Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wasan Kwallo ⚽

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ina tambaya ne akan kwallon qafa, akwai wanda yake neman aurena sana'arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake komai, so malam ina kokonto akan wannar sana'ar tasa, kada ya kasance sai anyi auren inji cewa ba halal bane, tunda ana biyansa idan sukayi wasa, to shine malam ko a taqaice a sanar dani wani abu akai, saboda musan makamar mu, nagode•

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To 'yar'uwa ına rokon Allah ya baki miji nagari, malamai suna kasa kwallo gıda uku

1. Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu su haɗu, su yi kwallo don su tsinka jinin jikinsu, wannan kam ta hallata mutukar ba ta kautar daga ambaton Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga .

2. Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su haɗa kuɗi su sayı kofi wanda a karshe kungiya ɗaya za ta ɗauka, wannan kam bai halatta ba, saboda daidai yake da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a tsakanin 'yan kwallo.

3. Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma malamai sun ce haramun ne saboda asali musabaka da wasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari'a ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin abin da aka halatta, sannan akwai ɓarna mai yawa a cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan Kwallon wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi da kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan har da doke-doke tsakanin kungiyoyin guda biyu.

Idan ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na biyu ko na uku, to ya wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki ji, to auransa akwai haɗari saboda zai ciyar dake da haramun.

Don neman karin bayani duba Fataawaa Al-lajna Adda'imah 3/238 da kuma Fataawaa Muhammad bn Ibrahim 8/116.

Allah ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments