Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shafa Hannu Fuska Bayan Kammala Addu'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam menene hukuncin shafa hannu a fuska bayan gama addu'a ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam. To ɗan'uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: "Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam idan ya ɗaga hannayansa ya yi addu'a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa"  Sunanu Attirmizi : 3386.

Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi saɓani game da ingancin shi, Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta : 1345.

Akwai waɗanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra'ayin Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu'ul fataawaa  22\509, haka Albani a Silsila Sahiha 2\146.

Malaman Fiqhu sun yi saɓani game da shafar fuska bayan addu'a, wasu sun tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu-hajar  ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a ɗaya daga cikin fatawoyinsa, akwai kuma waɗanda suka tafi akan cewa ba za'a ayi ba, saboda rashin ingancin hadisan da suka zo akan haka.

Abin da na fahimta a wannan matsalar shi ne ba za'a aibanta wanda ya shafa fuskarsa ba bayan addu'a, tunda yana da magabata .

Allah ne mafi sani

 DR. JAMILU ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments