Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Farka A Makare Tare Da Janaba Ta Yadda Idan Ya Tsaya Yin Wanka Lokacin Sallah Zai Fita

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya tashi da janaba a makare, kuma ya zama ba zai iya yin wanka har ya samu jam’in sallar Asubah ba, to wai a irin wannan halin zai iya tsarkake jikinsa daga ƙazantar, ya yi alwala kawai sannan ya je masallaci don ya samu jamin? Daga baya kuma in ya yi wankan tsarki wai sai ya rama waccan sallar da ya yi? Haka ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Al-Bukhaariy (597) da Muslim (1598) sun riwaito daga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

مَنْ نَسِىَ صَلاَةً فَلْيُصَلِّ إِذَا ذَكَرَهَا ، لاَ كَفَّارَةَ لَهَا إِلاَّ ذَلِك

Duk wanda ya manta da wata sallah, to sai ya yi ta idan ya tuna da ita. Ba ta da wata kaffara sai dai hakan.

A cikin wata riwaya ta Muslim: 1600 kuma ya ce

مَنْ نَسِىَ صَلاَةً أَوْ نَامَ عَنْهَا فَكَفَّارَتُهَا أَنْ يُصَلِّيَهَا إِذَا ذَكَرَهَا

Duk wanda ya manta da wata sallah ko ya yi barci bai yi ta ba, to kaffararta ita ce ya sallace ta a lokacin da ya tuna da ita.

Sannan a cikin hadisin barcin da suka yi a cikin halin tafiya har rana ta fito, Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

أَمَا إِنَّهُ لَيْسَ فِى النَّوْمِ تَفْرِيطٌ ، إِنَّمَا التَّفْرِيطُ عَلَى مَنْ لَمْ يُصَلِّ الصَّلاَةَ حَتَّى يَجِىءَ وَقْتُ الصَّلاَةِ الأُخْرَى ، فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ فَلْيُصَلِّهَا حِينَ يَنْتَبِهُ لَهَا ، فَإِذَا كَانَ الْغَدُ فَلْيُصَلِّهَا عِنْدَ وَقْتِهَا

Babu wani laifin sakaci a cikin sha'anin barci: Sakaci kawai yana ga wanda bai yi sallah ba ne har sai da lokacin wata sallar ya zo. To, duk wanda ya aikata haka (watau ya yi barci), to sai ya yi sallar a lokacin da ya faɗaku a kanta. Sannan kuma idan lokacinta ya zo a gobe sai ya sallace ta a kan lokacinta. (Muslim: 1594)

A ƙarƙashin waɗannan hadisan ne malamai suka ce

Game da wanda ya farka a makare tare da janaba, ta yadda idan ya tsaya yin wanka lokacin sallah zai fita, to da ya farka sai ya tafi ya yi wanka ya yi sallarsa. Kuma ko da lokacin sallar zai fita ba zai yi taimama ba. Haka kuma hukuncin ya ke ko da zai rasa jam'i, domin kiyayewa a kan lokaci ya fi kiyayewa a kan jam'i, kamar yadda yake a fili. Wannan kuma shi ne lokacinsa a shari'ance, tun da dai ba shi da wani laifi a kan barcin da ya kwashe shi.

Sannan kuma ko da shi da kansa ne ya janyo abin da ta sa ya makaran, duk da haka dai wankan zai yi sannan ya yi sallar ba taimama ba, ko da kuwa zai rasa lokaci ko zai rasa jam'i, domin shi ya janyo wa kansa wannan asarar.

Dubi maganganun malamai a kan irin wannan matsalar a cikin: Daraarul Mudiyyah Sharh Durarul Bahiyyah, shafi: 51, da At-Ta'leeqaatur Radiyyah Alar-Raudatin Nadiyyah: 1/211, da Al-Mausuu'atul Fiqhiyyatul Muyassarah Fee Fiqhil Kitaab Was-Sunnatil Mutahharah: 1/256, da Tamaamul Minnah Fit Ta'leeq Alaa Fiqhis Sunnah, shafi: 132-133, da Sahih Fiqhis Sunnah: 1/171, da Tamaamul Minnah Fee Fiqhil Kitaab Wa Saheehis Sunnah: 1/128.

Amma maganar wai ya je ya yi sallar da alwala bayan kuwa yana da janaba, wannan ba daidai ba ne, domin alwala ba ta iya gusar da janaba. Da taimama ce kawai ake halatta masa yin sallah a halin yana da janaba a lokacin da ba ruwa ko kuma a lokacin da ba zai iya yin amfani da ruwan ba, saboda rashin lafiya da makamancin haka, amma ba gudun rasa jam'i ba, a maganar da ta fi rinjaye a wurin malamai.

Haka ma maganar cewa wai ya rama sallar da ya yi a bayan ya yi wanka, wannan ma ba daidai ba ne.  Domin idan dai har Shari'a ta yarda ya yi sallar a haka, to kuwa babu dalilin da zai sa ya rama kuma daga baya. Tun da dai ba a yarda da maimaita yin sallah ɗaya sau biyu a rana ɗaya ba, sai da larura, kuma wannan ba shi daga ciki.

WALLAHU A'ALAM.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments