Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Baya Zuwa Sallar Jam’i A Masallaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Don Allaah mene ne hukuncin mijin da ba ya zuwa yin sallar jam’i a masallaci, sai dai ya riƙa yin sallolinsa tare da iyalinsa a gida?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Ko da yake malamai sun saɓa wa juna a kan wannan mas’alar, amma ingantacciyar maganar da ta fi rinjaye a wurinsu saboda ƙarfin hujja ita ce: Yin sallolin Jummaa da sallolin nan guda biyar na farilla tare da liman a cikin masallaci wajibi ne a kan kowane namiji baligi mai hankali, amma ba Sunnah ko Mustahabbi ba ne. Daga cikin dalilai a kan haka kuwa akwai

[1] Maganar Allaah Ta’aala cewa

وَإِذَا كُنتَ فِیهِمۡ فَأَقَمۡتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوٰةَ فَلۡتَقُمۡ طَاۤىِٕفَةࣱ مِّنۡهُم مَّعَكَ وَلۡیَأۡخُذُوۤا۟ أَسۡلِحَتَهُمۡۖ

Kuma idan kana cikinsu sai kuma ka tsaida musu sallah, to waɗansu jama’a daga cikinsu su tsaya tare da kai. (Surah An-Nisaa’: 102)

Wannan a sallar tsoro kenan.

To, idan kuwa har waɗanda suke cikin jihadin ɗaukaka Kalmar Allaah an hore su da yin sallah a cikin jama’a, to ina kuma ga wanda yake zaune lafiya a cikin gari?!

[2] Kuma Allaah Ta’aala ya ce

وَأَقِیمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱرۡكَعُوا۟ مَعَ ٱلرَّ ٰ⁠كِعِینَ

Kuma ku tsai da Allaah, ku bayar da Zakkah, kuma ku yi ruku’u tare da masu yin ruku’u. (Surah Al-Baqarah: 43).

Wannan umurni ya hukunta dole a yi sallah a tare da jama’a, amma ba ɗai-ɗai ba. Kuma umurnin Allaah a asali na wajibi ne.

[3] A cikin Sahih Muslim ya ƙulla babi mai suna

باب يَجِبُ إِتْيَانُ الْمَسْجِدِ عَلَى مَنْ سَمِعَ النِّدَاءَ

Babi: Wajibi ne a kan wanda ya ji kiran sallah ya tafi masallaci.

Al-Imaam Muslim (Rahimahul Laah) yana da fahimtar cewa zuwa masallaci don yin sallah tare da jama’a wajibi ne.

A ƙarƙashin babin kuma ya kawo hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu), wanda ya ce

أَتَى النَّبِىَّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - رَجُلٌ أَعْمَى ، فَقَالَ : يَا رَسُولَ اللَّهِ ، إِنَّهُ لَيْسَ لِى قَائِدٌ يَقُودُنِى إِلَى الْمَسْجِدِ . فَسَأَلَ رَسُولَ اللَّهِ -صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - أَنْ يُرَخِّصَ لَهُ فَيُصَلِّىَ فِى بَيْتِهِ ، فَرَخَّصَ لَهُ . فَلَمَّا وَلَّى دَعَاهُ فَقَالَ : « هَلْ تَسْمَعُ النِّدَاءَ بِالصَّلاَةِ » . فَقَالَ نَعَمْ . قَالَ « فَأَجِبْ »

Wani mutum ne makaho ya zo wurin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Ya Manzon Allaah! Ba ni da ja-goran da zai ja ni zuwa masallaci. Sai ya roƙi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi masa rangwame ya yi sallah a cikin gidansa, sai kuwa ya yi masa rangwamen. Amma da ya juya sai kuma ya kira shi ya ce: Shin ko kana jin Kiran Sallah? Ya ce: E. Sai ya ce: To, sai ka amsa (ka zo masallacin). (Sahih Muslim: 1518)

Idan dai mai larurar makanta kuma mara ɗan-jagora bai samu sassaucin ya yi sallah a gida ba, yaya mai lafiya sarai zai samu wannan sassaucin?!

[4] Kuma Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« مَنْ سَمِعَ النِّدَاءَ فَلَمْ يَأْتِهِ فَلاَ صَلاَةَ لَهُ إِلاَّ مِنْ عُذْرٍ »

Duk wanda ya ji kiran sallah amma kuma bai je masa ba to ba shi da sallah, sai dai ko in domin wani uzuri. (Sahih Ibn Maajah: 645).

Don haka dai zuwa masallaci ga wanda ya ji kiran sallah wajibi ne, sai dai in yana da wani uzurin da ya hana shi. Kuma uzuri a nan shi ne kamar rashin lafiya, ko ruwan sama da makamantan haka.

[5] Sannan kuma Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ لَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِحَطَبٍ فَيُحْطَبَ ، ثُمَّ آمُرَ بِالصَّلاَةِ فَيُؤَذَّنَ لَهَا ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلاً فَيَؤُمَّ النَّاسَ ، ثُمَّ أُخَالِفَ إِلَى رِجَالٍ فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ بُيُوتَهُمْ ، وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ لَوْ يَعْلَمُ أَحَدُهُمْ أَنَّهُ يَجِدُ عَرْقًا سَمِينًا أَوْ مِرْمَاتَيْنِ حَسَنَتَيْنِ لَشَهِدَ الْعِشَاءَ »

Na rantse da wanda raina ke a hannunsa! Na so in yi umurni da a tattaro ƙirare, sannan in yi umurnin a kira sallah, sai kuma in umurci wani mutum ya yi wa mutane limanci, sai ni kuma in koma ga mazajen nan da ba su zuwa masallaci in ƙona gidajensu a kansu. Na rantse da wanda raina ne hannunsa! Idan da ɗayansu ya san zai samu ƙashi mai tsoka a jikinsa, ko kuma kofato biyu na akuya masu kyau, wallahi! Da ya halarci sallar ishai. (Sahih Al-Bukhaariy: 644, Sahih Muslim: 651).

Idan da yin sallah a masallacin tare da liman Sunnah ne ba wajibi ba ne, to da kuwa bai yi musu barazanar ƙona gidajensu a kansu ba. Wannan ya isa babban gargaɗi ga masu ƙin zuwa masallacin, da waɗanda ma suke zuwa a makare. Allaah ya faɗakar da mu.

[6] A cikin Sahih Muslim ya ƙulla wani babi na musamman ya ce

باب صَلاَةُ الْجَمَاعَةِ مِنْ سُنَنِ الْهُدَى

Babi a kan cewa: Sallah a cikin jama’a tana daga cikin Sunnonin Shiriya.

A ƙarƙashin babin kuma ya kawo hadisin Abdullaah Bn Masud (Radiyal Laahu Anhu) cewa

مَنْ سَرَّهُ أَنْ يَلْقَى اللَّهَ غَدًا مُسْلِمًا فَلْيُحَافِظْ عَلَى هَؤُلاَءِ الصَّلَوَاتِ حَيْثُ يُنَادَى بِهِنَّ فَإِنَّ اللَّهَ شَرَعَ لِنَبِيِّكُمْ -صلى الله عليه وسلم- سُنَنَ الْهُدَى وَإِنَّهُنَّ مِنْ سُنَنِ الْهُدَى وَلَوْ أَنَّكُمْ صَلَّيْتُمْ فِى بُيُوتِكُمْ كَمَا يُصَلِّى هَذَا الْمُتَخَلِّفُ فِى بَيْتِهِ لَتَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ وَلَوْ تَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ لَضَلَلْتُمْ وَمَا مِنْ رَجُلٍ يَتَطَهَّرُ فَيُحْسِنُ الطُّهُورَ ثُمَّ يَعْمِدُ إِلَى مَسْجِدٍ مِنْ هَذِهِ الْمَسَاجِدِ إِلاَّ كَتَبَ اللَّهُ لَهُ بِكُلِّ خَطْوَةٍ يَخْطُوهَا حَسَنَةً وَيَرْفَعُهُ بِهَا دَرَجَةً وَيَحُطُّ عَنْهُ بِهَا سَيِّئَةً وَلَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا يَتَخَلَّفُ عَنْهَا إِلاَّ مُنَافِقٌ مَعْلُومُ النِّفَاقِ وَلَقَدْ كَانَ الرَّجُلُ يُؤْتَى بِهِ يُهَادَى بَيْنَ الرَّجُلَيْنِ حَتَّى يُقَامَ فِى الصَّفِّ.

Duk wanda yake son ya haɗu da Allaah a gobe (Qiyama) alhalin yana musulmi, to ya kiyaye a kan waɗannan sallolin a duk inda aka yi kiran zuwa a yi su. Domin lallai Allaah ya shar’anta wa Annabinku (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) Sunnonin Shiriya, kuma lallai ne su ɗin suna daga cikin waɗannan Sunnonin na Shiriya. To da za ku riƙa yin sallolin a cikin gidajenku, kamar yadda wannan makararren yake yin sallar a cikin gidansa, to da kuwa kun rabu da sunnar Annabinku. In da kuma kun rabu da sunnar Annabinku, to da kuwa kun ɓace. Kuma babu wani mutumin da zai yi tsarki kuma ya kyautata tsarkin, sannan ya fita da nufin zuwa wani masallaci daga cikin masallatan nan, face kuwa Allaah yana rubuta masa lada da kowace takawa yake yi, kuma yana ɗaukaka masa daraja da ita, kuma yana kankare masa zunubi da ita. (Ibn Mas’ud ya ce:) Haƙiƙa! Ni na gan mu, babu mai barin zuwa sallah a masallaci sai dai munafukin da munafuncinsa ya bayyana a fili. Haƙiƙa! Ya kasance ana zuwa da wani mutum, a ɗauko shi a tsakanin mazaje biyu, har sai an tsayar da shi a cikin sahu. (Sahih Muslim: 1520).

Watau dai namiji ya riƙa yin sallah a gida ba Sunnar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba ce, ba ɗabi’ar musulmin farko ba ne, kuma hanyar mutanen da suke neman kauce wa hanyar ɓata ne. Allaah ya taimake mu.

[7] Haka kuma Abud-Dardaa’i (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« مَا مِنْ ثَلاَثَةٍ فِى قَرْيَةٍ وَلاَ بَدْوٍ لاَ تُقَامُ فِيهِمُ الصَّلاَةُ إِلاَّ قَدِ اسْتَحْوَذَ عَلَيْهِمُ الشَّيْطَانُ فَعَلَيْكَ بِالْجَمَاعَةِ فَإِنَّمَا يَأْكُلُ الذِّئْبُ الْقَاصِيَةَ ».

Babu waɗansu mutane uku a wani ƙauye ko wani daji da ba a tayar da iƙamar sallah a cikinsu face kuwa lallai sheɗan ya yi rinjaye a kansu. Don haka ka kula da sallah a cikin jama’a, domin kura tana cin akuyar da ta yi nesa da saura ne. (Sahih Abi-Daawud: 511, Sahih An-Nasaa’iy: 817).

Idan kuwa ba a yarda mutanen ƙauye ko daji su ƙi yin sallah a cikin jamaa ba, to yaya za yarje wa mutanen cikin gari ko birni a kan haka?!

[8] Kuma Abu-Sa’eed Al-Khudriy (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِذَا كَانُوا ثَلاَثَةً فَلْيَؤُمَّهُمْ أَحَدُهُمْ وَأَحَقُّهُمْ بِالإِمَامَةِ أَقْرَؤُهُمْ »

Idan sun kasance mutum uku ne, to ɗayansu ya yi musu limanci. Kuma wanda ya fi cancantar yin limanci shi ne wanda ya fi su karatun Alqur’ani. (Sahih Muslim: 1561)

Idan mutane uku an ɗora musu yin sallah a cikin jam’i, to yaya kuma mazauna unguwar da take ɗauke da ɗaruruwa ko dubannin mutane?! Wannan ma dalili ne a kan wajibcin yin sallah a cikin jama’a.

[9] Kuma a cikin Sahih Al-Bukhaariy ya ƙulla babi mai suna

باب وُجُوبِ صَلاَةِ الْجَمَاعَةِ

Babin Wajibcin Sallah a cikin jama’a.

Watau dai Al-Imaam Al-Bukhaariy (Rahimahul Laah) ma yana ganin yin sallah a cikin jama’a wajibi ne, ba Sunnah ko mustahabbi ba.

Sai kuma ya kawo maganar Al-Hasan Al-Basariy (Rahimahul Laah) cewa

إِنْ مَنَعَتْهُ أُمُّهُ عَنِ الْعِشَاءِ فِى الْجَمَاعَةِ شَفَقَةً لَمْ يُطِعْهَا

Idan mahaifiyarsa ta hana shi zuwa sallar isha’i a cikin jama’a bai halatta ya yi mata biyayya ba.

Al-Haafiz Ibn Hajr (Rahimahul Laah) ya kawo cikakkiyar riwayar wannan atharin daga cikin Kitaab As-Siyaam na Al-Imaam Al-Marwaziy (Rahimahul Laah) da isnadi sahihi daga maganar Al-Hasan ɗin

فِي رَجُلٍ يَصُومُ يَعْنِي تَطَوُّعًا فَتَأْمُرُهُ أُمُّهُ أَنْ يُفْطِرَ قَالَ فَلْيُفْطِرْ وَلَا قَضَاءَ عَلَيْهِ وَلَهُ أَجْرُ الصَّوْمِ وَأَجْرُ الْبِرِّ قِيلَ فَتَنْهَاهُ أَنْ يُصَلِّيَ الْعِشَاءَ فِي جَمَاعَةٍ قَالَ لَيْسَ ذَلِكَ لَهَا هَذِهِ فَرِيضَةٌ

Dangane da mutumin da yake yin azumin nafila sai mahaifiyarsa ta umurce shi da ya karya shi? Sai ya ce: Ya karya shi ɗin kawai. Babu ramuwa a kansa. Kuma yana da ladan azumin da kuma ladan biyayya ga mahaifiyarsa. Sai kuma aka ce: Idan ta hana shi zuwa sallar Isha’i a cikin jama’a fa? Ya ce: Wannan ba haƙƙinta ba ne. Wannan farilla ce. (Fat-hul Baariy: 2/202)

Idan ba a yarda ya bi maganar mahaifiyarsa wurin ƙin zuwa sallah a cikin jamaa ba, to yaya za a amince ya bi maganar wanda bai kai ta matsayi ba, kamar mahaifi ko mata ko ɗa ko kuma son zuciyarsa!!

[10] Malaman da suke ganin yin sallar a cikin jama’a ba wajibi ba ne sun kafa hujja ne da waɗansu hadisai kamar wannan

Riwayar Abdullaah Bn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa), cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« صَلاَةُ الْجَمَاعَةِ تَفْضُلُ صَلاَةَ الْفَذِّ بِسَبْعٍ وَعِشْرِينَ دَرَجَةً »

Sallar Jama’a ta fifita a kan sallar mutum guda da daraja ashirin da bakwai. (Sahih Al-Bukhaariy: 645, Sahih Muslim: 1509).

A wata riwaya ta Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya ce

 « صَلاَةٌ مَعَ الإِمَامِ أَفْضَلُ مِنْ خَمْسٍ وَعِشْرِينَ صَلاَةً يُصَلِّيهَا وَحْدَهُ »

Sallah tare da Liman ta fi sallah ashirin da biyar da mutum ya yi shi kaɗai. (Sahih Muslim: 1508).

Dalilinsu a nan shi ne cewa: Tun da dai sallar a cikin jama’a fifikon daraja ne kawai take da shi a kan wacce aka yi ba a cikin jam’in ba, wannan ya nuna kenan sallar mutum guda ma ta inganta.

Sai dai kuma kasantuwar sallarsa shi kaɗai ta inganta wannan bai kawar da zunubin barin wajibin yin ta a cikin jama’a da aka ɗora masa ba. Shiyasa malamai suka bayyana cewa, domin yin sallarsa shi kaɗai ta inganta wannan bai nuna sallar a cikin jama’a ba wajiba ba ce, musamman dayake da ma ɗabi’ar wajibi kenan a samu ladansa ya nunnunku da yawa. (Dubi As-Shaikh Al-Albaaniy a cikin Tamaamul Minnah, shafi 277)

[11] Waɗansu kuma suna ƙin zuwa sallar tare da limamin ne da hujjar cewa, ba su san yanayin limamin ba: Na-kirki ne, ko ba na-kirki ba ne.

A nan malamai sun nuna cewa, yana daga Aqidar Ahlus Sunnah ce yin sallah a cikin masallaci ko da kuwa limamin ba mutumin kirki ba ne. Al-Imaam At-Tahaawiy (Rahimahul Laah) ya ce

( وَنَرَى الصلاة خَلْفَ كُلِّ بَرٍّ وَفَاجِرٍ مِنْ أَهْلِ الْقِبْلَة )

Kuma muna ganin halaccin yin sallah a bayan kowane mutum na-kirki ko na-banza daga cikin musulmi (masu fuskantar alqibla). (Al-Aqeedatut Tahaawiyyah:)

[12] Ibn Abil-Izz Al-Hanafiy (Rahimahul Laah) a wurin sharhin wannan maganar ya ambato riwaya a cikin Sahih Al-Bukhaariy mai cewa

 أَنَّ عَبْدَ الله بْنَ عُمَرَ - رَضِيَ اللهُ عَنْهُ - كَانَ يُصَلِّي خَلْفَ الْحَجَّاجِ بْنِ يُوسُفَ الثَّقَفِي ، وَكَذَا أَنَسُ بْنُ مَالِكٍ ، وَكَانَ الْحَجَّاجُ فَاسِقًا ظَالِمًا

Abdullaah Bn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya kasance yana yin sallah a bayan Al-Hajjaaj Bn Yuusuf At-Thaqafiy, haka ma Anas Bn Maalik. Kuma Hajjaaj ya kasance fasiƙi ne azzalumi.

Sai kuma ya sake kawo riwaya daga cikin Sahih ɗin dai cewa

« يُصَلُّونَ لَكُمْ ، فَإِنْ أَصَابُوا فَلَكُمْ وَلَهُمْ ، وَإِنْ أَخْطَئُوا فَلَكُمْ وَعَلَيْهِمْ »

Suna yi muku limanci, to idan sun dace ku da su duk kun dace. Idan kuma sun yi kuskure, to ku kun dace su kuma ta shafe su.

Daga nan kuma sai ya ce

اعْلَمْ ، رَحِمَكَ الله وَإِيَّانَا : أنه يَجُوزُ لِلرَّجُلِ أَنْ يُصَلِّي خَلْفَ مَنْ لَمْ يَعْلَمْ منه بِدْعَة وَلَا فِسْقًا ، بِاتِّفَاقِ الْأَئِمَّة ، وَلَيْسَ مِنْ شَرْطِ الِائْتِمَامِ أَنْ يَعْلَمَ الْمَأْمُومُ اعْتِقَادَ إِمَامِه ، وَلَا أَنْ يَمْتَحِنَه ، فَيَقُولُ : مَاذَا تَعْتَقِدُ ؟ ! بَلْ يُصَلِّي خَلْفَ الْمَسْتُورِ الْحَالِ

Ka sani, Allaah ya yi maka rahama tare da mu: Ya halatta mutum ya yi sallah a bayan wanda bai san wata bidi’a ko fasiƙanci daga gare shi ba, a haɗuwar dukkan limamai. Kuma ba shi daga cikin sharaɗin koyi da liman cewa sai mamu ya san aqidar limaminsa, ko kuma ya jaraba shi ya ce: Mecece aqidarka?

Shi dai ya yi sallah kawai a bayansa wanda bai san halinsa ba.

Sannan kuma ya ce

وَلَوْ صَلَّى خَلْفَ مُبْتَدِعٍ يَدْعُو إلَى بِدْعَتِهِ ، أَوْ فَاسِقٍ ظَاهِرِ الْفِسْقِ ، وَهُوَ الإمَامُ الرَّاتِبِ الَّذِي لَا يُمْكِنُهُ الصَّلَاةُ إِلَّا خَلْفَه ، كَإِمَامِ الْجُمْعَة وَالْعِيدَيْنِ ، وَالْإِمَامِ في صلاة الْحَجِّ بِعَرَفَة ، وَنَحْوِ ذَلِكَ - : فَإِنَّ الْمَأْمُومَ يُصَلِّي خَلْفَه ، عِنْدَ عَامَّة السَّلَفِ وَالْخَلَفِ . وَمَنْ تَرَكَ الْجُمْعَة وَالْجَمَاعَة خَلْفَ الْإِمَامِ الْفَاجِرِ ، فَهُوَ مُبْتَدِعٌ عِنْدَ أَكْثَرِ الْعُلَمَاءِ . وَالصَّحِيحُ أنه يُصَلِّيهَا وَلَا يُعِيدُهَا

Kuma idan da zai yi sallah a bayan ɗan bidi’a wanda yake kira zuwa ga bidi’arsa, ko fasiƙin da fasiƙancinsa ya bayyana, alhali kuma shi ne limami ratibi wanda ba zai yiwu a yi sallar ba sai dai a bayansa, kamar limamin Jumaa ko sallolin Idi biyu ko kuma limamin sallah a lokacin hajji a arfa, da makamantansu, to a nan ya halatta mamu ya yi sallah a bayansa kawai a wurin ɗaukacin malaman farko da waɗanda suka biyo bayansu. Kuma duk wanda ya bar yin sallah a bayan wani limamin da ba na-kirki ba, to shi ma ɗan bidi’a ne a wurin mafiya yawan malamai. Ingantacciyar magana dai: Ya halatta ya yi sallar kuma ba zai maimaita ta ba.

Har dai zuwa inda ya ambato ƙissar Uthmaan Bn Affaan (Radiyal Laahu Anhu) lokacin da yan tawaye suka kewaye gidansa, kuma wani daga cikinsu ya je ya yi wa mutane limanci. Shi ne wani ya tambayi Uthman (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Kai ne fa babban limamin dukkan jamaa, wannan kuma da ya yi wa mutane limanci limamin yan fitina ne! Sai ya ce

 ( يَا ابْنَ أَخِي ، إِنَّ الصلاة مِنْ أَحْسَنِ مَا يَعْمَلُ النَّاسُ ، فَإِذَا أَحْسَنُوا فَأَحْسِنْ مَعَهُمْ ، وَإِذَا أَسَاءُوا فَاجْتَنِبْ إِسَاءَتَهُمْ )

Ɗan ɗan’uwana! Ita sallah fa ita ce mafi kyawun abin da mutane suke aikatawa. Don haka idan suka kyautata sai ka kyautata tare da su. Idan kuma suka munana to, sai ka nisanci munanawarsu.

Har zuwa inda ya ce

وَأَمَّا إِذَا أَمْكَنَ فِعْلُ الْجُمُعَة وَالْجَمَاعَة خَلْفَ الْبَرِّ ، فَهَذَا أولى مِنْ فِعْلِهَا خَلْفَ الْفَاجِرِ . وَحِينَئِذٍ ، فَإِذَا صلى خَلْفَ الْفَاجِرِ مِنْ غَيْرِ عُذْرٍ ، فَهُوَ مَوْضِعُ اجْتِهَادِ الْعُلَمَاءِ : مِنْهُمْ مَنْ قَالَ : يُعِيدُ ، وَمِنْهُمْ مَنْ قَالَ : لَا يُعِيدُ .

Amma idan ya iya samun damar yin sallar Juma’a da ta jama’a a bayan limami mutumin kirki, to wannan shi ya fi kamata fiye da yin ta a bayan mutumin da ba na-kirki ba. A ƙarƙashin wannan, idan ya yi sallah a bayan limamin da ba na-kirki ba kuma ba tare da wani uzuri ba, to a nan ne malamai suka saɓa a cikin ijtihadinsu (ƙoƙarinsu). Daga cikinsu akwai wanda ya ce: Ya maimaita kawai. Akwai kuma wanda ya ce ba zai maimaita ba. (Sharhu Aqeedatit Tahaawiyyah: 2/409)

Haka nan dai har zuwa ƙarshen maganarsa (Allaah ya ƙara masa Rahama).

Muhimmin al’amari dai a nan, babu dalilin da zai sa namiji mai ƙarfi da lafiya ya ƙi zuwa masallaci, ya zauna ya riƙa yin sallah a gida tare da iyalinsa.

Lallai a yi wa irin wannan mutum nasiha, a jawo hankalinsa ga irin waɗannan nassoshin, da fatar Allaah ya shirye shi, ya dawo kan hanya tare da sauran musulmi.

Allaah ya ƙara mana shiriya.

WALLAHU A'ALAM.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments