𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Malam Nakan ga
waɗansu musulmi a
lokacin da aka ambaci sunan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
idan suka yi masa salati, sai kuma su ƙara da shafa fuska da shafa ƙirji.
Wai mene ne matsayin wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul
Laah
Asali dai addinin musulunci
addini ne da ya ginu a kan sallamawa da miƙa wuya gaba-ɗaya ga Allaah Ubangijin Halittu a cikin
komai na rayuwar mutum. Don haka musulmi na-gaskiya shi ne wanda ba ya yin duk
wani abin da yake da alaƙa da ibada sai yadda Allaah Maɗaukakin
Sarki ya nuna masa a kan harshen Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam), kamar kuma yadda magabatan al’ummar nan mai albarka suka fahimta kuma
suka yi aiki da shi, gwargwadon iyawarsa.
Sannan ayyukan addini malamai sun
kasa su gida biyu ne: Akwai ayyukan ibada tsantsa waɗanda ba a bai wa musulmi daman yin komai a
cikinsu da ra’ayi ko ganin dama ba, sai dai yadda shari’a ta fayya ce kawai.
Akwai kuma ayyukan al’ada waɗanda aka yarda musulmi ya
yi abin da yake so a ciki, matuƙar bai ci karo da wani hani na shari’a ba.
Shi kuma babin salati da sallama
ga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a addini yana ƙarƙashin
bauta (ibada) ne kamar sallah da zikiri, waɗanda
ba a yin su sai yadda shari’a ta nuna kawai. Ba a cikin babin al’ada ne ya ke,
kamar cin abinci da sanya tufafi ba.
Shiyasa a nan dole ne kafin a
fara wannan aikin na shafar goshi da ƙirji a lokacin yin salati, sai an saurara
tukuna, an binciki yadda shari’a
ta koyar da yadda ake yin salatin a gare shi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam). A binciki nassoshi daga cikin hadisai sahihai, da ayyukan Sahabbai da
Tabi’ai a gani ko
akwai irin wannan abin a cikinsu? Idan an samu hakan daga ayyukan magabata
shikenan, sai a ɗauke
shi a cigaba da yin aiki da shi a matsayin wani ladabi a lokacin salatin. Idan
kuma ba a samu ba, to sai a koma ga ƙa’idar
da malamai suka shimfiɗa
a kan yadda ake gane bidi’a
Daga cikin hanyoyin da ake gane
cewa abu bidi’a ce akwai cewa: Ya zama akwai yiwuwar a aikata aiki a zamanin
farkon wannan al’ummar, amma kuma sai ba a ga sun aikata shi ba. Don haka idan
aka aikata shi a bayansu to ya zama bidi’a, rashin aikatawar kuma ya zama
Sunnah kenan. Misali: Kiran sallah domin sallar Idi da Jana’iza. Ko kuma ɗaga murya da zikiri a
lokacin raka gawa. In da Sunnah ne da an yi su a zamanin farko, irin yadda aka
yi a wadansu wuraren da shari’ar ta yarda. Don haka in da wani zai yi kiran
sallah ko zikirin a lokacin raka gawa a yau, to da kuwa ya aikata bidi’a, bai yi
Sunnah ba.
A iyakan bincikenmu da tambayarmu
a wurin malamai, ba mu ga inda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya aikata irin wannan isharar ko shafar goshi da ƙirji a lokacin yin salati gare shi ba.
Haka kuma ba mu ga aikata hakan daga Sahabbansa ko ɗalibansu da mabiyansu da kyautatawa ba. Abin
da suka aikata kuma suka karantar da na-bayansu kawai shi ne yin salatin a gare
shi kaɗai, a duk
lokacin da aka ambaci sunansa, illa iyaka!
Kasantuwar kiristoci suna nuna
alamar gicciye (cross) da hannuwansu a kan goshi da ƙirji a lokacin ambaton
sunan Yesu (Annabi Isaa (Alaihis Salaam)), wannan bai bai wa musulmi daman su ƙirƙiro
irin wannan isharar su ma a cikin addinisu ba. Domin abu ne sananne cewa
addininsu daban, addinin musulunci kuma daban. Bai halatta musulmi su ƙirƙiri
kiɗa da waƙa da
rawa ko rangaji a cikin masallaci ba, domin su ƙalubalanci abin da kiristoci suke yi a
cikin coci. Kamar yadda bai halatta Ahlus-Sunnah su ƙirƙiri
murna da farin ciki a ranar Ashura ba, domin ƙalubalantar abin da Shi’a suke yi na nuna baƙin
ciki a ranar. Ba a gyara bidi’a
da bidi’a. Sunnah ce
ake amfani da ita domin ta kawar da bidi’a.
A irin wannan wurin ne ake jawo
maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa
« مَنْ أَحْدَثَ فِى أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ فِيهِ فَهُوَ رَدٌّ »
Duk wanda ya ƙirƙiri
wani abin da ba ya cikin al’amarin
nan namu, to shi abin mayarwa ne. (Sahih Al-Bukhaariy: 2697, Sahih Muslim:
4589).
A wata riwaya kuma ya ce
« مَنْ عَمِلَ عَمَلاً لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ »
Wanda ya aikata wani aikin da
babu umurninmu a kansa, to shi abin mayarwa ne. (Sahih Muslim: 4590).
Wato ko aikatawa mutum ya yi, ba
shi ya ƙirƙiro
ba, ba za a karɓa
masa aikin ba. Domin ya zama irin aikin ’yan Wuta, saboda maganarsa (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa
« وَكُلَّ مُحْدَثَةٍ بِدْعَةٌ، وَكُلَّ بِدْعَةٍ ضَلاَلَةٌ، وَكُلَّ ضَلاَلَةٍ فِى النَّارِ »
Kuma kowace ƙirƙira
bidi’a ce, kuma kowace
bidi’a ɓata ce, kuma kowace ɓata tana cikin Wuta.
(Sahih An-Nasaa’iy: 1578, Sahih Ibn Maajah: 45)
Allaah ya ƙara mana shiriya da ƙarin
tabbata a kan bin Sunnah, ya kare mu daga afkawa a cikin komar sheɗanun mutane da aljanu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.