Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sauya Launin Gashin Kai

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Don Allaah menene hukuncin rina gashin kai (colouring) ga mace ko namiji?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

1. Idan furfura ce aka rufe ta da baƙin launi, to haram ne. Saboda hadisin Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu Anhumaa) wanda ya ce: An zo da Abu-Quhaafah a ranar Fat-hu Makkah alhali kansa da gemunsa farare fat kamar gonar auduga, sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« غَيِّرُوا هَذَا بِشَىْءٍ وَاجْتَنِبُوا السَّوَادَ »

Ku sauya wannan da wani abu, amma ku nisanci baƙi. (Sahih Muslim: 5631).

2. Idan kuma da wani launi ne ba baƙi ba, shi ma ya halatta. Saboda hadisin Anas (Radiyal Laahu Anhu), wanda ya ce

قَدِمَ النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - وَلَيْسَ فِى أَصْحَابِهِ أَشْمَطُ غَيْرَ أَبِى بَكْرٍ ، فَغَلَفَهَا بِالْحِنَّاءِ وَالْكَتَمِ

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya iso Madinah alhalin a cikin Sahabbansa babu mai wani abu na furfura a kansa sai Abubakar, sai ya riƙa rufewa da hinna da katam. (Sahih Al-Bukhaariy: 3919).

Hinna shi ne lalle, ana amfani da shi a sauya launin gashi zuwa ja. Shi kuma katam yana sauya shi zuwa ruwan ƙwai.

3. Idan kuma ba furfura ba ce, kawai dai so ya ke ya ƙara wa gashin baƙi, ko kuma idan ya sauya shi da wani launin don shaawar ransa kawai, to wannan ma halal ne a asali. Ban san wani abin da ya hana hakan ba.

4. Amma yana iya zama makaruhi ko haram ma idan ya zama ya yi hakan domin koyi ne da waɗansu fasiƙai ko kafirai, kamar yadda abin yake aukuwa a yau. Saboda maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ »

Duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to shi yana cikinsu. (Abu-Daawud: 4033, kuma Al-albaaniy ya inganta shi a cikin Al-Irwaa’: 2691)

Sannan kuma da maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« إِنَّ الْيَهُودَ وَالنَّصَارَى لاَ يَصْبُغُونَ ، فَخَالِفُوهُمْ »

Yahudawa da Nasara ba sa rina furfurarsu, don haka ku saɓa musu. (Sahih Al-Bukhaariy: 3462, Sahih Muslim: 5632).

Ban san wani dalili da ya keɓance maza kaɗai a cikin hukuncin waɗannan hadisan, ya cire mata ba. Sai dai duk an san cewa, gashin mace musulma al’aura ce - ko ta rina shi ko ba ta rina ba - wanda ya zama wajibi ta rufe shi, sai dai ga waɗansu daga cikin muharramanta kaɗai. Kamar yadda Allah Yace

وَقُلْ لِّـلْمُؤْمِنٰتِ يَغْضُضْنَ مِنْ اَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوْجَهُنَّ وَلَا يُبْدِيْنَ زِيْنَتَهُنَّ اِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَـضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلٰى جُيُوْبِهِنَّۖ وَلَا يُبْدِيْنَ زِيْنَتَهُنَّ اِلَّا لِبُعُوْلَتِهِنَّ اَوْ اٰبَاۤٮِٕهِنَّ اَوْ اٰبَاۤءِ بُعُوْلَتِهِنَّ اَوْ اَبْنَاۤٮِٕهِنَّ اَوْ اَبْنَاۤءِ بُعُوْلَتِهِنَّ اَوْ اِخْوَانِهِنَّ اَوْ بَنِىْۤ اِخْوَانِهِنَّ اَوْ بَنِىْۤ اَخَوٰتِهِنَّ اَوْ نِسَاۤٮِٕهِنَّ اَوْ مَا مَلَـكَتْ اَيْمَانُهُنَّ اَوِ التّٰبِعِيْنَ غَيْرِ اُولِى الْاِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ اَوِ الطِّفْلِ الَّذِيْنَ لَمْ يَظْهَرُوْا عَلٰى عَوْرٰتِ النِّسَاۤءِۖوَلَا يَضْرِبْنَ بِاَرْجُلِهِنَّ لِيُـعْلَمَ مَا يُخْفِيْنَ مِنْ زِيْنَتِهِنَّۗ وَتُوْبُوْۤا اِلَى اللّٰهِ جَمِيْعًا اَيُّهَ الْمُؤْمِنُوْنَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُوْنَ

Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõywa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments