga ciki akwai
riwayar Ibnul-kasim a Mudawwanah waccce take nuna hallacin rike hannu a Nafila
da kuma karhancin rikewa a Farilla, akwai kuma riwayar Ashhabu da Muddarif da
Abdulmalik da Ibnu Nafi'i daga Imamu Malik wacce take nuna halarcin rikewa a
Farilla da nafila, kamar yadda Ibnu Abdul Barr ya ambata a Istizkar 2/291 da kuma
kuma mai littafin Albayan wattahsi a l /394.
Imamu Mâlik ya
rawaito hadisin rike hannu a sallah a cikin Muwadda, a lamba ta : 290, saidai
wasu malaman suna cewa ya karhanta rikewa a cikin sallar farilla ne a riwayar
Ibnul-Kasim saboda ya saɓawa
aikin mutanan Madina.
Duk da
kasancewar Imamu Mâlik bajimin malami mai tsoron Allah, saidai a matsayinsa na ɗan adam yana iya yın
kuskure, sannan wasu hadisan da ayyukan sahabbai suna iya ɓuya gare shi, kamar yadda
ya tabbatar da hakan a maganganunsa, wannan yasa lokacin da halifan zamaninsa
ya so ya iyakance aikin mutane a hadisan da suka zo a Muwadda, Imamu Malik ya
hana shi, ya kafa hujja da cewa: a wajan malaman Madina kawai ya yi karatu,
akwai wasu malaman da bai haɗu
da su ba.
Rike hannu a
sallah Sunnah ce tabbatacciya daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam kuma hakan
shi ne aikin mafi yawan sahabbai da tabi'ai da manyan malamai, ba za'a barta
saboda wani malami ba, tare da cewa : wanda ya saki hannu a sallah, bai yi
laifi ba, kuma sallarsa ta yi.
Allah ne mafi
sani.
Dr. Jamilu
Yusuf Zarewa
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.