𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam, wai
menene hukuncin mutum ya sha fitsarinsa a matsayin magani?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah.
Ya zo a cikin
siffofin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa: Kuma yana
halatta musu daɗaɗan abubuwa, kuma yana
haramta musu munana. (Surah Al-A’raaf: 158).
Kuma tun
dayake fitsari ƙazanta ne kuma mummuna, to ya shiga cikin haramtattun abubuwa
kenan.
Shiyasa
malamai suka haɗu a
kan cewa: Fitsari da kashin mutum duk najasa ne.
Shi kuma
najasa wajibi ne kowane musulmi ya nisantar da jikinsa da tufafinsa daga gare
shi.
Kuma haram ne
musulmi ya yi amfani da najasa ta fuskar ci ko sha ko shafawa a jiki ko a
tufafinsa ko mazauninsa.
Sannan ko da
da sunan magani ne, hakan ɗin
bai halatta ba saboda maganar malamai da Al-Imaam Al-Bukhaariy ya kawo a cikin
Kitaab Al-Ashribah a farkon Baab na: 15 cewa
وَقَالَ الزُّهْرِىُّ : لاَ يَحِلُّ شُرْبُ بَوْلِ النَّاسِ لِشِدَّةٍ تَنْزِلُ ، لأَنَّهُ رِجْسٌ
، قَالَ اللَّهُ تَعَالَى : ( أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ )
Az-Zuhuriy ya
ce: Shan fitsarin mutane bai halatta ba saboda wani tsanani da ya sauka, domin shi
ƙazanta
ne. Allaah Ta’aala ya
ce: ‘An halatta muku
daɗaɗan abubuwa.’
(Abdurrazzaaq ya riwaito shi da isnadi ingantacce).
Sai kuma ya ce
وَقَالَ ابْنُ مَسْعُودٍ فِى السَّكَرِ : إِنَّ اللَّهَ لَمْ يَجْعَلْ شِفَاءَكُمْ فِيمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمْ .
Kuma Ibn
Mas’ud ya faɗa a kan
kayan maye: Haƙiƙa! Allaah bai sanya warakar ku a cikin abin da ya haramta muku
ba. (Ahmad a cikin Kitaab Al-Ashribah da At-Tabaraaniy a cikin Al-Kabeer suka
riwaito shi da ingantaccen isnadi).
Wannan maganar
ta zo marfu’iyah daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
sai dai ba ta inganta ba, kamar yadda Al-Haafiz ya kawo a cikin Fat-hul Baariy:
12/634, kuma Al-Albaaniy ya bayyana matsayinta a cikin Da’eef Al-Jaami’: 1637.
Kodayake
malamai sun tattauna a kan darussan da su ke cikin waɗannan atharan, amma dai a ƙarshe
abin da Al-Haafiz Ibn Hajr ya nuna shi ne, maganar nan ta Al-Imaam Az-Zuhuriy
ita ce ingantacciya, matuƙar dai ya tabbata cewa shan fitsari ba ya kore ƙishirwa.
(Fat-hul Baariy: 12/633).
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.