𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Malam! Mutum ne
ya saki Matarsa tana da juna biyu, To ya hukuncin wannan sakin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullah
Wabarkatuh.
Mutumin da ya saki Matarsa tana
da juna biyu Matsala biyu ce a taƙaice
1. Matsala ta Farko:- shin saki
ya yuwu ko bai yuwuba? Alal haƙiƙa saki ya yuwu, kuma saki a lokacin da
mace take da juna biyu; saki ne wanda ya halatta duk da cewa a cikin malaman fiƙihu
akwai masu cewa saki da juna biyu bai halatta ba suna ƙirgashi a cikin Adɗalaƙul
bida'i. Amma a cikin nafsin ƙur'ani
za a fahimci cewa ya halatta, wanda wannan shi ne fatawar sauran malaman.
Dalilin faɗin Allah maɗaukakin
sarki: " Mata ma'abauta juna biyu iddarsu shi ne su haife a binda ke cikin
cikinsu"
To kaga da sakin bai halitta ba;
da Allah ba zai shagalta wajen faɗin
yadda za su yi idda ba, yadda Ubangiji ya tsaya ya yi sharhin yadda za suyi
idda, wannan dalilin ne a kan cewa sakin ya yuwu, wannan dalilin ne kan cewa
sakin ya halatta, to dan haka duk wadda aka saka da juna biyu sakin ya halatta
kuma ya yuwu ( ta saku ).
Yanzu abinda ya rage shi ne
iddarta ba za ta fita daga ciki ba, har sai lokacin da ta haihu, ko yau aka
saketa sai ta haihu gobe ko jibi, ka ga kwana biyu kenan to ta fita daga idda
ya halatta tayi Aure.
2. Sannan abu na gaba:- wajibi ne
ga miji ( wanda ya sake ta ) ya zamanto ciyar da ita, shayar da ita, tufar da
ita, duk suna a wuyansa gidan da za ta zauna ya biya haya, in gidan iyayen ta
ne ciyarwa da shayarwa duk suna a wuyansa har lokacin da za ta haihu, idan ta
haihu kuma dole ne ya ciyar da ita dan ta shayar da ɗansa, sai dai in ya samu wata mai shayarwa
su kai ittufaƙin yadda zai biya, ya karɓe
ɗan ya kai mata, saboda
a shari'ance a kwai wannan, amma in ba haka ba shi zai riƙa
ciyar da ita saboda shayar da ɗansa."
WALLAHU A'ALAM
✍️ Abu Rukayya Falale
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐅𝐀𝐂��𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.