Hukuncin Sallah Da Tufafin Da Jinin Haila Ya Shafa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Mace ce ta yi sallar Azahar da La’asar da tufafin da jinin haila ya shafa, ba ta sani ba sai da ta zo wanki. To ko za ta rama sallolin ne?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

    Jinin haila dai najasa ne a haɗuwar dukkan malamai. Don haka, in ya shafi tufafi ba za a yi sallah da shi ba sai bayan an wanke shi. Yadda za a yi wankin kuwa shi ne

    A fara da kankare shi ko murtsuke shi domin a gusar da sandararren jikinsa da ya bushe a kan tufar.

    Daga nan sai a sa ruwa mai tsarkakewa a wanke daidai wurin da ya shafa sosai.

    A ƙarshe ana iya yin amfani da magarya ko wani sabulu domin ƙara tsabtacewa.

    Sai kuma a ɗebo ruwa a yayyafa wa sauran tufar har sai ta jiƙu gaba ɗayanta.

    Daga nan ana iya yin sallah a cikinta. (Silsilah Saheehah: 299).

    Amma matar da ta yi sallah a cikin tufan da yake dauke da wannan najasar, to ba za ta fita daga dayan biyu ba: Ko dai ya zama ta yi hakan da gangar ne ko kuma da mantuwa.

    Idan da gangar ne, ita ma ko dai ya zama tana da ikon gusar da najasar kamar yadda aka ambata a sama, ko kuma ya zama ba za ta iya ba.

    Idan za ta iya gusar da najasar amma kuma ta ki yi har ta yi sallar da haka, to sallarta ba ta yi ba. Dole sai ta sake ramawa a bayan tuba da neman gafarar Allaah Ta’aala a kan hakan.

    Idan kuwa ba ta samu ikon gusar da najasar ba, ko ba ta samu wani tufan da za ta iya sanyawa da wannan mai najasar ba, ko kuma ta ji tsoron lokacin sallar zai fita kafin ta yi wadancan ayyukan, to sai ta yi sallarta a haka tare da najasar, kuma sallar ta yi, in shà Allâh. Domin kamar yadda malamai suka ce, shi gusar da najasa sharadi ne a sallah amma yana tare da iko ne kuma da tunawa. Saboda abin da Allaah ya ce

    { لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا }

    Allaah ba ya dora wa kowane rai face dai iyakan iyawarsa. (Surah Al-Baqarah: 286).

    Idan kuwa ta yi sallar a cikin tufafin masu najasa a bisa mantuwa ko rashin sani ko tilasci ne, to a nan ma sallarta ta yi babu wata ramuwa a kanta, in shà Allâh. Saboda ayar da ta gabata, sannan kuma da hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    « إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِى الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ ».

    Hakika! Allaah ya yafe wa al’ummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta ta a kansa. (Sahih Al-Jaami’: 1731).

    Sai dai kuma duk da haka za ta ɗauki wadancan matakan na gusar da najasar daga jikin tufar domin sallolin da za su biyo baya.

    Allaah ya kara mana fahimta.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.